Yadda kaho ya fito a kan wata mata a Indiya

Matar ta ce tana fama da matsanancin ciwo tun bayan fitowar kahon.

Yadda kaho ya fito a kan wata mata a Indiya

Wata mata a kasar Indiya na neman taimako bayan kaho ya tsiro a kanta sakamakon ciwo da take fama da shi.

Matar mai suna Mimiya Bai ta ce ta gano hakikanin halin da take ciki ne bayan likitoci sun shaida mata cewa kaho ne yake tsirowa a kanta shekara uku da suka wuce.

Matar mai shekara 60 ta shaida wa jaridar jaridar ‘New Indian’ cewa, “Sama da shekara uku ina fama da ciwo. Na nemi taimako amma ba wanda ya saurare ni,” in ji ta.

A halin yanzu Mimiya tana ci gaba da neman magani a asibiti, duk da cewa likitoci sun bayyana cewa lalurar tata na da wuyar sha’ani.

Ta yake tabbatar da cewa kaho ne yake tsirowa a kan matar, wani likita da ke duba ta a kasar, Abhishek Jain, ya bayyana cewa wani nau’in cuta ne ke sanya kaho tsirowa a jikin mutum, amma ana iya maganinsa ta hanyar yin tiyata.

Matar da kahon ya fito mata a kai

Mimiya ta ce mutane da yawa sun yi mamakin lokacin da ta shaida musu cewa kahon ya fara girma a kanta.

Ba za a iya yi wa matar tiyata a kananan asibitoci da ke yankin ba, sai an kai ta babban asibiti mai kwararrun likitoci don yi mata magani.

Iyalanta sun bayyana cewa likitoci sun ba su shawara kai ta babban asibiti don yi mata magani a kan lokaci.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan