Yadda jami’an tsaro suka kwato mutane 10 da aka sace a Katsina

Rundunar ’yan sanda da sojoji sun dakile yunkurin yin garkuwa da mutane tare da ceto mutane 10 da aka sace a yankin Jibia, Jihar Katsina.

Yadda jami’an tsaro suka kwato mutane 10 da aka sace a Katsina

’Yan sanda. (Hoto: NAN)

Rundunar ’yan sanda tare da hadin gwiwar sojoji sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane tare da ceto wasu mutane 10 da aka sace a Karamar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina.

Kakakin rundunar yan sandan, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu, ya ce an kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su ne a kan hanyar Kukar Babangida zuwa Yan Gayya.

“A lokacin da jami’an tsaron hadin gwiwan suke sintiri ne gungun wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai suka bude musu wuta.

“Nan take jami’an suka mayar da martani inda suka yi nasarar dakile harin tare da ceto mutane 10 da aka yi garkuwa da su,” in ji shi.

ASP Abubakar Sadiq-Aliyu ya ce kwamishinan yan sandan jihar, Aliyu Abubakar-Musa, ya yaba wa jami’an bisa irin bajintar da suka suka.

Ya bukaci jama’a da su ci gaba da ba wa rundunar da sauran hukumomin tsaro goyon baya da bayanan da suka dace domin a gaggauta daukar matakin yaki da duk wani nau’in aikata laifuk a jihar.