Yadda kabilar Mbororo ke rayuwa a Kamaru

Sakamakon bikin tunawa da al’umma da suka tashi daga matsuguninsu zuwa wani wuri na daban.A ranar Talata ya sake bayyana cewa kabilar Mbororo suna ci gaba da fuskantar matsala a wurare da suke zaune.Wannan kabila ta shahara masamman wurin yin kiwon shanu da kuma aikin gona. Hakan ya haddasa fadace-fadace tsakanin su Mbororon da kuma […]

Yadda kabilar Mbororo ke rayuwa a Kamaru
Yadda kabilar Mbororo ke rayuwa a Kamaru

Sakamakon bikin tunawa da al’umma da suka tashi daga matsuguninsu zuwa wani wuri na daban.
A ranar Talata ya sake bayyana cewa kabilar Mbororo suna ci gaba da fuskantar matsala a wurare da suke zaune.
Wannan kabila ta shahara masamman wurin yin kiwon shanu da kuma aikin gona. Hakan ya haddasa fadace-fadace tsakanin su Mbororon da kuma makwabtansu na wasu kabilu daban, bayan shanun Mbororo sun yi musu ta’adi a gonaki.
A Kamaru dai kabilar Mbororo tana zaune ne a yankunann karkara na lardin Adamawa da kuma Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.
Har ila yau, a Kamaru ana samun Mbororo  a yammacin kasar da gabashi da arewa maso yamma. A takaice wannan al’umma na bibiyar yankin da zai fi dacewa  wato mai dausayi da zai taimaka wurin kiwon dabbobinsu da kuma habaka noman abincin da suke yi. Abin da ya sa ke nan suka zama marasa matsuguni na asali. Ganin cewa, Mbororo mutane ne da suke kaura daga wannan wuri zuwa wancan, wannan lamari kan haifar musu da kyama daga wurin wasu jama’a.
Ganin cewa su da dabbobinsu suna shiga filayen jama’a. Irin salon wannan rayuwa a bayan gari ta jawo wa Mbororo koma baya, masamman ma a irin wannan zamani na wayewar kai.
Yaran Mbororo ba su samun daman yin karatu na zamani, face koya musu kiwon shanu da ake yi musu. Matan kuma daga an haifesu ana nuna musu kawai ne aurene ke jiransu idan suka girma. Dangane da haka ake fara samar musu da mazan da za su auresu tun suna kanana.
Duk da cewa wannan al’ada ce ga Mbororo salon irin wannan rayuwa, amma tare da taimakon gwamnati da kuma wasu kungiyoyi masu zaman kansu ana ta jan hankulansu domin su mayar da hankali wurin neman ilimi masamman ma ga ’ya’ya mata. Kodayake, an fara samun ci gaba, a dalilin cewa wasu Mbororo da suka yi katarin ilimantuwa tun farko sun fara hankaltuwa da kafa wata kungiya mai fafutukar neman ci gaban kabilar wato “Mbororo Social and Cultural Debelopment Association” (MBOSCUDA) wadda itama ka goyi bayan fitowar Mbororo daga daji domin su samu ilimantuwa a dama da su a dukkanin fannonin rayuwa.
Wannan kungiya da aka kafa a birnin Bamenda a lardin arewa masoyamma Kamaru, tana a rassa a wasu kasashen Yammacin Duniya kamar ingila. A yanzu haka dai Shugabanta wanda shi ne Jaji Manu Gidado ya ce za su dada tashi haikan domin ganin an samu wayewar kai ga makiyaya Mbororo, wadanda a shekarun baya suka dimbin asarar dukiyoyinsu sakamakon satan shanu da wasu kungiyoyi masu tada kayar baya suke yi a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da kuma Kamaru.