Yadda Kano ke samar da madarar Naira biliyan 2.2
Kowacce daga cikin cibiyoyin guda 100 tana iya adana lita miliyan 146 na madara
Madara muhimmin abinci ne da ake bukata domin samun sinadarai masu ginawa da ƙara ƙarfi da lafiyar jiki. Bincike ya nuna cewa mutane biliyan shida ne ke shan madara a duniya, wanda ya sa shan madarar saniya da kiwon dabbobi ya zama wani vangare na rayuwar ɗan adam.
Dubban mata Fulani suna samun kuɗaɗen shiga ta hanyar sayar da madara ga ɗaiɗaikun mutane ko jama’a ko ’yan kasuwa, waɗanda suke sha ko sarrafa shi domin amfanin kasuwanci.
Lura da muhimmancin madara ga rayuwar ɗan Adam da kuma ƙoƙarin rage haɗarin da ke tattare da shan ta, Hukumar Haɓaka Noma da Kiwon Dabbobi ta Jihar Kano (KSADP) ta zuba jarin Dala miliyan 8.03 don gina cibiyoyi 100 na tattara madara a jihar, da nufin tallafa wa makiyaya domin su wadatar da buƙatun masana’antar madara da sauran masu buqatar ta.
An tallafa wa Ƙungiyar Masu Sayar da Madarar Saniya ta Kasuwar Ƙofar Wambai da ɗakin ajiye kayan sanyi domin tabbatar da tsafta da kuma ingancin madara.
- An kashe ɗan banga da yin garkuwa da ’yan mata 6 a Neja
- An dakatar da dagaci kan zargin saran maraya da adda
Shugaban ƙungiyarsu, Alhaji Muhammad Alaramma, ya ce harkar kiwon dabbobi na bunqasa sosai a Jihar Kano sakamakon matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka ta hanyar hukumar KSADP, wadda ta ba wa ƙungiyar tallafin wurin ajiye kayan sanyi.
Lita dubu hamsin a kullum
“Kullum ana sayar da aqalla lita 50,000 na madara, amma wani lokaci ba ya kaiwa haka, saboda qarancin madara a Kano a halin yanzu. Mutane sukan kawo shi daga Jos da Bauchi da Jama’are da sauran wurare.
“Wurin ajiyar kayan sanyi da aka ba mu yana da matuqar amfani, amma ƙalubalen shi ne ba ya amfani da lantarki mai amfani da hasken rana. Amma mun yi yarjejeniya da wani wanda ya karɓi hayar wani vangare na wajen, shi kuma a madadin haka yana ba mu wutar lantarki, daga injin ɗinsa.
“Naira 200 muke karva a kan kowane bokitin madara da aka kawo ajiya daga hannun ’ya’yan qungiyarmu, waɗanda sun kusa mutum 20,000,” in ji shugaban ga wakilinmu.
Barazanar ƙwayar cuta
Madarar da aka sarrafa na iya harbuwa da ƙwayar cuta idan ba a kiyaye ta ba, wanda hakan na iya shafar lafiyar ɗan Adam. Masana sun bayyana cewa kashi 70 cikin 100 na cututtukan da ke damun xan adam suna da alaƙa da dabbobi. Don haka shan madara mara tsafta na iya zama babban haxari ga lafiyar ɗan Adam.
Shirin Haɓaka Noma da Kiwon Dabbobi na Jihar Kano, tare da tallafin Bankin Ci-gaban Islama (IsDB) da Asusun Inganta Rayuwa (LLF), na gina cibiyoyi 100 na tattara madara a Kano don inganta samuwar madara domin kasuwanci da ɗaga darajarta, da kuma magance matsalar qarancinta da rashin ingancinta a harkar kasunwancin.
Wani ƙwararre kan kiwon dabbobi a KSADP, Dakta Garba Saleh, ya bayyana cewa ana gina cibiyoyin madarar ne domin tattara ta daga makiyaya domin a ci gaba da raba wa masu sarrafawa.
“Manufar ita ce tabbatar da tsafta da ingancin madara, ta yadda duk sinadaran da suka dace ba za a lalata su ba. Idan babu cibiyar tarawa za a iya rasa mahimman sinadaran da ke cikin madara cikin sauƙi.
“A ƙarƙashin shirin, za a kafa cibiyoyin tattara madara (MCC) guda 100 inda a halin yanzu an kammala 40 daga ciki.”
Yawa da darajar madarar
Ƙwararrun a fannin kiwon dabbobi ya bayyana cewa ana sa ran kowace cibiyar za ta ajiye aƙalla lita 28,000 na madara a mako, kimanin lita miliyan 1.46 a kowace shekara. Hakan nan nufin yawan dararar cibiyoyin guda 100 za su adana a shekara ya kai lita miliyan 146.
Ana kuma sa ran makiyaya 25 za su riƙa ba wa kowane MCC madara, ta yadda kowane MCC zai riƙa samar da Naira 4,622,872 a duk mako.
A wata guda zai samar da kimanin Naira miliyan 18.5, wato Naira miliyan 221 a duk wata. Hakan na nufin za a samu jimillar Naira biliyan 2.2 (Dala miliyan 1.4) daga MCC 100 ɗin a shekara.
Yadda cibiyoyin suke
Kowace cibiya tana amfani da wutar lantarki mai amfani hasken rana kuma tankin sanyaya abubuwa wanda aka qera da qarfe mara yin tsantsa; da kuma injin tata da famfo da na’urar xumama ruwa da kayan gwajin madara da na tsaftar muhalli da mazuban tattara madara da rijiyoyin burtsatse masu tankin sama.
Zuwa yanzu, an gina cibiyoyi biyar a Doguwa, huɗu a Albasu, huɗu a Danbatta, sannan uku-uku a Dansoshiya a Ƙaramar Hukumar Kiru da Garko da Garun Malam da Tofa da Kura da Dawakin Tofa.
Makiyaya na murna
Wani Bafulatani makiyayi a ƙauyen Ɗansoshiya, Muhammad Major, ya ce duk da cewa an an kammala cibiyar tara madarar yankinsu, amma dai ba ta fara aiki ba, amma duk da haka makiyaya suna farin ciki da kafa cibiyar.
Muhammad Major ɗan shekara 52 ya ce, “An kammala cibiyar Ɗansoshiya amma ba ta fara aiki ba, don haka Kano muke kai madara mu sayar. Amma idan ya fara aiki, nan zan riƙa kaiwa a ba ni kuɗina ba sai na kashe kuɗin mota zuwa Kano ba, ka ga na rage kashe kuɗi.”
Manyan kanfanoni irin su L&Z sukan yi amfani da cibiyoyin da KSADP ta kafa baya ga nasu na ƙashin kansu, ci-gaban kasuwancinsu.
Barazanar manyan kamfanoni
Wasu da ke harkar kuma sukan yi amfani da madarar gari ko waken suya, domin haɗawa da madarar shanun da suka samu daga masu kawo musu, wadda ta yi karancin sosai.
Wata Bafulatana da ke kawo nono Kano daga Bunkure, Hauwa’u Abubakar, ta ce ba a kafa irin wannan cibiya a yankinsu ba. Hauwa’u takan kashe kuɗin mota N1,000 a kullum zuwa Kano inda take sayar da bokiti uku zuwa biyar na nono kowanne a kan kimanin N6,5000, a duk tafiya.
Hauwa ta ce, “Kullum nan (Kano Line) nake kawo bokiti uku zuwa biyar na nono, inda muke sayar da duk bokiti a kan N6,500. Wasu a nan suke saya su kai Kasuwar Ƙofar Wambai su sake sayarwa, amma na fi so in tsaya a nan a saboda in rage kashe kuxin abin hawa.”
Shi ko Abdulmuɗɗalibi Sani, wanda ke sana’ar fura da nono, yakan sayi nono ne a wurin matan Fulani a cibiyar da ke Kano Line. Ya ce ya sayi bokiti shida saboda ya ya fi arha idan aka kwatanta da na Kofar Wambai, inda dillalai kan yi amfani da damar su ƙara farashi.
Ya ce ƙananan masu sayen nono irinsa na fama da manyan kamfanoni irin su L&Z da ke harkar, waxanda suke da nasu cibiyoyin tattara madara inda suke saya kai-tsaye daga hannun makiyaya.
Abdulmuɗɗalibi ya ce “Manyan mutane da ke saya kai-tsaye daga wurin matan Fulani su ke haddasa ƙarancin madara da tsadarsa, amma kuɗinsa bai kai haka ba.”
Wai mai sayar da madara, Awwal Sa’id wanda yakan sayi bokiti biyar zuwa shida a Kano Line ya ce, abin da ya jawo shi shi ne cinkoson da ke Ƙofar Wambai da kuma yadda dillalai ke sanya farashi.
Yadda za a bunƙasa harkar
Wani qwararre a fannin kiwon dabbobi a Hukumar KSADP, Dakta Garba Saleh, ya yi imanin cewa kasuwancin madara zai samu ci-gaba sosai a nan gaba.
Ya bayyana cewa ko da yake a halin yanzu Nijeriya ba ta samar da madarar da za ta wadatar da buqatar cikin gida, za a kai lokacin da qasar za ta riƙa fitar da ita zuwa ƙetare idan aka haɓaka tare da tallafa wa harkar.
Ya ce ƙasashen Kenya da Uganda da Rwanda sun bunƙasa fannin madararsu ne ta hanyar taimako da tallafa wa ƙananan kamfanoni domin fitar da ita zuwa qasashen qetare.
Qalubalen harkar
Sai dai kuma shanu ’yan qasa na daga cikin ƙalubalen. Dakta Saleh ya bayyana cewa shanu ’yan qasa ba sa samar da madara mai yawa, domin abin da suke samarwar a yini guda bai fi lita uku zuwa biyar ba, idan aka kwatanta da shanun qasashen waje da ke ba da lita 50 a kullum.
Sannan kuma ciyawa ’yar ƙasa ba ta da sinadaran gina jiki sosai, sannan yin kiwo ba tare da gandun kiwo ba, babu riba.
Ya ce domin magance wannan matsala Hukumar KSADP tana aiki a wani fili mai fafin hekta 3,000 inda za a noma nau’ika daban-daban na ciyayi da aka ƙara wa inganci, irin su nau’in Nafia da Stylo da kuma Gamba.
Hukumar KSADP na kuma aikin yin barbarar shanu ’yan qasa da na waje domin ganin sun samu siffofi da nagartar ’yan ƙasar waje.
Kafa Ma’aikatar Kiwon Dabbobi zai iya kawo sauyi ta hanyar samar da ingantaccen abincin dabbobi wanda zai inganta samar da madara mai nagarta da yawan gaske wanda hakan zai kawo riba mai tsoka.