Yadda jami’in agaji ya lalata ‘yar shekara 10
‘Yan sanda sun damke wani jami’in kare kananan yara da ya yi wa ‘yar shekara 10 faye a jihar Borno. Asirin wanda ake zargin ya tonu ne bayan yarinyar ta sanar da uwarta cewa sau biyu makwabcin nasu mai aiki da kungiyar Street Child Nigeria ya lalata ta. Mahaifiyar yarinyar ta ce abin ya fara ne […]
‘Yan sanda sun damke wani jami’in kare kananan yara da ya yi wa ‘yar shekara 10 faye a jihar Borno.
Asirin wanda ake zargin ya tonu ne bayan yarinyar ta sanar da uwarta cewa sau biyu makwabcin nasu mai aiki da kungiyar Street Child Nigeria ya lalata ta.
Mahaifiyar yarinyar ta ce abin ya fara ne a ranar da mutumin, “ya rage musu hanya daga Damboa, sai diyata ta taya shi shigar da kayan da ya sayo dakinsa, amma ya danne ta da karfin tsiya ya rufe mata baki, ya yi mata fyade a ranar Lahadi”.
Bayan haka ya sake yi wa yarinyar fyade ranar Talata a hanyar ta ta zuwa makaranta, lamarin da ya sa aka kira ta daga makarantar cewa diyarda ba ta iya zama da kyau.
Bayan ta binciki diyar tata, sai ta gaya mata cewa mutumin ne ya lalata ta da kuma lokutan da ya yi mata fyaden.
Babbar Darektar kungiyar agaji ta WINN, Lucy Dlama Yunana ta tabbatar wa wakilinmu da faruwar abin da mahaifiyar yarinyar ta fada.
“Mun kai karar shi kuma yanzu yana hannun ‘yan sanda, kawai abin da muke so shi ne a yi masa hukunci”, inji ta.
Yanzu haka mutumin na tsare a ofishin ‘yan sanda na GRA da ke Maiduguri, sai dai wakilinmu bai kai ga ji daga rundunar ‘yan sandan jihar Borno ko wanda ake zargin ba tukuna.