Yadda Kanawa ke alhinin rasuwar Ghali Umar Na’Abba
Ghali Umar Na’Abba ya rasu da sanyin safiyar ranar Laraba a Abuja.
Wasu daga cikin al’ummar Kano sun bayyana rasuwar tsohon shugaban majalisar wakilai, Ghali Umar Na’Abba a matsayin babban rashi ga jihar da ma kasa baki daya.
Ghali Na’Abba ya rasu ranar Laraba a Abuja yana da shekara 65 a duniya.
Wasu Kanawa da suka zanta da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) sun bayyana marigayin a matsayin mai ilimi, bin doka da oda da kuma neman cigaban kasa.
Wani Darakta a ma’aikatar gwamnatin tarayya, Abdullahi Nura, ya ce marigayi Ghali Na’Abba ya ba da gudunmawa wajen ci gaban Jihar Kano da ma kasa baki daya.
Ya kara da cewa “Marigayi Na’Abba yana karfafa mutane su zauna lafiya da juna kuma su tsaya a kan gaskiya.”
Malam Aliyu Aminu, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Kano, ya bayyana marigayin a matsayin mai taimakon jama’a.
A cewarsa, Ghali Ba’a ba ya taimaka wa talakawa da mabukata wajen inganta zamantakewa da tattalin arziki.
Shi ma, Ashiru Abubakar, wanda tsohon dan majalisa ne, ya ce marigayin dan siyasa ne da ke tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin mutane.
Alhaji Ismail Sani, ya ce ya samu rasuwar Ghali Na’Abba cikin kaduwa, ya kuma bayyana shi a matsayin mai tawali’u.
Ya kuma bayyana marigayin a matsayin mai tsoron Allah wanda halinsa da rayuwarsa suka kasance wajen yi wa al’umma hidima.
Salihu Tanko Yakasai, babban mataimaki na musamman kan kafafen yada labarai na zamani ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya yi addu’ar Allah Ya jikan mamacin.
Ya kuma bayyana marigayin a matsayin babban dan siyasa da ya sadaukar da rayuwarsa wajen ci gaban jiharsa da kasa baki daya.
Har ila yau, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, a cikin sakon ta’aziyyarsa, ya yi addu’ar Allah Ya jikan marigayin.
Kazalika, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, wanda ya bayyana a matsayin cikakken dan siyasa wanda ke nufin alheri ga kasar nan.
Za a yi jana’izar marigayi Na’Abba a yau a Kano.