Yadda Jana’izar Khamenei ke gudana a Iran

Iran ta rufe birnin Tehran, a yayin da ake sa ran fiye da mutum miliyan 10 ake sa ran za su halarci jana’izar shugaban Iran da aka kashe, Ayatollah Ali Khamenei.

Yadda Jana’izar Khamenei ke gudana a Iran

Gwamnan Tehran, Mohammad Sadegh Motamediyan, ya bayyana cewa za a rufe duk fadin lardin daga Asabar zuwa Talata saboda jana’izar jarogan Addini na kasar Iran, Ayatolla Ali Khamenei.

Kakakin gwamnatin Iran, Fatemeh Mohajerani, ta sanar da Talata a matsayin hutu domin saukaka wa masu zuwa jana’izar “shugaban shahidai” su bar birnin.

Fiye da mutane miliyan 10 ake sa ran za su halarci jana’izar Khamenei, wanda magoya bayansa suka rika daga jajayen tutocin a matsayin alamar kira na ramuwar gayya.

Wasu ’yan Iran sun kwashe sa’o’i suna jiran fara taron a harabar masallacin da za a yi addu’ar, suna fatan za a bude kofofin tun da daddare.

“Mun zo ne saboda kaunar shugabana. Wannan jira mai dadi ne amma mai daci,” in ji Somayye, daya daga cikin masu jiran.

Fatemeh, dalibar jami’a, ta ce dogon jiran ba komai ba ne idan aka kwatanta da hidimar da Khamenei ya yi wa ƙasar.

Mahdi, wani dalibi, ya kara da cewa jiran “sa’o’i 10 zuwa 12 ba komai ba ne, kamar muna halartar jana’izar dan uwammu ne.

Tarihin Mulkin Khamenei

Khamenei ya zama jagoran Iran a 1989 bayan yakin Iran da Iraq.

Ofishinsa ya rika kula da rundunar soji, kotuna, gidajen rediyo da talabijin na gwamnati da kuma manyan mukamai na kasa.

A zamaninsa, Rundunar Mayakan Juyin Juya Halin Musulunci ta IRGC ta zama mai karfi a harkokin tsaro, siyasa da tattalin arziki. Iran ta kuma fadada shirinta na makaman roka, tana ganin hakan kariya ne daga Amurka, Isra’ila da makwabta.

Shirin nukiliyar Iran ta kasance babban abin takaddama tsakakinta a kasashen Yamma, inda Khamenei ya dage cewa Iran ba ta neman kera makaman nukiliya, amma tana da ’yancin habaka uranium.

A siyasarsa ta yankin, ya dogara da gwamnatoci da kungiyoyin da ke goyon bayan Iran, abin da ya kara fadada tasirin kasar amma ya tsananta rikici da kasashen Gulf, Isra’ila da Amurka.

=

Martanin Iraniyawa

Maimakon mutuwarsa ta raunana kasar, ta zama abin hadin kai ga dubban ’yan Iran da suka fito domin nuna kauna da girmamawa ga jagoransu mafi dadewa a mulki.

Mohammad Eslami, mai bincike a Jami’ar Tehran, ya bayyana cewa magoya bayan marigayi jagoran Iran, Ali Khamenei, sun rika daga jajayen tutocin a matsayin alamar kira na ramuwar gayya.

“Suna rokon gwamnatin Iran ta kashe wadanda suka kashe jagoransu,” in ji shi.

Ya kara da cewa marigayi jagoran bai tsaya kawai a matsayin shugaban kasa ba, “ya fi haka, ya kasance fiye da shugaba na al’ada.”

A yayin da jajayen tutocin suke zama alamar kira ga ramuwar gayya, magoya bayan Khamenei na ganin mutuwarsa ta wuce batun siyasa, ta zama al’amari na ƙasa da addini.

Ali Akbar Dareini, mai bincike a Cibiyar Nazarin Dabarun Tsaro da ke Tehran, ya bayyana cewa tsohon jagoran Iran ya gina tsarin mulki mai karfi wanda aka kafa shi ta yadda ba ya dogara da mutum daya.

“Shi ya sa Iran ta tsira daga yakin Amurka da Isra’ila… duk da cewa an kashe jagoran ƙasa da manyan kwamandojin soja a ranar farko ta yaƙin, wannan na daga cikin manyan nasarorin Khamenei,” in ji Dareini.

Tsarin mulkin da Khamenei ya kafa ya tabbatar da cewa hukumomin ƙasa ba su dogara da mutum ɗaya ba.

Wannan ya ba da damar ci gaba da gudanar da mulki duk da matsalolin tsaro da rikice-rikice.