Yadda kamuwar Trump da COVID-19 za ta shafi zaben Amurka

Shugaban ya kamu cutar ne mako bayan ya ce wa Amurkawa kar su damu da ita domin “ba kowa take kanwa ba” sai tsofaffi da masu ciwon zuciya. Yanzu dole sai ya killace kansa daga shiga cikin mutane har sai ya warke; kazalika zai dakatar da yawon yakin neman zabe. Kwanaki biyu da suka gabata, […]

Yadda kamuwar Trump da COVID-19 za ta shafi zaben Amurka

Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump

Shugaban ya kamu cutar ne mako bayan ya ce wa Amurkawa kar su damu da ita domin “ba kowa take kanwa ba” sai tsofaffi da masu ciwon zuciya.

Yanzu dole sai ya killace kansa daga shiga cikin mutane har sai ya warke; kazalika zai dakatar da yawon yakin neman zabe.

Kwanaki biyu da suka gabata, Trump ya soki babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar Democrat, Joe Biden, da cewa yana yawan sanya takunkumi, kuma ba ya iya tara jama’a a wurin yakin neman zabe kamar nasa.

Zuwa yanzu babu tabbas game da ko Shugaban zai iya halartar babban taron mahawarar ‘yan takarar shugaban kasar da ke tafe a ranar 15 ga Oktoba.

Zaben Shugaban Kasar Amurka na ranar 3 ga watan Nuwamba, 2020, zai gudana ne wata daya bayan kamuwar Mista Trump da cutar.

Cutar ta kama mutum miliyan 7.2 a Amurka wadanda ta yi ajalin sama da mutum 200,000 daga cikinsu.

Da ma dai a sha yin korafi kan yadda Trump ke kin sanya takunkumin kariyar COVID-19 da kuma kin yin nesa-nesa yayin kasancewa tare da mutane kamar yadda tsarin kariyar cutar ke bukata.

A shekara 74, shugaban ya fada cikin rukunin mutanen da suka fi hadarin kamuwa da cutar da kuma mutuwa ta sanadiyyarta a Amurka.

Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta Amurka (CDC) ta ce masu shekaru 64-74 su ne kashi 80 cikin 100 da wadanda cutar ta kashe a kasar.