Yadda jam’iyyun PRP da NNPP suka tsole wa APC da PDP ido a zaben bana a Bauchi
Duk da cewa ana kallon jam’iyyun APC da PDP a Najeriya cewa su ne manyan jam’iyyu da suke fafatawa a tsakaninsu domin lashe mukaman siyasa, a bana a Jihar Bauchi jam’iyyun PRP mai alamar dan mabudi da NNPP mai alamar kayan marmari sun tagaza inda suka taka rawa ta hanyar fafatawa da manyan jam’iyyun biyu […]
Duk da cewa ana kallon jam’iyyun APC da PDP a Najeriya cewa su ne manyan jam’iyyu da suke fafatawa a tsakaninsu domin lashe mukaman siyasa, a bana a Jihar Bauchi jam’iyyun PRP mai alamar dan mabudi da NNPP mai alamar kayan marmari sun tagaza inda suka taka rawa ta hanyar fafatawa da manyan jam’iyyun biyu kuma suka kayar da su a zaben Majalisar Wakilai da ta jiha a wasu mazabun jihar.
Kuma jam’iyyun sun rika zuwa na biyu ko na uku a inda ba su samu nasara ba, yayin da a wani wurin ma da kyar manyan jam’iyyun suke samu su kwaci kansu daga gare su.
Watakila ganin irin nasarorin da suka samu da kuma dimbin magoya bayan da suke da su ne ya sa duk batun hadaka a tsakanin jam’iyyun adawa da ya yi tasiri a Jihar Bauchi ’yan takarar kujerar Gwamnan jihar a karkashin jam’iyyun PRP da NNPP sun tsaya ne suka yi takararsu ba tare da sun mara wa dan takarar PDP Sanata Bala Mohammed ko dan takarar APC Gwamna Mohammed Abubakar baya ba.
Jam’iyyar PRP wadda ta samo asali lokacin da marigayi Malam Aminu Kano ya kafa ta a ranar 1 ga Oktoban 1978 lokacin da ake kokarin shiga Jumhuriyya ta Biyu ranar sama da shekara 41 da suka wuce ta fafata a dukan zabubbuka jamhuriyyar ciki har da na Shugaban Kasa inda ta kafa gwamnatocin a tsofaffin jihohin Kano da Kaduna.
Bayan da sojoji suka yi juyin mulki a 1983 an rusa dukan jam’iyyu amma da aka sake kada kugen siyasa a wannan jamhuriyya sai aka sake yi wa jam’iyyar rajista kuma tun daga nan take fafatawa a zabubbuka, sai dai fitowarta na bana ta yi tasiri kwarai a zaben da aka gudanar.
Misali a zaben Gwamnan Jihar Bauchi, jam’iyyun da suka bi bayan manyan jam’iyyun su ne PRP da NNPP sai GPN. Sakamakon zaben Gwamna da aka sanar duk da cewa ba a kammala ba, Jam’iyyar PDP ta samu kuri’a dubu 469 da 512, sai APC kuri’a dubu 465 da 453 sai PRP wadda ta samu kuri’a dubu 45 da 735 yayin da NNPP ta samu kuri’u dubu 31 da 57 sai GPN wadda ta samu kuri’a 2,143,
A zaben wakilan Majalisar Dokoki ta Kasa, Jam’iyyar PRP ta samu nasara lashe kujerun Majalisar Wakilai na kananan hukumomi biyu mafiya girma a Jihar Bauchi wato Mazabar Karamar Hukumar Bauchi da kuma ta Katagum.
A Mazabar Katagum, Alhaji Umar Abdulkadir Sarki na Jam’iyyar PRP ya lashe zaben da sama da kuri’a dubu 23 da 680 sai kuma Ibrahim Mohamed Baba na APC ya samu kuri’a dubu 18 da 976 sai Garba Dogo na NNPP ya zo na uku da kuri’a dubu 8 da 983 sai Maula Adamu na PDP da ya samu kuri’a dubu 4 da 867
A zaben Dan Majalisar Tarayya na Mazabar Karamar Hukumar Bauchi Yakubu Shehu Abdullahi na Jamiyyar PRP shine ya lashe da kuriu 69,088 APC, ta samu kuriu 53,470 sai PDP tasami kuriu 43,727 botes, NNPP ta sami kuriu 4,266 .
Koda yake Jam’iyyar APC ta sha da kyar inda ta lashe kujerun Sanata na mazabun Bauchi ta Kudu da Bauchi ta Arewa da Bauchi ta tsakiya amma jam’iyyun PRP da NNPP sun kasance biye da APC.
A Mazabar dan Majalisar Dattawa ta Bauchi ta Tsakiya, Jamiyyar APC ce ta yi nasara da kuri’a dubu 120 da 871 sai Jam’iyyar PRP ta zo ta biyu da kuri’a dubu 66 da 24, PDP ta zo ta uku da kuri’a dubu 57 da 69 .
A Mazabar dan Majalisar Dattawa ta Bauchi ta Arewa kuwa duk da cewa Jam’iyyar APC ta sha da kyar da kuri’a dubu 110 da 611, Jam’iyyar NNPP ta take mata baya da kuri’a dubu 92 da140, sai PDP ta samu kuri’a dubu 56 da 379, PRP ta hudu da kuri’a dubu 1 da 234
A zaben majalisar jihar rawar da jam’iyyun suka taka a zaben bana tana da muhimmanci inda a mazaba mafi girma da yawan kuri’a wato mazabar dan Majalisa mai wakiltar Birnin Bauchi, Jamiyyar NNPP ce talashe zaben da kuri’a dubu 27 da 36 inda ta doke Jam’iyyar PDP wacce ta samu kuri’a dubu 23 da 844 sai APC ta sami kuri;a dubu 20 da 614
A wata zantawa da manema labarai kan batun hadakar jam’iyyun adawa, dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a Jam’iyyar PRP Dokta Muhammad Ali Pate ya ce jam’iyyarsu ta fi Jam’iyyar PDP kwazo a zaben Shugaban Kasa da kuma na ’yan Majalisar Dokojki ta Kasa, inda ya ce ba a fayyace yadda za a zabi mutum guda da za su rufa masa baya ba cikin ’yan takara don haka za su goyi bayan hadakar da aka yi ne bisa gaskiya da adalci.
Ita kuwa Jam’iyyar NNPP wanda ta tsayar da Ahmad Shu’aibu Adamu a takarar Gwamna ta hadu da tankade da rairaya wanda ya jawo ta koma baya. Domin a farkon fitowarta akwai jiga-jigan ’yan siyasa irin su Mahmood Maijama’a da Sanata Abubakar Maikafi da sauransu, wadanda suka fice daga cikin jam’iyyar suka koma Jam’iyyar APC. Sai dai hakan bai hana jama’a su zabe ta ta samu nasara a wasu muhimman mukaman siyasa ba.
Wani mai fashin baki kan al’amuran siyasa a Bauchi, Muhammad Jibril Sogiji ya ce a gaskiya irin rawar da jam’iyyun suka taka yana nuni ne da irin nagartar ’yan takarar da suka tsayar a wasu mazabu, kuma jama’arsu sun zabe su wani waje an danne su ne amma in ba haka ba da irin nasarar da za su samu za ta fi haka.
Sogiji ya ce kuma haka yana nuni ne da cewa al’ummar Jihar Bauchi bana sun samu damar da suka yi zabe bisa cancanta ba kawai jam’iyya suka bi ba, sun bi mutum mai nagarta da suke kyautata zato a gare shi wanda haka shi ne ke nuni da cewa kananan jam’iyyu suna iya zama wajen da al’umma za su dogara a lokacin da ’yan siyasa suka mamaye manyan jam’iyyu suka dora wadanda ba su so.