Yadda jaruman fim suka watsar da fim suka tsunduma cikin siyasa
Ga alamu wasu daga cikin jaruman fina-finan Nollywood da na Kannywood sun bi sahun takwarorinsu na wasu kasashen duniya, inda suka tsunduma cikin harkokin siyasa gadan-gadan a sassa da dama na kasar nan. Tuni jaruman fina-finan Kannywood kamar su Sani Musa Danja da makamantansu suka yi nisa a cikin harkokin siyasa inda a kwanakin baya […]
Ga alamu wasu daga cikin jaruman fina-finan Nollywood da na Kannywood sun bi sahun takwarorinsu na wasu kasashen duniya, inda suka tsunduma cikin harkokin siyasa gadan-gadan a sassa da dama na kasar nan.
Tuni jaruman fina-finan Kannywood kamar su Sani Musa Danja da makamantansu suka yi nisa a cikin harkokin siyasa inda a kwanakin baya Shugaba Goodluck Jonathan ya nada Sani Danja wakili a kwamitin koli na Hukumar Tace Fina-finai Ta kasa.
Hakazalika fitaccen mai wasan barkwacin nan mai suna Rabilu Musa dan Ibiro ya bayyana karara cewa Gwamna Rabi’u Musa Kwakwaso yake goyon baya tun lokacin da suka samu matsala da shi da shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, karkashin jagorancin Malam Rabo.
Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa da Aminiya cewa dan Ibro yana dasawa da Gwamna Kwankwaso kuma yana daya daga cikin ’yan fim da suke kusa da shi. Haka ma ya bi gwamna a lokacin da ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC ba tare da wani bata lokaci ba.
Ita ma jaruma Nkiru Sylbanus ta fina-finan Nollywood, tuni ta yi nisa a cikin harkar siyasa; inda ta taba rike mai ba Gwamnan Jihar Imo shawara kan harkokin yawon bude ido. Bayan da ta ajiye wannan mukami saboda wasu
dalilai na kashin kanta, Gwamnan Jihar Imo Owelle Rochas Okorocha ya sake nada ta shugabar sabuwar cibiyar fina-finai ta jihar.
Kodayake Sani Musa Danja bai taba cewa ya jingine harkokinsa na fim ba saboda mukamin siyasar da ya samu amma fitacciyar jaruma Nkiru ta taba shelanta wa duniya cewa ta jingine harkar fim don ta fuskanci kalubalen da ke gabanta na sabon mukamin da aka ba ta na mai ba gwamna shawara kan yawon bude ido. Sai dai daga bisani ta dawo ruwa bayan ta ajiye mukamin sakamakon yamadidin da ake yi na cewa matsala ta samu a cikin harkar. Kodayake ta yi ta musanta zarge-zarge da jita-jitar da ake yadawa cewa korarta gwamnan ya yi saboda zargin kasa tabuka komai a sabon ofishin da aka ba ta.
Shi ma fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Saint Obi ya zama mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa. Kafofi masu karfi sun tabbatar wa Aminiya cewa Obi ya samu mukamin ne saboda kusancinsa da wasu makusantan Shugaban kasa Jonathan
kuma sun dora masa nauyin amfani da kwarewar da yake da ita wajen ganin Shugaban kasa ya ci zaben shekarar 2015.
Majiyar da ke kusa da shi ta tabbatar da cewa tuni ya watsar da harkar fim, ya mayar da hankali kan sabon kalubalen da yake gabansa kuma tuni shi da wasu abokanen huldarsa suka yi nisa wajen ganin sun fito da wata dabara da za su cimma nasarar nauyin da aka dora musu.
Ba kamar sauran jaruman da suka rika yin nuku-nukun bayyana shiga cikin siyasa ba, shi kuwa shahararren jarumin fina-finan Nollywood, Desmond Olushola Elliot fitowa ya yi fili ya bayyana aniyarsa ta neman jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar dan majalisar jiha a mazabar
Surulere 1 da ke Jihar Legas.
Tuni jarumin ya yi watsi da harkokin fina-finansa, ya shiga kamfe gadan-gadan inda a makon da ya gabata ya yi taro da kungiyar zawarawan yankin; inda ya raba musu kyaututtuka tare da yi musu alkawurra daban-daban.
Desmond ya gayyaci wasu fitattu da yake ganin za su iya taimaka masa ya samu biyan bukata kamar fitaccen dan wasan kwallon kafar nan mai suna Kanu Nwonkwo, inda ya yi bayanin neman zawarawan da mutanen mazabar Legas da shugabanin jam’iyyar APC su goya masa baya domin ya kai ga gaci.
Sai dai akwai wasu jaruman maza da mata da suka tsunduma cikin harkokin siyasa a boye don tsoron kada su samu matsala a cikin harkokinsu na fina-finai amma akwai wadanda ba su fito karara sun nuna suna goyon bayan wani ba amma a cikin fina-finansu sukan nuna a fakaice suna goyon bayan wani dan takara ko wata jam’iyyar siyasa.
Sai dai mafi yawa daga cikin jaruman da Aminiya ta tuntuba a wayar salula sun bayyana cewa sun shiga harkar ne don su bayar da gudunmawarsu wajen ci gaban al’umma da kasa baki daya.
To sai dai fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Ramsey Nouh ya bayyana cewa shi bai zai taba shiga siyasa ba kamar yadda wasu abokanensa jarumai suke yi. Ya ce ba shi da sha’awar siyasa saboda fage ne da yake yi masa wahalar sha’ani.
“Ni mai ayyukan fasaha ne, abin da na fahimta shi ne mutum zai iya cewa ba zai taba yin wani abu ba amma dalilai za su iya tilasta masa yin abin duk da haka ni ban kware wajen harkokin siyasa ba saboda fage ne wanda yake yi mini wahalar shiga.” Inji shi.
Amma ya ce jarumai maza da mata da suke yin kamfe ga wasu ’yan siyasa suna da ’yancin su yi haka kuma bai kamata wani ya tsangwame su ba saboda sun nuna ra’ayin goyon bayan wani da suke ganin zai iya shugabantarsu.