Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Obasanjo ya ce zai yi kewar tsohon shugaban na Amurka.

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana yadda tsohon Shugaban Amurka, Jimmy Carter, ya taka muhimmiyar rawa wajen ceto rayuwarsa.

Obasanjo ya yi wannan bayani ne a taron tunawa da Carter, wanda gudanar a ɗakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, a Jihar Ogun, don karrama Carter.

Tsohon shugaban na Amurka ya rasu ranar 29 ga watan Disamban 2024, yana da shekaru 100.

Obasanjo, ya bayyana cewa Carter ya kai wa marigayi Janar Sani Abacha ziyara da kansa domin roƙon a sako shi daga kurkuku.

“Shugaba Carter yana cikin abokaina na waje da suka jajirce don ceton rayuwata.

“A lokacin ziyararsa, ya shawo kan Abacha kan lallai a sake ni,” in ji Obasanjo.

“Shi kaɗai ne baƙon da ba ɗan Afirka ba da ya yi wannan ƙoƙari saboda neman ‘yancina.”

Har ila yau, Obasanjo ya bayyana yadda Carter ya sanar da shi game da gudummawar Ted Turner, wanda ya kafa tashar CNN, wanda ya nuna ƙwazo wajen neman a sake shi.

“Carter ya ce min, ka gode wa Ted Turner saboda kyautatawarsa. Ya zo wajena ya ce, ‘Ka bai wa abokina Obasanjo ‘yanci, zan kula da shi da iyalinsa a duk inda ya zaɓa ya zauna.’ Wannan ya sa na yi kuka,” in ji Obasanjo.

Obasanjo ya bayyana Carter a matsayin shugaba mai tsari, tawali’u, da tausayi, wanda suka yi tarayya a harkar gidajen noma.

Ya ce shugabancin Carter da ƙudurinsa na adalci sun yi matuƙar tasiri.

“Zan yi kewar babban abokina, amma ina da tabbacin za mu haɗu a Aljanna,” in ji shi.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7