Yadda jiragen soji suka ragargaji ’yan bindiga a dajin Kaduna
Jiragen sojin sun ragargaza maboyar yan bindigar a dazukan Igabi da Giwa
Jiragen Rundunar Sojin sama ta Najeriya sun ragargaza ’yan bindiga da dama a dazukan kananan hukummin Giwa da Igaba a Jihar Kaduna.
Kakakin rundunar, AVM Edward Gabkwet ya ce a ranar Juma’a jiragen yakin suka tarwatsa maboyar wani dan bindiga mai suna Alhaji Layi a yankin Kufan Shantu da ke Karamar Hukumar Giwa.
Jami’in ta ci gaba da cewa a yayin harin, jiragen sun kuma ragargaza ma’adanar kayan amfanin ’yan ta’addan.
Jiragen sun kai makamancin harin a Dajin Malum na Karamar Hukumar Igabi, inda “suka hango ’yan ta’addan sunan kai-komo a sansaninsu, suka tarwatsa shi, suka aika su barzahu.
Edward Gabkwet ya jiragen sojin sun kai hare-haren ne a ci gaba da aikin da suke yi na murkushe ’yan ta’adda a yankin Arewa masu yamma.
Sanarwar da ya sanya wa hannu a ranar Lahadi ta ce, duk da kalubalen da suke fuskanta, sojoji na samun nasara a aikin kakkabe ’yan bindiga a yankinn.
(NAN)