Yadda Jonathan ya tozarta Suleiman Abba
A ranar Talata ce Shugaban kasa Goodluck Jonathan da niyya ya tozarta Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Malam Suleiman Abba, ta hanyar korarsa daga aiki ta kafar sadarwar Tweeter din kakakinsa Rueben Abati, ba tare da sanar da shi ba, wanda hakan ya sanya Suleiman Abba ya yi ta aiki a ofishinsa na tsawon […]

A ranar Talata ce Shugaban kasa Goodluck Jonathan da niyya ya tozarta Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Malam Suleiman Abba, ta hanyar korarsa daga aiki ta kafar sadarwar Tweeter din kakakinsa Rueben Abati, ba tare da sanar da shi ba, wanda hakan ya sanya Suleiman Abba ya yi ta aiki a ofishinsa na tsawon awanni bayan sallamarsa kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
Jaridar Premium Times ta ce, har zuwa karfe 11:23 na dare bayan fiye da awa goma da sallamarsa daga aiki ta intanet bai samu wani bayani daga Shugaban kasar ko wani wakilinsa don sanar da shi cewa an sauke shi daga mukaminsa ba.
Da rana kakakin Shugaban kasa Reuben Abati ya fitar da sanarwa a shafinsa na Tweeter cewa Shugaban kasar ya sauke Suleiman Abba tare da nada Na’ibin Sufeto Janar Solomon Arase a madadinsa ba tare da ya yi wani karin bayani ba, kuma ba tare da ya yi masa fatar alheri ba, irin yadda aka saba a Najeriya.
Suleiman Abba wanda shugabancinsa na wata tara ke cike da takkadama, a cewar jaridar babu shakka da gangan aka tozarta shi wajen sauke shi daga mukaminsa. Ta ce wani abokinsa ya shaida mata cewa Abba ya kadu kwarai kan laifin da ya aikata da za a yi masa wannan cin zarafi, bayan ya bauta wa gwamnati da kasar nan.
Mista Abati wanda ya bayyana sauke Abba da cewa ya fara aiki ne “nan take” ya fitar da sanarwar ce kwafen sanarwar da misalin karfe 1:24 na rana, ya sake maimaitawa da karfe 1:47 tare da bayyana Arase a matsayin wanda Shugaba Jonathan ya zaba.
Suleiman Abba dai shi ne shugaban ’yan sanda na hudu da ya yi aiki a karkashin Shugaba Jonathan. Kuma lokacin da wani abokinsa ya tuntube shi da misalin karfe 3:00 na rana ya ce ba a sanar da shi kan sauke shi ba, kuma ma yana kan aiki. Kuma da misalin karfe 11:23 na dare da aka sake tuntubarsa ya ce, ba a ba shi takarda ko sako ko da ta na’ura ce cewa an sauke shi ba.
Akwai bayanan da suke cewa an yi waje da Sufeto Janar Abba ne don hukunta shi kan rawar da ya taka a lokacin zabubbukan da suka gabata, kuma hakan yana zuwa ne a daidai lokacin da ya rage kasa da mako biyar na wannan gwamnati.
Abba ya kasance a tsaka mai wuya inda manyan jam’iyyun siyasar kasar nan PDP da APC suka rika zarginsa da nuna musu son kai.
Jaridar ta ce majiyarta ta ce PDP ta damu sosai kan yadda Abba ya gaza ko ya ki ba ’yan sanda umarnin su goya wa ’yan takararta baya tun daga Shugaba Jonathan zuwa kasa domin su lashe zaben.
Wani jami’in gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa jaridar cewa: “Ba zan iya cewa akwai danyen ganye tsakanin Shugaban kasa da Sufeto Janar din ba a bayan zaben. Gwamnati tana jin Sufeto Janar din bai yi kokarin da ya kamata ba wajen tallafa wa Shugaban kasa ya samu nasara ba,” inji jami’in.
Jami’an gwamnati sun kawo misali da tura ’yan sanda gabanin zaben musamman a wuraren da ake da matsala kamar Jihar Ribas, inda jaridar ta ruwaito cewa Shugaba Jonathan cikin fushi ya umarci Abba ya sauya tura Mataimakin Sufeto Janar Tunde Ogunsakin zuwa Jihar Ribas kafin zaben gwamnoni na 11 ga Afrilu, amma sai aka ji labarin a kafafen watsa labarai bayan su uku kadai suka yi maganar.
Wasu majiyoyi sun ce sauran laifuffukan Abba sun hada da zargin ya fara sauya akalar biyayyarsa ga zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari, inda suka kawo misali da yadda ya tura karin ’yan sanda cibiyar tattara sakamakon zaben Shugaban kas a daidai lokacin da aka janye jami’an tsaro na SSS lokacin da Orubebe ke hanayaniya. Wani laifin nasa shi ne ya tarbi Janar Buhari a filin jirgin sama kuma ya halarci ba shi takardar shaidar lashe zaben Shugaban kasa a hedkwatar Hukumar INEC.
Akwai majiyar da ta ce Shugaban kasar ya samu rahoton sirri kan kyakkywar dangantakar da ke tsakanin Suleiman Abba da manyan ’ya’yan APC, yayin da wata majiyar ta ce an sauke Abba ne saboda ya ki bin umarnin Shugaban kasa da Jam’iyyar PDP na ’yan sanda su taimaka wajen murde zabubbukan da suka gabata.
A ranar Asabar da ta gabata, babban labarin jaridar The Nation shi ne “Ana matsa wa Jonathan ya kori Sufeto Janar” inda a ciki jaridar ta ce wasu manyan jami’an gwamnati na matsa wa Shugaba Goodluck Jonathan ya kori Sufeto Janar din duk da cewa Shugaban kasar ba ya da sha’awar yin haka. Jaridar ta ce Jonathan ya yanke shawarar kyale Abba da sabuwar gwamnati mai zuwa, amma bincikenta ya gano cewa akwai wadanda ba su ji dadin wasu matakai da Abba ya dauka a zaben Shugaban kasa da Jonathan ya amince da shan kaye.
Ta ce wasu gagga a gwamnati na cin zafi kan in ban da jihohin Ribas da Delta da Kuros Riba da Ekiti da Akwa Ibom da kuma daukacin jihohin Kudu maso Gabas ba inda ’yan sanda suka yi aiki da abin da aka tsara musu kan zaben, musamman a jihohi masu muhimmanci da suka hada da Legas da Oyo da Ondo da Ogun da Osun da Borno da Kaduna da kuma Kwara. An ce Abba ya umarci DPO-DPO a Legas cewa su bi umarnin Kwamishinan ’Yan sanda maimakon mataimakin Sufeto Janar.
Wata majiya mai tushe ta ce, wasu manyan jami’an gwamnati sun ji haushin yadda ’yan sanda suka ksa yin abin da suka saba a lokacin zaben na bana, “Ina jin Abba ya zabi zama dan ba ruwanmu lokacin zaben domin tsare rantsuwar aikinsa.To amma halartarsa wurin mika wa Buhari takardar shaidar lashe zaben ya sanyaya gwiwar jami’an fadar Shugaban kasa, inda suke ganin hakan ya saba wa tsarin aikinsa,” inji majiyar.
Sai dai Shugaban Yaki da Mahandaman Shugabanni Debo Adeniran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: “Akwai abin mamaki kan yadda aka kori Abba makonnin kadan bayan zaben da Jonathan ya fadi. Kuma abin ya fi rudarwa idan aka lura Abba yana da sauran shekara 10 kafin ya kai lokacin ritaya.”
Adeniran ya ce, akwai yiwuwar Abba ya samu makiya saboda ya ki “aiki da umarnin Jonathan da Jam’iyyar PDP na a murde zaben,” inji shi.
Abba ya goyi bayan Shugaban kasa da Jam’iyyar PDP a lokacin da rikici ya kaure a Majalisar Wakilai, inda har ya bayyana cewa bai dauki Aminu Tambuwal a matsayin shugaban majalisar ba.
Sauke Suleiman Abba ya zo ne bayan kwana daya da Jakadan Amurka a Najeriya James Entwistle ya kai masa ziyara yana yaba yadda ’yan sandan suka yi aikin da ya dace a lokacin zaben, inda suka raba kansu daga nuna goyon baya ga wani bangare.
Kuma an ce Abba na shirin kaddamar da kamfen din gyara hallayar ’yan sanda nan da makoni masu zuwa ne sai wannan guguwa ta tafi da shi.
Wata kungiyar siyasa a Jihar Ekiti mai suna Ekiti Democratic Coalition (EDC) ta yaba kan korar Suleiman Abba, inda ta zarge shi da hada kai da Jam’iyyar APC wajen kokarin kwace nasarar Gwamnan Jihar Ayodele Fayose da jama’a suka zaba.
Sai dai kuma kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) da kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC) sun nuna shakku kan sauke Abba daga mukaminsa. kungiyar ACf ta bukaci Shugaba Goodluck Jonathan ya yi wa ’yan Najeiya bayani kan dalilinsa na sauke Abba, kamar yadda shugaban kungiyar tsohon Sufeto Janar Ibrahim Coomasie ya bayyana a hira da gidan talabijin na Channels.
Alhaji Ibrahim Coomasie, ya ce sauke Abba bayan ’yan kwanaki da kammala zabe kuma wata daya da kwanaki a mika mulki akwai shakku kuma ya tayar da zarge-zarge daga bangarori da dama.
Shi kuwa Farfesa Ishak Akintola na kungiyar MURIC ya ce korar mutum mai babban matsayi kamar Abba yana haifar da tambayoyin da babu amsarsu, inda ya ce ba a saba da gwamnati mai barin gado tana sallama da nada manyan jami’ai ba.
Sai ya yi tambayoyin cewa “Shin da gaske Shugaba Jonathan zai mika mulki? Idan haka ne, me ya sa shi gaggawar nada sabon Sufeto Janar na ’Yan sanda ga sabuwar gwamnati mai zuwa? Me zai sa a kori Sufeto Janar jim kadan da faduwar jam’iyya mai mulki a zabe? Shin saboda “bai yi abin da ake so ba ne’ lokacin zaben? Ko ya ki bin haramtaccen umarni ne? Wadannan tambayoyi suna da matukar muhimmanci, saboda ’yan adawa sun sha zargin gwamnatin Najeriya da yin amfani da hukumomin tsaro wajen tauye zabin al’ummar Najeriya.”
A jawabinsa na ban-kwana Suleiman Abba ya ce ya yi bakin kokarinsa tare da gudanar da zaben nagari ciki kwanciyar hankali a zaben na bana. Abba wanda ya bayyana haka lokacin da yake mika ragamar shugabanci ga Mukaddashin Sufeto Janar Solomon Arase a shekaranjiya Laraba, ya ce galibi jama’a kan gaza fahimtar aikin dan sanda. “Na gode wa Allah Wanda Ya kawo ni kan wannan mukami na Sufeto Janar; kamar yadda Ya ce, Shi ke bada mulki ga wanda Ya so kuma Ya karbe daga wanda Ya so, to Ya kawo karshen mulkina a matsayin Sufeto Janar, cikin lafiya tare da samun yabo daga abokan aikina.”
Ya gode wa Shugaba Jonathan kan nada shi a kan mukamin da kuma sauke shi inda ya yi alkawarin ci gaba da gudanar da rayuwarsa a sabon mataki da ya samu kansa.
Tuni abokansa suka shawarce shi ya fice daga kasar nan don kare rayuwarsa sai bayar wannan mahaukciyar guguwa ta wuce ya dawo.
Bayanai sun nuna cewa cikin jami’an gwamnatin Jonathan da dama ya duri ruwa sakamakon korar Abba daga mukaminsa, inda suke tsoron kada guguwar ta hada da su.
Idan za a iya tunawa jaridar Sahara Reporter ta ranar 20 ga Disamban shekarar 2010, ta buga rahoton cewa a ranar 17 ga Disamban shekarar lokacin da Shugaba Jonathan ke jawabi ga gwamnonin Jam’iyyar PDP a kokarinsa na neman tsayawa takara ya yi barazanar cewa zai kifar da jirgin da suke ciki muddin ya rasa wannan dama. “Ku (gwamnoni) kun ba ni tabbacin goyon baya amma a boye wasunku na kamfe wa Atiku. To ba zan zauna a nan ku tozarta nib a. Kun ki ba ni duk abin da na nema. Babu Shugaban kasa a ko’ina da jam’iyyarsa ke yi masa yadda kuke min.”
Kafi nan a ranar 16 ga Disamban ya yi barazana ga gwamnonin na PDP cewa: “Ni ne direban wannan jirgin ruwan; ba zai kife ni kadai ba, zan nutsar da wannan jirgin (siyasar) ya yi kasan ruwa da duk abin da yake cikinsa.”
Tambayar da jama’a ke yi a yanzu korar Suleiman Abba da kokarin korar wasu jami’ai ciki har da Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Ahmadu Mu’azu ko wani bangare ne na kifar da wannan jirgi da Jonathan ya yi barazana? Daga nan zuwa 29 ga Mayu mai zuwa ne hakan zai tabbata ko akasinsa.