Yadda Kaka ta kashe jikanta ta cinye namansa
Wata tsohuwa mai suna Fatima Sadaka da ke garin Koso a yankin Doko da ke cikin karamar hukumar Labun ta jihar Neja ta yanka jikanta dan shekara 9 mai suna Muhammad Liman, inda ita da abokanta suka shanye jininsa kuma suka gasa namansa suka cinye.Aminiya ta gano cewa, gidan Fatima yana kusa ne da gidan […]

Wata tsohuwa mai suna Fatima Sadaka da ke garin Koso a yankin Doko da ke cikin karamar hukumar Labun ta jihar Neja ta yanka jikanta dan shekara 9 mai suna Muhammad Liman, inda ita da abokanta suka shanye jininsa kuma suka gasa namansa suka cinye.
Aminiya ta gano cewa, gidan Fatima yana kusa ne da gidan iyayen yaron, kuma ita ce ta haifi mahaifin yaron, sannan kuma sun shaku sosai da marigayin. Kakar yaron dai ta hada baki ne da wata kawarta mai suna Amina Wusa da kuma wani mai suna Zhitsu Aliyu suka hallaka jikan nata.
Da aka kai su hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Sashen Binciken Manyan Laifuffuka (CID),sun tabbatar da aikata laifin da ake tuhumarsu da aikatawa, inda suka nuna cewa, bayan da suka kama yaron sun ajiye shi na wadansu ‘yan kwanaki tukun,daga bisani sai suka kai shi wani wuri inda Zhitsu Aliyu ya yanka shi, suka shanye jininsa kuma suka gasa namansa suka raba a tsakaninsu.
Mayun guda uku sun yi nadamar aikata danyen aikin, inda suka nemi a yi musu sassauci, tare da alkawarin ba za su sake aikata irin wannan abun kunya ba.
Da Kofur Moses Emberger ya gabatar da wadanda ake tuhumar da aikata laifin a gaban alkalin Babban Kotun Majistire da ke Minna Alhaji Hameed Ahmad Bima, sun shaida wa alkalin cewa sun shirya ne a tsakaninsu za su rika yanka jikokinsu su cinye namansu, shi ne ita Fatima ta fara da nata, daga bisani su kuma sauran sai su biyo bayanta. Aminiya ta yi tattaki zuwa garin Koso inda ta samu mahaifin yaron da aka kashe, watau Malam Muhammad Muhammad Liman Koso, wanda manomi ne dan shekara 35, kuma yana da mata 3 da ‘ya’ya 10, wanda ya bayyana cewa a shekarun baya ma mayu sun cinye masa wani yaron nasa mai suna Bilyaminu.
Dangane da abun da ya faru da dansa Muhammad kuwa, sai ya ce,’kimanin makonni hudu da suka wuce, watau ranar juma’a, muka yi haramar zuwa gona tare da marigayin, bayan da na yi nazarin cewa aikin da ke gonar babu yawa sai na ce masa ya yi zamansa a gida, ni kuma sai in yi sauri in yi aikin kafin lokacin sallar juma’a ya yi in dawo gida. Da zan tafi na kawo Naira goma na ba shi don ya sayi abin da yake sha’awa, rabuwa ta da shi ke nan.’
Ya ci gaba da cewa,’lokacin da na dawo daga gona ban gan shi ba, ban damu ba, don a wadansu lokutan ya saba zuwa wurin ‘yan uwansa yara su dauki lokaci mai tsawo suna wasa, daga bisani sai ya dawo gida a lokacin da ba ka tsammani. Lokacin da hankalinmu ya fara tashi shi ne lokacin da matana suka shaida mini cewa Liman bai dawo gida domin ya ci abincin rana ba, sannan ga almuru ya kawo jiki. Na ce musu su kwantar da hankalinsu, kodayake zuciyata ta ba ni cewa akwai abin da ya faru’ inji Malam Muhammad.
Malam Muhammad ya ce, daga nan sai ya je ya shaida wa mahaifinsa, wato Kakan yaron Malam Muhammad Liman, wanda Malami ne mai karantar da addinin islama, kuma shi ne limamin garin, abin da ya faru, daga nan sai suka dunguma suka je suka sanar da mai garin na Koso. Daga nan ne aka gayyato jama’a aka shaida musu bacewar marigayi Muhammad Liman. Sai aka shiga nemansa har zuwa tsakar dare, kamar karfe 3 na dare sannan aka huta, sai bayan da aka idar da sallar asuba aka ci gaba.
Daga bisani ne mutanen gari suka koma wajen kakar yaron, watau Fatima, suka matsa mata, a karshe dai ta amsa cewa lallai su ne suka kashe yaron tare da kawarta Amina da kuma Zhitsu Aliyu.
Malam Muhammad Abubakar, daya ne daga cikin abokan mahaifin marigayin, ya shaida wa Wakilinmu cewa,’’ ina dawowa ba tare da bata lokaci ba sai muka shirya taron addu’a, inda muka sauke Al’kur’ani tare da yin wadansu addu’o’in. Muna cikin haka ne aka sanar da mu wadanda suka yi aika-aikar, nan da nan muka tinkare su. Sai dai mun fara ne da Zhitsu Aliyu wanda bai musa abin da suka aikata ba, don kuwa ya shaida mana cewa, ya yi amfani da magani ne ya wuce da marigayin a lokacin da ya fito daga gidan Kakarsa Fatimah Sadaka, ya je ya yanka shi.’
Muhammad Abubakar ya shaida wa Wakilinmu cewa, tuni matasan gari suka kori daya daga cikin mayun da aka gano a garin na Koso, mai suna Ya Bago, da iyalinsa, kuma suka yi musu kashedin kar su kuskura su sake dawowa wannan garin. Malama Aisha Muhammad, wadda aka fi sani da Adishetu, ‘yar shekara 28 da haihuwa, ita ce mahaifiyar marigayin, ta bayyana wa Wakilinmu yadda al’amarin ya faru kamar haka, ’da gari ya waye, bayan da ya gama gaishe ni,sai na aike shi wurin wata ‘yar uwata inda ya amso mini agushi. Bayan da ya dawo sai na sake aikensa ya sayo mini kukar da na yi amfani da ita domin miyar sauran tuwon da muka ci. Daga lokacin shi ke nan rabuwarmu ke nan.’’
Malama A’isha ta yi bayyanin cewa , ‘’Na yi imanin duk mai rai mamaci ne, a matsayina na musulma na yarda da kaddara, sai dai abin da ya dore mini kai shi ne yadda aka yanka shi, sannan kuma suruka ta wadda na dauka a matsayin uwa ita ce ta kasance da hannu dumu-dumu cikin lamarin, inda aka gano cewa an ba ta wadansu sassa na namansa da kansa, kuma suka shanye jininsa. Allah ne Ya ba ni shi,shi ne kuma zai ba ni wanda ya fi shi.’’
Alhaji Kolo Koso, shi ne shugaban matasan garin, ya bayyana cewa, tuni suka dauki matakin kakkabe irin wadannan mutanen daga garin nasu, inda suka kori Ya Bago da iyalinsa, kuma ba za su yarda Fatima Sadaka da kawarta Aminah Wusa da Zhitsu Aliyu su sake dawowa garin ba.
Malam Muhammad Liman, shi ne limamin garin, kuma Kakan marigayin, ya bayyana marigayi Muhammad da cewa da yaro ne mai kwazo da sanin ya kamata, duk da shekarunsa kadan ne.
Ya cigaba da cewa, ‘Saboda irin kwazon da ya nuna a makarantun boko da na islamiyya ne ya sa muka yi shirin tura shi birnin Zariya wurin dan uwan mahaifinsa a cikin kakar bana domin ya yi karatu sosai a can.’’Ya bayyana asarar marigayin da aka yi da cewa abu ne mai cin rai, don kuwa yaron ya dauko halaye ne irin na manya, wanda jama’a da dama ke yi wa kallon yana iya zama babban mutum.
Ya ce, ‘’kai dan Jarida, wannan asarar ba ta iyayensa kadai ba ne,asara ce wadda ba ta tsaya a jihar Neja kadai ba,Najeriya ce baki daya ta yi asara. Dalili kuwa shi ne, Allah Ya ba marigayin kaifin basira da hikima kuma ga kuma ilimi fiye da yadda kake tsammani.’’
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘Yan sandan jihar Neja, ASP Ibrahim Abiodun Gambari, ya tabbatarb da faruwar lamarin, inda ya yaba wa al’ummar garin na Koso, kasancewar duk da zafin abin da aka aikata ba su dauki doka a hannunsu ba. Ya tabbatar da cewa, rundunar za ta tabbatar an hukunta duk wanda ke da hannu wajen aikata wannan mummunan aikin.