Yadda jikin masunci ke kumbura bayan katse masa na’urar numfashi a ruwa
Wani masunci mai suna Alejandro Ramos mai shekara 56 da ke garin Pisco a kasar Peru ya fuskanci canjin rayuwa bayan katsewar abin numfashi a ruwa. Masuncin ya kai shekara hudu yana sana’ar kamun kifi a teku. Bayan da ya samu katsayewar iskar numfashi da yake shaka idan yana nikaya, sai jikinsa ya ci gaba […]
Wani masunci mai suna Alejandro Ramos mai shekara 56 da ke garin Pisco a kasar Peru ya fuskanci canjin rayuwa bayan katsewar abin numfashi a ruwa. Masuncin ya kai shekara hudu yana sana’ar kamun kifi a teku.
Bayan da ya samu katsayewar iskar numfashi da yake shaka idan yana nikaya, sai jikinsa ya ci gaba da kumbura lokacin da yake kamun kifi.
Alejandro Ramos, wanda aka fi sani da Willy, yana gudanar da sana’arsa ce a cikin teku.
A lokacin da Alejandro yake kasar teku yana yunkurin kama kifi, kimanin shekara hudu ke nan, wani jirgin ruwan dakon kaya ya yi kuskuren katse na’urar da yake shakar numfashi da ita.
Alejandro, ya ce, “Ina kasar ruwa tsawon kafa 114, sai wani jirgin ruwan dakon kaya ya matso kusa da inda nake ya katse min hanyoyin numfashina biyu. A lokacin da na samu katsewar numfashin na kasance ba zan dauki lokaci mai tsawo a cikin ruwan ba, sai kawai na rataya bel dina wanda zai taimaka min in yi iyo zuwa saman ruwa, daga nan na fara fita hayyacina.”
“Na bude idona sai ba na gani yadda ya kamata, saboda a lokacin da aka katse abin numfashin ba na iya yin numfashi,” inji shi.
Bayan hadarin Willy, ya rayu amma wasu sassaan jikinsa suna kumbura, yayin da nauyinsa ya karu da kilo 30. Willy dai yana fama da ciwon kirji da kwankwaso sanadiyyar kumburin jikinsa.
Willy, ya ce, “Na fada cikin wani yanayi har sai da na fara yunkurin kashe kaina.”
A duk lokacin da Willy ya zauna sai mutane su fara zuwa suna taba jikinsa musamman wajen da ya kumbura suna tambaya a kan yadda jikin yake, kamar yadda wata ’yar uwar Willy ta sanar.
Kwanan nan Willy ya ziyarci asibitin Nabal a garin Lima don ganin likita Dokta Raul Aguado. kan matsalar. Likitan ya auna jikin Willy, inda ya fara gwada hannunsa ya kai santimita 74 yayin da fadin kirjinsa ya kai sentimita 135.
Bayan gwaje-gwajen Dokta Raul a jikin Willy, ya ce, bai taba ganin irin wannan cutar da ta same shi bayan hadari ba, kuma magungunan da aka yi amfani da su ba su yi wa Willy aiki ba.