‘Yadda kanena da surukina suka sace dana suka kashe bayan sun karbi kudin fansa’

A ranar Litinin da ta gabata ce al’ummar Unguwar Sabo Abeokuta a Jihar Ogun suka wayi gari da labari mai daga hankali inda kanen mahaifi da wan mahaifuya suka sace wani  yaro dan shekara bakwai suka yi garkuwa da shi kuma suka kashe shi suka jefa gawarsa a kogi bayan sun karbi kudin fansa daga mahaifinsa. […]

‘Yadda kanena da surukina suka sace dana suka kashe bayan sun karbi kudin fansa’

A ranar Litinin da ta gabata ce al’ummar Unguwar Sabo Abeokuta a Jihar Ogun suka wayi gari da labari mai daga hankali inda kanen mahaifi da wan mahaifuya suka sace wani  yaro dan shekara bakwai suka yi garkuwa da shi kuma suka kashe shi suka jefa gawarsa a kogi bayan sun karbi kudin fansa daga mahaifinsa.

’Yan sanda ne suka yi nasarar kama wadanda ake zargi da garkuwa da yaron da suka hada da kanen mahaifin yaron da yayan mahaifiyar yaron wanda mahaifin yaron yake rikonsa sama da shekara tara sai kuma wani mai dan acaba wanda shi ma kakanninsu daya da mahaifin yaron da kuma wani mai sayar da tsire da a gidansa suka fara boye yaron kafin su kashe shi.

Aminiya ta zanta da mahaifin yaron, Alhaji Abdulhamid Musa Cindo inda ya bayyana yadda lamarin ya auku cewa “A ranar Larabar makon jiya wadanda ake zargin suka dauke dansa dan shekara 7 mai suna Abdulmalik. Duk da cewa ba shi suka shirya dauka ba, yayansa suka nufa. Bayan an yi Sallar Isha suka dauki yaron, ya sansu duk ’yan uwansa ne suka kira shi suka saya masa biskit suka hau babur suka tafi da shi. Mu muna masallaci ba mu sani ba sai daga baya wani Bayarabe yake fada mana ya ga lokacin da wadansu suka dauki yaron a babur. Mahaifiyar yaron Hajara ita ta lura ba ya cikin ’yan uwansa, sai ta ankarar da mu, nan da nan muka bazama nema daga nan na sanar wa ’yan sanda sai suka ce mu saurara sai bayan awa 24.”

Ya ce ana cikin haka da safe sai wani ya kira shi a waya yana magana da Ingilishi ya ce ga yarona a Obada wata unguwa a Abeokuta. “Sai na ce dama neman yaron muke, ya rike mana shi zan zo in karbe shi in ba shi tukwici. Sai ya ce masu garkuwa da mutane ne, don haka idan ina son yaron sai na ba shi Naira miliyan biyar, na ce ba ni da su. A karshe suka yarda za su karbi Naira dubu 300 bisa shawarar da ’yan sanda suka ba mu, sai na tura aka kai musu kudin inda suka bukata a Oke Mosu bayan Ofishin Gwamnan Ogun,” inji shi.

Ya ce bayan sun karbi kudin sai suka ci gaba da kiransa suna fada masa wai ba za su saki dansa ba, an fada musu shi mai kudi ne, don haka za su wuce da shi Legas sai ya ce musu Allah na nan.

Mahaifin ya ce ’yan sanda ne suka gayyace shi ofishinsu, “Da na isa sai suka karbi wayata suka sanya lambobin waya hudu a cikinsu akwai lamba biyu a ciki, suka tambaye ni wane ne na ce masu kanena ne ubanmu guda da shi, dayar lambar na aje ta da sunan Abdullahi sai dai ban tantance wane Abdullahi ba ne. Nan take ’yan sandan suka shaida min cewa wadanda suka yi garkuwar na kusa da ni ne, amma kada in kuskura in fada wa kowa, sai sun saki yaron sannan a kama su,” inji shi.

Ya ce, “Wani abin mamaki shi ne wadanda suka saci yaron da su aka yi ta aikin nemansa, addu’o’in da muka shirya a masallacin kofar gidana duk da su aka yi. Haka suka rika shiga cikin gida suna bai wa mata hakuri suna nuna alhininsu, har suna cewa wannan abu su aka yiwa. Sai daga baya Hassan  ya zo yana cewa, ya samu Naira dubu 90 kanensa ya turo masa daga Ghana ya kuma turo wa matarsa Naira dubu 10 don haka zai je ya sayi babur. Sai na ce masa ya bari ranar Litinin in cika masa Naira dubu 50 ya saya domin dubu 100 ba zai samu babur mai kyau ba. To a wannan lokaci ne na fara zarginsa domin bayan na biya kudin fansar ne.”

“Ko a lokacin na ji a jikina sun kashe shi, koda aka shirya za a je a taho da shi a Legas da suka ce sun kai shi. Sai suka ce ba su san inda yake ba daga bisani suka ce sun kashe shi sun jefa a ruwa. Mutum uku daga cikinsu ’yan uwana ne na jini kuma na kusa. Wanda ya shirya dauke dan nawa kanena ne mahaifinmu daya, tare muke da shi a Jihar Ogun duk wani abin da dan uwa yake yi wa nasa na yi masa kuma ina kan yi masa. Hatta rigar da ke wuyansa lokacin da ’yan sanda suka kama shi ni na ba shi, haka shi ma Nura Habibu dan uwan matata ce. Ni na dauko shi daga Sakkwato bayan na auri kanwarsa na rike shi a matsayin babban yarona, na bude masa shago yana kasuwanci a kofar gidana, komai nawa na banki babu wanda bai sani ba, tare da kanwarsa karama na rike su wacce na aurar bara. Shi kuma Hasan dan acaba  kakaninmu daya da shi. Wannan abu Allah ne Ya kawo don haka na bar maSa al’amarin. Ba ni na kama su ba, hukuma ce ta kama su, ita ke da alhakin bincike ta yi wa wanda ta samu da laifi hukunci daidai da laifin da ya aikata,” inji shi.

 

Yadda na gano daya daga cikin barayin  yaron- Adgboke

Ibrahim Adebgoke aboki ne ga Alhaji Cindo ya shaida wa Aminiya yadda ya fara gano Hassan Okada wanda shi ne yake waya da Alhajin kuma shi ne ya je ya karbo kudin fansar. Ya ce “Lokacin da za a kai musu kudin fansar sai na dauki shatar mota na batar da kama na bi bayan wanda ya je ya kai kudin, kwastam sai na ci karo da wani matashi da bakaken kaya rike da leda a hannu. Wannan ya faru a yammacin Alhamis da aka ba su kudin fansar. Washegari da safe sai na ga matashin ya zo ya gaida Alhajin. Na ce ban yarda da shi ba, shi na gani jiya da yamma a wajen da aka kai kudin fansa rike da leda. Bayan ya bar wajen sai na ga ya shiga wani kango da ke bude a bayan gidan Alhajin sai na yi kamar zan yi fitsari na labe a gefe.

Sai na jiyo shi yana waya yana zage-zage yana cewa Alhaji an fada min kana da kudi don haka ka turo mana kudi. Sai na sake zuwa wajen Alhaji na ce an kiraka yanzu? Wannan yaron ne a kangon da ya shiga yana kiranka ta waya don haka ka sa a kama shi. Nan ma Alhaji ya ki amincewa domin bai zaci haka ba, sai daga baya Allah Ya sa aka kama su.”

 

‘Abin da ya sa muka yi garkuwa da yaron’

Aminiya ta zanta da wadanda ake zargin su hudu inda kanen Alhaji Cindo, mai suna Faruk Dila ya ce shi ne ya kashe yaron. Shi kuma Hassan Okada wanda ’yan sanda suka samu kudin fansar a dakinsa ya shaida wa Aminiya cewa Faruk Dila ne ya shirya garkuwar saboda yana bukatar kudin da zai yi aure na uku. “Ya fada min yana son yin aure domin sun rabu da matarsa ta farko ta biyun kuma ta mutu a dakinsa, don haka yake bukatar kudi ya yi aure. Ya ce min zai kashe yaron saboda ya gane shi, kuma ya jefa gawar a ruwa,” inji shi

Nura Habibu wanda dan uwar matar Alhajin ne ya shaida wa Aminiya cewa, ba ya da hannu a lamarin, sai dai akwai wani mutum da ake kira Abubakar wanda ya zo daga Arewa shi ma dan uwan Alhajin ne, “Da Abubakar ya zo ba ya da waya sai ya ce in ba shi aron waya da layi, sai na ba shi, da wannan wayar yake kiran Faruk Dila. Yanzu Abubakar ya gudu, bayan ya dawo min da wayar bayan kwana uku, sai jami’an tsaro suka bibiyi wayar suka kama ni da ita.” inji shi.

Muhammad Bello mai sayar da tsire da ake zargin an boye yaron a dakinsa ya shaida wa Aminiya cewa alakarsa da Hassan Okada yana kiransa ya zo ya kai shi inda yake sayar da nama.

Aminiya ta samu labarin cewa Muhammad Bello da Hassan Okada sun taba shirya garkuwa da wani dan sanda inda suka karbi fansar Naira miliyan daya.

Da yake gabatar wa manema labarai wadanda ake zargin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi ya yi kira ga jama’a su rika taka-tsantsan da wadanda suke tare da su. “In har dan uwa zai wa dan uwansa wannan to wa za a amince mawa?” Ya yi tambaya.

Tuni dai aka yi jana’izar yaron, Abudulmalik Cindo a garin Sabo Abeokuta a ranar Talatar da ta gabata.