Yadda kabilar Ngondo take bikin tallata al’adunta a Kamaru

Daga cikin kabilu fiye da 200 da kasar Kamaru take da su, ko wace kabila tana da irin nata al’adun gargajiya da kuma bukukuwan da suke da alaka da ita. Hakazalika, ta fannin abinci ko wace kabila na da irin abincin da ta shahara wurin sarrafa shi. A wani lokacin ita ce take kirkiro da […]

Yadda kabilar Ngondo take bikin tallata al’adunta a Kamaru
Yadda kabilar Ngondo take bikin tallata al’adunta a Kamaru

Daga cikin kabilu fiye da 200 da kasar Kamaru take da su, ko wace kabila tana da irin nata al’adun gargajiya da kuma bukukuwan da suke da alaka da ita.

Hakazalika, ta fannin abinci ko wace kabila na da irin abincin da ta shahara wurin sarrafa shi. A wani lokacin ita ce take kirkiro da salon yadda ake girka abincin da kanta.
Dangane da bikin tallatar da al’adun gargajiya, kabilar birnin Douala na gudanar da wasu wasanni na gargajiya da ake kira “Ngondo”.
Ma’anar Ngondo a harshen ’yan Douala shi ne bikin hada kan mazauna gefen ruwa. Bikin ya kunshi nuna al’adun gargajiya da kuma wasu tsatsubai da ake yinsu a asirce, a dalilin cewa a fadinsu suna zantawa ne da kakanne da suka kwanta dama domin neman wani tabarruki da kuma samun shawarwari game da yadda za su tafiyar da al’amurra a cikin ko wace sabuwar shekarar miladiyya da take tafe.
Har ila yau, ana fara bikin ne da jijjibin rana, inda manyan jami’an kabilar na Douala suke halarta. daya daga cikin bangaren gargajiya na wannan biki shi ne tsere da ake yi a cikin kwale-kwale a babbar koramar da take Douala. Gabannin haka kuma sai dattawa sun fara tafiya ganawa da mamata a kebe a cikin wata bukka. Ana kwashe mako guda ana gudanar da wannan biki da ya kunshi fannoni daban-daban. Ana yin gasa na girke-girken abinci da raye-rayen gargajiya da wasu wake-wake hadi da damben gargajiya. Sai kuma zaben sarauniyar kyau da ake yi.
Bayan wannan ana zaben shugaban bikin “Ngondo” wanda shi ne zai shirya bikin na badi. Hakan nan kuma shi ne zai dinga isar da sakonnin kakanne izuwa saura jama’a. Har ila yau, a cikin wasan akan aiken wani mutum da aka riga aka horar da shi zuwa karkashin ruwan korama dauke da kwando a hannu ya tafi ya jiyo boyayyen labarin da mamata suke da shi da kuma za su bayyana wa sauran jama’a.