Yadda Kano ta yi rashin tsoffin kwamishinoni cikin kwana 3

Tsofaffin kwamishinonin sun rasu ne cikin kwana uku bayan fama da rashin lafiya.

Yadda Kano ta yi rashin tsoffin kwamishinoni cikin kwana 3

Jihar Kano ta yi rashin tsofaffin kwamishinoni guda biyu da suka yi aiki a gwamnatocin baya a cikin kwanaki uku da suka wuce.

Wadanda Allah Ya yi wa rasuwar su ne tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu, Alhassan Muhammad Dawaki da kuma Kwamishinar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki Barista Zubaida Damakka.

Dawaki ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya, yana da shekara 79 kuma ya bar mata da ’ya’ya 15.

Dawaki ya yi Kwamishinan aikin noma a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau, sannan a zamaninsa a kaddamar da baburan Adaidaita sahu a Kano.

Wani na hannun daman marigayiya Damakka, wanda tsohon babban mataimaki ne na musamman ga gwamna kan kafafen sadarwa na zamani, Abubakar Aminu Ibrahim, ya tabbatar cewa ta rasu ne a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya, ta bar mijinta da ’ya’ya uku.

An yi jana’izarsu a Kano ranar a Lahadi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

A wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Mataimakin Gwamnan, Ibrahim Garba Shu’aibu ya fitar, ya bayyana Dawaki a matsayin fitaccen mutum da ake mutuntawa wanda rasuwarsa ta girgiza mutane da dama.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana kaduwarsa game da rasuwar Dawaki, inda ya yi addu’ar Allah Ya yi masa rahama tare da bai wa ’yan uwa hakurin rashinsa.

NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Kauce Wa Gadon Ciwon Suga

’Yan bindiga sun lalata tashar wutar lantarkin da ake ginawa a Kogi

Trump ya bai wa Elon Musk muƙami a Gwamnatin Amurka

Dalilin da ke haddasa yawaitar katsewar lantarki — EFCC