Yadda jiragen soji suka ragargaza sansanin ISWAP A Dajin Sambisa
An bi sahun ’yan ta’addan maboyarsu a cikin kungurmin jeji inda aka rika cilla musu bama-bamai ta sama.
![Yadda jiragen soji suka ragargaza sansanin ISWAP A Dajin Sambisa Yadda jiragen soji suka ragargaza sansanin ISWAP A Dajin Sambisa](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2024/01/WhatsApp-Image-2024-01-08-at-09.00.19.jpeg)
Rundunar sojin Sama ta Najeriya ta kai farmaki kan sansanin kungiyar Boko Haram, inda ta kashe ’yan ta’adda da dama tare da lalata maboyarsu a vankin Parisu da ke gefen Dajin Sambisa a jihar Borno.
Harin da sashen sojin sama na Rundunar Operation HADIN KAI ya kai a ranar 5 ga Disamba, ya kashe mayakan ISWAP masu dimbin yawa.
Kafin nan sai da jirgin rundunar ya kai hari bayan samun sahihan bayanai kan abin da ke faruwa a wasu manyan sansanonin ’yan ta’addar inda ya hallaka mayaka masu yawan gaske.
Wata majiyar tsaro ta ce an bi sahun ’yan ta’addan ne zuwa maboyarsu a cikin kungurmin jeji inda aka rika cilla musu bama-bamai ta sama.
Hare-haren sun lalata ginin da ’yan ta’addan suke ciki da kuma kayan aikinsu yayin da wadanda suke yunkurin tserewa daga yankin kuma aka rika yi musu dauki dauki-dai-dai ta sama.