Yadda Jonathan ya dakatar da musayar ’yan matan Chibok

Wata jaridar Birtaniya ta wallafa labarin cewa saura kiris a yi musayar ’yan matan Chibok da mayakan Boko Haram suka sace, amma gwamnati ta dakatar da hakan.Jaridar Daily Mail ta kasar Ingila ta ce ga alama dakatar da musayar ’yan matan ya fusata shugabannin kungiyar Boko Haram.Bayanai sun ce Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya […]

Yadda Jonathan ya dakatar da musayar ’yan matan Chibok
Yadda Jonathan ya dakatar da musayar ’yan matan Chibok

Wata jaridar Birtaniya ta wallafa labarin cewa saura kiris a yi musayar ’yan matan Chibok da mayakan Boko Haram suka sace, amma gwamnati ta dakatar da hakan.
Jaridar Daily Mail ta kasar Ingila ta ce ga alama dakatar da musayar ’yan matan ya fusata shugabannin kungiyar Boko Haram.
Bayanai sun ce Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya yi waya daga birnin Paris inda ya halarci wani taro kan tsaro tare da shugabannin kasashen da ke makwabtaka da Najeriya da kuma shugaban Faransa cewa a dakatar da musayar.
Jaridar ta ce wani da kungiyar ta amince da shi ne, ya zama mai shiga tsakanin kungiyar da gwamnati a kokarin ceto ’yan matan cikin ruwan sanyi.
Daily Mail ta ce, mutumin ya yi tafiya mai cike da hadari, inda ya je sansanin ’yan Boko Haram ya kuma samu amincewarsu na su sako ’yan matan da suka sace a garin Chibok, yayin da kuma za a sako musu wasu daga cikin magoya bayansu da gwamnati ke tsare da su.
A cewar bayanan mutumin ya ga ’yan matan da aka sace da idonsa, kuma ya tabbatar da cewa ana ciyar da su da kula da su yadda ya kamata, kuma ’yan matan na Chibok, sun shaida masa cewa suna son Gwamnatin Tarayya ta biya wa ’yan kungiyar bukatunsu, domin su koma gidajen iyayensu.
Sai dai ana dab da cimma yarjejeniyar fara musayar ’yan matan Chibok din ne gwamnatin ta dakatar da hakan.
Jaridar ta ce kwan-gaba kwan-baya da gwamnatin ke yi game da hanyoyin da za a bi, wajen ceto ’yan matan fiye da 200 ne ya janyo soke shirin ceto ’yan matan ta hanyar musaya.
A ranar 17 ga watan Mayun da muke ciki ne, Shugaban Faransa Francios Hollande ya kira taro kan batun tsaro a Paris, inda Shugaba Jonathan ya gana da shugabannin kasashen Nijar da Kamaru da Chadi da kuma jami’an diflomasiyyar Birtaniya da Amurka da Isra’ila da kuma Faransa, kuma daga can ne aka ce ya bugo waya a dakatar da musayar.