Yadda kafintan Indiya ya sanya wa dansa sunan Pakistan
Wani Kafin ta a kasar Indiya mai shekara 40 ya rada wa ’ya’yansa suna Bharat (India) da Pakistan, mutumin mai suna Gurmeet Singh na nuni da cewa “daya muke” wato ioyali guda ne sabanin yadda ake ta ruruta takaddama tsakanin kasashen biyu. Gurmeet na zaune ne tare da matarsa da ’ya’yansa uku, maza biyu da […]
Wani Kafin ta a kasar Indiya mai shekara 40 ya rada wa ’ya’yansa suna Bharat (India) da Pakistan, mutumin mai suna Gurmeet Singh na nuni da cewa “daya muke” wato ioyali guda ne sabanin yadda ake ta ruruta takaddama tsakanin kasashen biyu.
Gurmeet na zaune ne tare da matarsa da ’ya’yansa uku, maza biyu da mace guda a madaidaicin gidansu da ke garin Maulot da ke Punjab ta kasar Indiya kimanin kilomita 70 a kan iyakar Indiya da Pakistan . ’Ya’yansa, daya dan shekara 11 Bharat da Pakistan dan shekara 10 na nuni da cewa lokacin da aka raba kasashen biyu mutane na zaune cikin lumana.
“Na tsanani gaba,” a cewar Gurmeet, wanda aka haifa bayan an raba kasar. Sai dai rikicin da aka yin a adawa da mabiya addinin Sikh a shekarar 1984 shi shaida ne. Lokacin yana da shekara 10, sai iyayensa suka yi kaura daga gundumar Haryana Hansi zuwa Malout.
“Ina dan karami, amma zan iya tuna yadda tashin hankalin ya somo bayan da aka kashe Indira Ghandi. Maganar ta shin hankali ta bar mini abin da ba zan iya mantawa ba. Babu fushin kiyayya a tare da ni. Yafiya ce mafita,” kamar yadda jaridar the National Herald ta ruwaito daga bakin Gurmeet.
“Na yanke wa kaina matsayar yada sakon kauna da yafiya a tsakanin mutane, kasashe da makwafta. Don haka na sanya babban dana suna Bharat da kuma karamin Pakistan,” kamar yadda jaridar ta ruwaito.Ya ce babu abin da ke sanya masa annashuwa kamar ya ji Bharat y ace, “Pakistanm dan uwana ne.”
Sai dai ya ce sunan Pakistan da ya sanya wa dansa ta sa ana yi masa isgili iri-iri a cikin al’umma.
“Mutane na kaskantar da ni. Sukan ce ’yan Pakistan za su sace shi da sauran abubuwan takaici. Duk da haka ni da matata Lakhwinder tursasawa bat a sa mun sauka daga ra’ayinmu ba. Tsawon lokaci zai sa mutane su fahimci m anufar sunan ’ya’yana, ta yadda yanzu ba su da matsala wajen kiran karamin dana Pakistan.”
An samu matsala lokacin da Gurmeet ya je sanya ’ya’yans amakaranta, inda aka tursasa shi kan lallai sai ya sauya wa Pakistan suna zuwa Karandeep, inda matsin lambar shugabannin makaranta ta sa ya karyo. Sai dai ya ce har yanzu a gida ana kiransa da Pakistan, haka ma sauran abokansa ke kiransa.
Wani abin mamaki da ban sha’awa Gurmeet ya yi wa shagon kafintancinsa lakabin sunan ‘Bharat-Pakistan Woodworker’
“Ruhi ba zai samu kwanciyar hankali ba, matukar zuciya na damfare da tunanin kiyayya ga wani abu ko mutane ko kasashe. Haka lamarin yake a saukake. Ta tyiwu ni jahili ne talaka, amma ina da tabbacin imanin karfin soyayya ga kowa da kowa,” kamar yadda gurmeet ya yi nuni.