Yadda jiragen yaƙi suka halaka ’yan ta’adda a Zamfara

Jiragen Sojin Nijeriya sun halaka ɗimbin ’yan ta’adda da ke shirin kai hari a yankin Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Yadda jiragen yaƙi suka halaka ’yan ta’adda a Zamfara

Jiragen Sojin Nijeriya sun halaka ɗimbin ’yan ta’adda da ke shirin kai hari kan al’ummar yankin Babban Ƙauye a Jihar Zamfara.

Zugar ’yan ta’addan da suka gamu da ajalinsu a harin jiragen sun fito ne daga gungun jagoran ’yan fashin daji, Ɗan Isuhu da kuma Dogo Sule.

Jiragen sun kuma yi wa gungun wasu ’yan ta’adda luguden wuta a yankin Tsafe a yayin da suke shirin kai wa wasu ƙauyuka da sojoji hari a yankin.

Majiyoyin tsaro sun ce ’yan ta’addan sun gamu da luguden bama-baman ne daga jiragen Rundunar Operation Farautar Mujiya.

Kakakin Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, Iya Komodo Olusola Akinboyewa, ya ce bayan ’yan fashin dajin sun taru, za su kama hanyarsu ta kai hare-haren ne sojoji suka samu bayanan sirri, ba tare da ɓata lokaci ba kuma suka far musu, suka aika su barzahu.

Ya shaida wa manema labarai a ranar Lahadi cewa hare-haren an kai su ne a ranar Juma’a kuma an halaka wasu manyan ’yan ta’adda.

Iya Komodo Olusola Akinboyewa ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da yin bakin ƙoƙari wajen murƙushe ayyukan ’yan ta’adda.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda