Yadda Jonathan ya kassara Najeriya-Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban Kasa ta ce gwamnatin Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonatahan ta durkusar da Najeriya ta hanyar “Cin hanci da rashawa da kashe kudi ba bisa ka’ida da sauran almundahana”. Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kasa Kan Harkokin Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Garba Shehu shi ne ya yi furucin a sanarwar da […]

Yadda Jonathan ya kassara Najeriya-Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban Kasa ta ce gwamnatin Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonatahan ta durkusar da Najeriya ta hanyar “Cin hanci da rashawa da kashe kudi ba bisa ka’ida da sauran almundahana”.
Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kasa Kan Harkokin Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Garba Shehu shi ne ya yi furucin a sanarwar da ya fitar jiya don mayar da martani kan ikirarin da Jonathan ya yi na cewa a shekarar 2105 gwamnatinsa ta bar wa Shugaba Buhari tattalin arziki mai kyau.
Shehu ya ce gwamnatin Jonathan ta mika wa Shugaba Buhari rushashshen tattalin arziki wanda tsawon shekarun da gwamnatinsa ta yi tana cin hanci da rashawa suka durkusar da shi.
Ya bayyana cewa idan aka duba bangarori da yawa za a ga cewa Jonathan da gwamnatinsa sun gudanar da gwamnatin da a tarihin Najeriya ba a taba samun gwamnatin da ta jefa tattalin arziki kasar cikin halin-ni-’yasu kamar ta ba.
Ya bayyana cewa inda Jonathan da jam’iyyarsa ta PDP sun ci gaba da mulki da sun ci gaba da yaudarar mutane ta hanyar karbo bashi suna tallafawa sata da barna kuma su ci gaba da dora matsalar a kan al’ummar da za su zo nan gaba.
Ya bayyana cewa a lokacin da gwamnatin Buhari ta karbi mulki, jihohi 21 ba sa iya biyan albashi sannan kuma kudin ariyasa na ma’aikata sai kara taruwa yake yi a kan gwamnati .
“Matakin kawai da PDP ta dauka mafita shi ne su debi kudin tallafin zaizayar kasa sannan kuma su baiwa kowace jihar da PDP ke mulki biliyan biyu. Bashin da Tsohuwar Ministar Kudi, Dokta Okonjo Iweala ta rika karbowa ne ya hana gwamnatin tarayya cin bashin albashin ma’aikata”. Inji shi