Yadda jiragen soji suka kashe mutane 200 a Kasuwar Jilli
Jiragen kai harin ne a yayin wani samamen soja da ke niyyar kai hari kan waɗanda ake zargin ’yan Boko Haram ne a yankin.
Aƙalla mutane kusan 200 ake fargabar sun mutu bayan jiragen soji sun kai hari kan kasuwar a garin Jilli da ke kan iyakar jihohin Borno da Yobe a ƙarshen mako.
Jiragen kai harin ne a yayin wani samamen soja da ke niyyar kai hari kan waɗanda ake zargin ’yan Boko Haram ne a yankin.
Mazauna yankin sun bayyana yadda jiragen yaƙi guda huɗu suka kai harin a lokacin da ake tsaka da harkoki a kasuwar ta mako mako da ke tsakanin ƙananan hukumomin Gubio ta Jihar Borno da kuma Geidam a Jihar Yobe.
A wata sanarwa da kakakin ɓangaren jiragen sama na rundunar Operation HADIN KAI, Sani Uba, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an hallaka ’yan ta’adda da dama, an lalata motocinsu, yayin da sauran suka tsere a lokacin harin.
- ’Yan bindiga na neman N150m kan mutanen da sace a Ƙanƙara
- Kasuwar Jilli cibiyar ’yan ta’adda ce — Buratai
Sai dai bayan bayyanar rahotannin mutuwar fararen hula, rundunar sojin saman Najeriya ta sanar da fara bincike kan lamarin.
NAF ta ce ta ɗauki zarge-zargen da muhimmanci, inda ta kunna sashen binciken illar da fararen hula ke fuskanta (CHAI-Cell) domin gano gaskiyar abin da ya faru a wajen.
Kasuwar mako-mako ta Jilli na jawo ’yan kasuwa da masu saye daga yankuna da dama, ciki har da Gubio, Futchimiram da Benisheikh a Jihar Borno, da kuma Gurokayeya da Geidam a Jihar Yobe.
Majiyoyi da dama sun ce jirgin yaƙin da ya kai harin na bin diddigin wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne da suka je kasuwar domin karɓar haraji daga ’yan kasuwa da kuma samo kayayyaki.
Wani ganau mai suna Umar Bomai ya shaida wa wakilinmu cewa kimanin ’yan kasuwa 200 aka kashe a ƙauyen Jilli da ke yankin Futchimiram na Karamar Hukumar Geidam.
“Lamarin ya faru ne yayin da a daidai lokacin da kasuwar ke ciki da jama’a. Da farko mun ga jirgi ɗaya yana zagayawa sama, muna zaton yana bayar da tsaro. Amma daga baya wasu suka ƙaru har suka kai huɗu.
“Nan take muka ji wata ƙara mai ƙarfi, ba tare da sanin cewa hari ne daga sama ba. Kafin mu ankara, jiragen suka fara jefa bama-bamai, jama’a suka fara guje wa domin tsira.
“Ko da mutane na ƙoƙarin tserewa, harin bai tsaya ba. Mun ƙirga gawarwaki kusan 200 a wurin, kuma mai yiwuwa sun fi haka,” in ji shi.
Yawan mace-mace na iya ƙaruwa
Wani mazaunin yankin, Babagana Bukar, wanda mahaifinsa na cikin waɗanda suka rasu, ya ce adadin na iya zarce 200 yayin da ake ci gaba da gano gawarwaki.
“Yawan waɗanda suka mutu na iya haura 200. Wasu sun mutu a kasuwa, wasu kuma a daji yayin da suke gudu. Hatta a asibiti, mutum 11 daga cikin waɗanda aka kwantar sun rasu yayin jinya. Har yanzu muna ci gaba da tattara gawarwaki,” in ji shi.
Da aka tuntubi kansilan yankin Futchimiram, Malam Lawan Zanna, ya ce kimanin mutum 200 aka kashe, duk da cewa ba a tantance ainihin adadi ba.
Ya ce, “Har yanzu ba mu da cikakken adadin waɗanda suka mutu, amma wani ganau ya tabbatar min da cewa sama da mutum 200 sun rasu.
“A yanzu haka muna da mutum 24 da ke kwance a Asibitin Kwararru na Geidam da kuma Asibitin Koyarwa na Damaturu.”
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ma ya ruwaito cewa fararen hula 200 sun mutu a harin, abin da ya dace da bayanan da mazauna yankin da jami’an gwamnati suka bayar.
Ƙungiyoyin farar hula da masana harkokin tsaro sun nuna matuƙar damuwa kan harin, wanda rahotanni suka ce mafi yawan mutanen da aka kashe ’yan kasuwa, tare da jikkata wasu da dama.
Gwamnatin Yobe ta tabbatar da mutuwar fararen hula
A nata ɓangaren, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta ce wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa ’yan kasuwa ne daga ƙaramar hukumar Geidam.
Hukumar ta ce bisa umarnin gwamna Mai Mala Buni, ta ƙaddamar da matakan gaggawa tare da tura jami’an bincike zuwa yankin domin tantance halin da ake ciki.
Ta kuma buƙaci jama’a su kwantar da hankali tare da guje wa yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba, musamman dangane da adadin waɗanda suka mutu, tana mai tabbatar da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin kai agajin jin kai.
Haka kuma gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa an kashe fararen hula da dama, galibinsu ’yan kasuwa, bisa kuskure a harin.
Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Abdulsalam Dahiru (mai ritaya), ya ce, “Rundunar jiragen sama ta Operation HADIN KAI ta kai hari a Jilli, wanda aka sani a matsayin sansanin Boko Haram a ƙaramar hukumar Gubio ta Jihar Borno, a ranar Asabar, 11 ga Afrilu, 2025.
“Wasu mazauna Geidam da suka je kasuwar mako-mako ta Jilli sun shiga cikin waɗanda abin ya shafa, kuma an kai su Asibitin Kwararru na Geidam inda ake kula da su.”
Gwamnatin ta jaddada cewa Jilli na daga cikin wuraren da ‘yan ta’adda ke amfani da su, tare da kira ga jama’a da su kwantar da hankula.
Wani mai aikin sa-kai a yankin, Idriss Alhaji Baffa, ya ce asibitin Geidam ya cika maƙil, yana matuƙar buƙatar gadaje da masu bayar da jini.
“Babu wadataccen gado a asibitin. Wasu marasa lafiya ana kula da su a ƙasa, wasu ma a cikin motoci saboda rashin wuri.
“Mutane da dama na buƙatar jini cikin gaggawa. Duk da cewa akwai masu son bayarwa, ba a samun dacewar jini sosai. Lamarin na da matuƙar tsanani, muna buƙatar taimako cikin gaggawa,” in ji shi.