Yadda kara mai rikitarwa ta auku a tsaunin Zuma
Tsaunin Zuma na daya daga cikin mashahuran al’amura da suka zame wa kasar nan tambari a idon duniya, saboda manuniyar albarkatun kasa ta gano babbar tulluwar tsaunin da ke cikin karamar Hukumar Tafa a Jihar Neja. Tun daga babban birnin tarayya, Abuja zuwa Kaduna ana iya hango tulluwar tsaunin Zuma. Tsayin wannan tulluwa daga kasa […]
Tsaunin Zuma na daya daga cikin mashahuran al’amura da suka zame wa kasar nan tambari a idon duniya, saboda manuniyar albarkatun kasa ta gano babbar tulluwar tsaunin da ke cikin karamar Hukumar Tafa a Jihar Neja.
Tun daga babban birnin tarayya, Abuja zuwa Kaduna ana iya hango tulluwar tsaunin Zuma. Tsayin wannan tulluwa daga kasa zuwa sama ya kai mita 725. Tambarin wannan tsauni ya bayyana karara a kan takardar kudin Naira 100.
Tarihi ya nuna cewa, kabilar Gbagyi na fakewa a bayan tsaunin lokacin da ake yake-yake tsakanin kabilu. Baya ga alfanun da aka samu daga wannan tsauni a zamanin da, yana kuma tattare da dimbin al’amurra masu rikitarwa, wadanda suka samo asali daga imani da camfe-camfen kabilar
Shaharar da wannan tsauni ya yi ta sa mazauna kauyukan da ke kewaye da shi suka yi matukar razana yayin da gefen tsaunin da ke fuskantar Zuba ya yi kara da sautin bam, kuma ya yanke ya fado kasa, ya tarwatse da matsananciyar kara, tare da haifar da kurar da ta turnuke har saman tsaunin tamkar hadari, da maraicen Laraba, 11 ga Nuwamba, 2015.
Yayin da Aminiya ta ziyarci gefen tsaunin da al’amarin ya auku, bangaren da ya bantare daga jikinsa ya tarwatse ya taru a karkashin tsaunin, tare da kurar da ta zubo, daidai alamar da bantarewar ta bari.
Aminiya ta ziyarci kauyen Chachi a cikin karamar Hukamar Tafa, inda wannan shahararren tsauni yake, yayin da dagacin kauyen, Malam Musa Abubakar, wanda kuma shi ne mai kula da tsaunin da kewayensa a gargajiyance, ya ce ba zai iya tuna lokacin da wannan al’amari ya faru a tsaunin ba.
Mazauna kauyukan da ke kewaye da tsaunin sun bayar da bayanai mabambanta game da al’amarin da ya auku ranar Laraba. daya daga cikin sojojin da ke gadi a daura da tsaunin, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya ce shi da abokan aikin sa sun ji wata kara mai kama da tsawa, wacce ta zo tare da girgiza kasar kewayen tsaunin, kuma kura ta turnuke sama. Ya kara da cewa shi ya yi zaton bam ne.
Wani mazaunin Chachi mai suna Malam Alhassan ya ce karar da al’amarin ya haifar ta jefa mazauna kewayen tsaunin cikin matsananciyar firgita, a yayin da kuma wadansu mazaunan suka ce dabbobin daji da na gida da ke wannan muhallin sun ranta a na kare cikin firgita, a yayin da kuma wadanda suke kan tsaunin su ma suka fado suka yi ta mutuwa. A cewarsa, mazauna kewayen tsaunin sun bayyana fashewarsa a matsayin wani al’amari ne mai ban mamaki.
Aminiya ta tuntubi Hukumar Binciken Albarkatun kasa ta Najeriya (Nigeria Geological Surbey Agency) a daya daga cikin jami’an hukumar ya ce ba za su iya bayar da wani bayani mai gamsarwa ba sai sun ziyarci inda al’amarin ya faru, sun gudanar da binciken kimiyya a tsaunin.