Yadda jami’an tsaro suka yi artabu da ’yan bindiga a Katsina

A ranar Juma’ar makon jiya ne mazauna unguwar Filin Polo da ke cikin garin Katsina suka wayi gari cikin firgici, ganin yadda jami’an tsaro, ‘yan sanda da sojoji, suka yi musu kawanya dauke da bindigogi, wadanda suka yi artabu da ’yan bindiga.Wani ganau-jiyau, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa da […]

Yadda jami’an tsaro suka yi artabu da ’yan bindiga a Katsina
Yadda jami’an tsaro suka yi artabu da ’yan bindiga a Katsina

A ranar Juma’ar makon jiya ne mazauna unguwar Filin Polo da ke cikin garin Katsina suka wayi gari cikin firgici, ganin yadda jami’an tsaro, ‘yan sanda da sojoji, suka yi musu kawanya dauke da bindigogi, wadanda suka yi artabu da ’yan bindiga.
Wani ganau-jiyau, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa da sassafe ya ji wata karar da da farko ya yi zaton taransafomar wutar lantarki ce, domin wani lokaci takan yi haka, amma daga baya sai ya fahimci ta harbin bindiga ce. Ya fito waje ke nan don ganin abin da ke faruwa, sai ya ga motoci uku dauke da sojoji, bayan ga wasu uku kuma babu kowa a cikinsu. A nan ya fahimci lallai akwai abin da ke faruwa don karar da yake ji daga yammacin gidansa ne. Kafin ya koma cikin gida sai kuma ga wasu karin motocin ‘yan sanda da kuma jami’an farin kaya na SSS.
Shi ma wani mazaunin unguwar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Na ga sojoji sun wuce da wani mutum da ankwa ga hannunsa sun shiga cikin unguwa, can sai ni da wadanda muke tsaye tare muka fara jin karar harbe-harbe saboda haka kowanenmu ya yi ta kansa”.
Ita kuwa makwabciyar gidan da jami’an suka kai wa samame ga ‘yan bindigar da ba a tantance ko su wane ne ba, wadda ta ki yarda a ambata sunanta ko daukar hotonta, amma ta amince da yin bayanin cewa, “Na ji ana buga kofar gidan, wanda kowane lokaci yake a rufe, tun lokacin da wadannan mutane suka shige shi kimanin watanni biyu da suka wuce. Mun san dai akwai mace da yara biyu da kuma maza uku. To lokacin da ake bugun gidan da karfi, wanda aka bude daga baya, na ji ana tambayar wani yana cewa, ‘E,shi ne gidan’, kawai sai na ji karar bindiga, sai harbe-harbe suka kaure tsakanin su na ciki da
kuma sojojin da ke waje. Sojojin sun shiga cikin gidan har suna tambayar matar inda saura suke. Farko mun ji tana cewa ita ba tare take da su ba, amma daga baya sai muka ji ana cewa, ‘Ta harbe shi a hannu’. Kai, wallahi in da ina dauke da ciki da ban san lokacin da zan haihu ba saboda tsananin karar harbin bindiga, ga tashin hankalin da ya same mu babu wajen gudu. Sojoji da bindiga sun zagaye, sai amon fitar harsasai muke ji”.
Ta ce, tun da wadannan mutane suka kama wannan gida, babu ruwansu da kowa. Hatta matar ko yaran ba su mu’amala da kowa. “Babban abin da ya fara ba mu haushi da tsoro, wanda har na ji mazajenmu suna niyyar daukar mataki
Cigaba a shafi na 4