Yadda jami’an tsaron ABU suka kama wanda ya yi yunkurin garkuwa da kawunsa
Wani matashii mai suna Halliru Sani mai shekara 35 da ya fito daga garin danja a Jihar Katsina kuma yake zaune a garin Samaru a karamar Hukumar Sabon Gari, Zariya a Jihar Kaduna da ake zargi da yunkurin yin garkuwa da ma’aikatan Jami’ar Ahmadu Bello ciki har da kawunsa da ke dalibta a jami’ar, ya […]

Wani matashii mai suna Halliru Sani mai shekara 35 da ya fito daga garin danja a Jihar Katsina kuma yake zaune a garin Samaru a karamar Hukumar Sabon Gari, Zariya a Jihar Kaduna da ake zargi da yunkurin yin garkuwa da ma’aikatan Jami’ar Ahmadu Bello ciki har da kawunsa da ke dalibta a jami’ar, ya shiga hannun jami’an tsaro na jami’ar bayan da asirinsa da na abokin harkarsa ya tonu a lokacin da suka yi yunkuri sace wani ma’aikacin jami’ar.
Ana zargin Halliru Sani da abokin muguwar sana’arsa da tsorata mutane da yin garkuwa da su ne domin neman kudin fansa.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin Babban Jami’in Tsaro na Jami’ar, Kanar Jibrin K. Tukur (mai ritaya) ya ce Halliru Sani da Abdullahi Musa, sun yi barazana ga daya daga cikin ma’aikatan jami’ar mai suna Dokta Keku Philip na Sashin Tsirrai da Gandun Daji da ke Cibiyar Bincike da Nazarin Dabarun Noma na Jami’ar (NAERLS), inda suka bukaci ya ba su Naira dubu 200 a matsayin fansa ko su sace shi.
Ya ce ganin yadda suke kiransa babu kakkautawa ne sai Dokta Keku ya kai rahoto ga ofishin tsaro na jami’ar kuma jami’ansu suka tashi tsaye da hadin gwiwar jami’an sauran sassa da kuma amfani da na’urar tantancewa har Allah Ya ba su nasarar kama wadanda suke barazanar ga rayuwar ma’aikata da dalibansu.
Da Aminiya ta tuntubi Dokta Keku Philip ya ce mutanen sun tsorata shi kwarai da gaske domin har ta kai yana shirn barin garin ya koma inda yake ganin zai boye saboda duk inda ya sa kafa sai su buga masa waya su ce sun gan shi, don haka ya gama buyarsa su kama shi, har ta kai ya dawo ofishin jami’an tsaro na jami’ar yana kwana.
Kawun Hallirun, mai suna Bala Aminu dan karamar Hukumar danja kuma dalibi a Tsangayar Tarihi ta Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya ya shaida wa Aminiya cewa, “Ni kawun Halliru Sani ne, da wadda ta haife shi da ni uwanmu daya ubanmu daya don haka ya san sirrina, ta nan ya samu damar yi mini barazana yana ta karbar kudina, ya karbi Naira dubu Naira dubu 40 inda ya ce in tura masa katin waya. Na farko na tura masa Naira dubu 40, sannan na tura masa dubu goma domin da jami’an tsaro na jami’a suka sani sai suka ce duk abin da ya ce in yi to in yi kada in yi gardama.
Shi ma Nura Mainama Bomo, ya ce, “Ni abokin yayan Halliru Sani ne, kuma abokin wasana ne, ya ce dama ana zargin Halliru da aikata miyagun laifuffuka domin an taba zarginsa da kashe kanensa da kanen mahaifinsa ya haifa suka kwashe masa kudi. Marigayin ya taso da arziki yana sayar da kaya waya, shekara biyu da suka wuce aka kashe shi, kuma an tsare shi na tsawon lokaci kafin a sako shi, da yake magana ce ta gida don haka ba ta yi tsawo ba, kuma jin wannan labari sai duk hankali ya koma baya ana tuna irin miyagun dabi’unsa na baya.”
Shi kuwa abokin zargin nasa, Abdullahi Musa mai shekara 30 da ke sayar da nama kuma yake zaune a Kwanar Biye daidai kan Kwanar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, wurin da ya yi kaurin suna kan fashi da makami da ya sa ’yan sanda ajiye jami’ansu, ya musanta cewa ya aikata wani mugun hali. Sai dai ya ce shi ne ya bai wa Halliru lambar Dokta Keku Philip domin wai yana so ya taimake shi a kan harkar noma.
Game da ko wadanda aka kama suna da hannu a kisan Deborah Precious Asso da wani dalibi da aka yi garkuwa da shi a hanyar Kaduna zuwa Zariya, Kanar Jabril K. Tukur ya ce, “Ba su da hannu a wancan kisa da kuma garkuwa da dalibin domin ba a makarantar aka sace dalibin ba kuma da iyayensa musu garkuwa da mutanen suka yi magana ba da mu ba.”
Sai ya bukaci ma’aikata da daliban jami’ar su kwantar da hankalinsu, kuma su rika bayar da labarin duk wani abu da ba su amince da shi ba ga jami’an tsaro a kan lokaci.