Yadda kani ya jawo ’yan banga suka kashe yayansa kan Naira dubu 16
Al’ummar Unguwar Makera da ke gundumar Kufena a karamar Hukumar Zariya da ke Jihar kaduna sun samu kansu a cikin halin dimauta sakamakon yadda wani saurayi dan shekara 16 mai suna Muhammadu Bisallah ya jagoranci ’yan banga suka kashe yayansa mai suna Ayuba Bisallah dan shekara 19 bisa zargin yayan nasa da sace masa Naira […]

Al’ummar Unguwar Makera da ke gundumar Kufena a karamar Hukumar Zariya da ke Jihar kaduna sun samu kansu a cikin halin dimauta sakamakon yadda wani saurayi dan shekara 16 mai suna Muhammadu Bisallah ya jagoranci ’yan banga suka kashe yayansa mai suna Ayuba Bisallah dan shekara 19 bisa zargin yayan nasa da sace masa Naira dubu 16.
Wa da kanin dai uwarsu daya ubansu daya kuma dukkansu suna zaune ne a gida daya a Unguwar Makerar.
Aminiya ta ziyarci unguwar da lamarin ya faru inda ta tarar da al’ummar unguwar sun yi cirko-cirko suna tattaunawa a kan wannan lamarin mai cike da takaici
Mahaifin samarin biyu Malam Bisallah Zakari cikin kuka ya yi wa wakilinmu bayani kan yadda lamarin ya auku inda ya ce: “A ranar Juma’a na tasa su mun tafi gona, kamar yadda na saba duk safiya da musalin karfe shida nake sa su a gaba mu tafi gona. Mu kai kamar karfe 8:00 muna aiki kafin kowa ya dawo ya tafi nasa wurin, to haka muka yi muka tafi a ranar da safe. To da misalin karfe 7:30 sai marigayin ya baro mu a can gonar ya dawo gida, ashe akwai sabani a tsakaninsa da dan uwansa, kanin yana zargin cewa wai ya dauke masa Naira dubu 16. A lokacin na san da maganar sai na ce masa tunda zargi ne ba ka da tabbacin haka, ka yi a hankali kada ka yi abin da zai kawo sabani a tsakaninku. Bayan na tafi Kaduna a ranar shi kuma kanen bai ji shawarar da na ba shi ba, sai ya je ya gayyato ’yan banga wadanda suke Unguwar Dankali suka zo suka kama yayan nasa suka tafi da shi can ofishinsu.”
Ya kara da cewa “Ko me ’yan bangan suka yi masa? Allahu a’alamu, amma dai da alamar sun yi masa mummunan duka wanda a sanadiyyar haka har muka kai shi makabarta kansa yana zubar da jini kuma da alamun hakarkarinsa duk sun karya su da duka.”
Ya ce “Bayan sun gama la’anta shi ne aka zo da shi gida, kuma cikin ’yan mintina kadan, Allah Ya dauki rayuwarsa, iyakar abin da na sani ke nan. Amma dama ana zargin ’yan bangan nan cewa sun saba irin wannan lamari na dukan kawo wuka ga wadanda suke tuhuma, domin ko a kwanan baya haka suka kashe dan makwabcinmu ta hanyar irin wannan mummunan azaba da suke gana wa mutane idan suka shiga hannunsu.”
Ya ce a yanzu haka maganar da ake yi akwai wani yaro ma da ke kwance har yanzu shi ma haka suka yi masa irin wannan duka suka yar da shi a bayan gari. “Don haka irin wannan rashin hankali da yaron nawa ya yi tare da shi da wadannan marasa hankali ’yan banga ’yan uwansa ya cutar da ni kwarai da gaske. Sai dai kawai in yi hakuri in bar wa Allah. Amma ’yan sanda sun zo sun dauki hoton gawar yaron tare da tattara bayanai kuma shi kanin nasa yana hannunsu tare da wadansu daga cikin ’yan bangan uku wadanda ake zargi da kashe min da, ina jira in ga yadda za a yi,” inji shi.
Wakilinmu ya ziyarci ofishin ’yan sanda na danmagaji a karamar Hukumar Zariya, domin jin halin da ake ciki, amma sai ya tarar Babban Jami’i mai kula da ofishin wato DPO ya tafi Kaduna. Sai dai wani dan sanda da ya nemi a sakaye sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce suna rike da ’yan banga uku tare da kanin marigayin wanda shi ne ya jagoranci kashe yayan nasa. “Muna ci gaba da bincike tare da lalubo wanda duk yake da hannu a lamarin don gurfanar da su a gaban shari’a,” inji dan sandan.