Yadda karancin kudi ya takaita tafiye-tafiyen ’yan Najeriya lokacin zabe

Alamu sun nuna akwai yiwuwar samun karancin masu fita zabe sakamakon karancin kudi da ake fama da shi.

Yadda karancin kudi ya takaita tafiye-tafiyen ’yan Najeriya lokacin zabe

Alamu na nuna cewar za a iya samun tsaikon mutane wajen fita zaben Shugaban Kasar ranar Asabar sakamakon canjin kudin da ya haifar da karancin takardun kudi a Najeriya.

Aminiya ta zanta da wasu ’yan Najeriya wadanda suka yi niyyar yin balaguro don yin zabe amma karancin kudi na neman murkushe wannan aniyar nasu.

Tun bayan kaddamar da sabbin takardun Naira N1000, N500 da kuma N200 a watan Disamba, jama’a suka shiga walagigin samun kudin a bankunansu na kasuwanci, injinan ATM da kuma wajen masu sana’ar PoS.

Matafiya a Abuja sun koka

Yayin da Aminiya ta zaga wasu daga cikin tashoshin motar da ke Birnin Tarayya, ta gano tsirarun matafiya ne kadai ke shirin yin tafiya don yin zabe sakamakon karancin kudi.

Aminiya ta lura da yadda wasu daga cikin direbobi ke karbar kudi ta hanyar ‘transfer’, yayin da wasu kuma suka fi son a ba su kudi hannu, maimakon tura musu ta asusun ajiyar bankunansu.

A tashar mota ta Gwagwalada, Emeka Johnson, wanda ke shirin yin balaguro zuwa Jihar Imo, ya ce zai yi tafiyar ne duk da karancin kudi da ake fama da shi.

“Karancin Naira wani abu ne na daban, sannan wajen masu sana’ar PoS da muka dogara da su duk da tsadar kudin caji, su ma ba su da kudin. Na fahimci lamarin ya fi kamari a Gabas,” a cewarsa.

A tashar mota ta Zuba kuwa, Solomon Ogunleye, wanda ke shirin tafiya Jihar Ekiti, ya bayyana yadda aka kara kudin mota.

“A farkon shekarar nan na biya kudin mota N4,000, amma yanzu suna cewa sai N7,000, yayin da wasu direbobin kuma suke dagewa kan cewar sai dai a ba su tsabar kudi. Wannan kadai na iya zama silar da zai hana mutane yin tafiya don yin zabe,” in ji shi.

Shi kuwa wani injiniya mai suna Nsikak Epenyong, cewa ya yi daga Abuja zuwa Akwa Ibom a mota mara AC N11,000 ne, yayin da a mota mai AC kuma N13,000 amma a yanzu sun koma N16,500 da kuma N18,500.

Borno

A Maiduguri kuwa, fasinjoji na rige-rigen zuwa tashar motar gwamnati ta ‘Borno Express Mass Transit’ don biyan kudin motarsu ta injin PoS.

Da wakilinmu ya ziyarci tashar, daya daga cikin jami’an tashar, Adamu Yakubu, ya ce suna samun dandazon fasinjoji da ke son yin tafiya ciki da wajen Jihar Borno.

“Kamar kowace kakar zabe, yawan fasinjojin da ke yin tafiya ya karu a wannan lokaci, duk da karancin kudi da jama’a ke fama da shi. Kana iya ganin motocin sufuri na jihohin daban-daban, kuma kowace mota na dauke da injin PoS da fasinja zai biya kudinsa wanda zai tafi asusun gwamnati kai tsaye.

“Mutane suna zuwa nan don tafiya Kano, Kaduna, Gombe, Filato, Nasarawa, Katsina da sauransu tun daga satin da ya wuce,” in ji shi.

Kazalika, Yakubu ya ce mutane na yin tafiye-tafiye zuwa Kananan Hukumomi, musamman Kudancin Borno.

Wani daga cikin fasinjojin, Muhammad Bayero, ya shaida wa wakilinmu cewar zai tafi Kaduna don yin zabe a can.

“Abu ne mai kyau ka tafi gida ka yi zabe, akalla ko ba komai mutum zai kasance da iyalinsa, musamman lokacin zabe saboda babu wanda zai ce ga abin da zai iya faruwa. A takaice dai wannan shi ne dalilin da ya sa zan tafi gida,” a cewarsa.

Ita ma wata fasinja, Naomi Eleja, wadda ta ke shirin tafiya Karamar Hukumar Biu, ta ce a garin Miringa ta yi rajistar katin zabenta, kuma a can ne za ta iya yin zabe cikin kwanciyar hankali.

“Na shirya yin tafiya tare da ’yan uwana amma ni kadai ce wacce zan tafi saboda yanayin da ake ciki. Ba ni da kudin da zan iya biya wa kowa, ga kuma matsalar karancin kudi wadda ta shafi wasu daga cikinsu.

“Mutane da yawa ba za su yi zabe a wannan karon ba sakamakon yanayin da ake ciki a kasar nan, kuma abubuwa sai ci gaba da lalacewa suke yi kullum,” in ji ta,

Yayin da Aminiya ta ziyarci tashar mota ta ‘yan kasuwa, ta riski motoci da dama a tsaye babu mutane yayin da wasu fasinjoji ke korafi kan yadda wasu direbobi suka ki karbar kudi a asusunsu na banki.

“Ko dai ka biya madarar kudi ko kuma ba za ka yi tafiya ba. Muna fuskantar matsaloli da yawa,” in ji ta.

Kano

A Kano kuwa, mutane sun shiga damuwa kan yadda suke son yin tafiya don yin zabe amma karancin kudi ya haifar da tsaiko.

Wakilinmu a Jihar Kano, ya ziyarci fitacciyar tashar motar Unguwa Uku, inda ya iske tashar ana ci gaba da hada-hada amma ba kamar yadda aka saba gani ba, musamman a lokacin karatowar zabe.

An samu raguwar fasinjoji da ke yi wa tashar tsinke don yin tafiye-tafiye gabanin lokutan zabe.

Nasiru Ibrahim, wanda shi ne shugaban lodin motocin Kaduna a tashar Unguwa Uku, ya alakanta karancin fasinjoji da ake samu da wahalar kudi da ake fama da shi a hannun mutane.

“Mutane ba sa zuwa ko ina; wannan yanayi ya bata mana rai. Kamar yadda ka ke gani tashar ba a yin hada-hada kamar yadda aka saba.

“Mutanen da suka zo da niyyar yin tafiya suna komawa gida saboda babu kudi a hannu ko a wajen masu PoS sakamakon matsalar intanet.

“Gaskiya, tsiraru ne ke yin tafiya. Mun shafe shekaru masu yawa a nan; amma ba mu taba fuskantar yanayi irin wannan ba. Tashoshin mota suna zama babu masaka tsinke a lokutan da zabe ke karatowa,” a cewarsa.

Wani direba ya shaida wa wakilinmu cewar da yawan fasinjojin da ke son yin tafiya na komawa gida.

“Muna zaune a nan muna jiransu. Suna zuwa suna kuma komawa gida. Da yawansu suna shirin yin tafiyar saboda zabe. Don haka wannan zai iya shafar zaben kai tsaye.

“Kuma yadda ran mutane ya baci game da wannan matsala, na iya haifar da koma baya ga zaben baki daya. Mutane za su iya zama a gida su ki fitowa wajen zabe,” a cewarsa.

Lamarin haka yake a tashar manyan motoci da suka fi yin jigilar mutane musamman zuwa Gabashi da Kudancin kasar nan.

Aminiya ta gano cewar motocin na tsaye inda suke jiran fasinjoji, sai dai yawan fasinjojin da ke shirin yin tafiyar ‘yan kasuwa ne da mata.

Da yake bayyana mana abin da ke faruwa, Judo Ogbiano, ya ce mutane na son yin tafiye-tafiye amma rashin kudi na hana su.

Ya ce: “Da yawan mutanen da ka ga ni a nan tura kudinsu ta Intanet suka yi. Najeriya ta shafe sama da shekara 60 amma a maimakon a samar mana yanayi mai kyau amma an jefa mu cikin wahala. Sai yaushe ne za mu fara jin dadin kasar nan?”

Shi kuwa, Collins Ogbonna, ya ce ba zai yi zabe ba saboda ba shi da kudin yin tafiya.

“Tun farko a Legas ya kamata na kada kuri’a ba a Kano ba. Amma kamar yadda ka ke gani na kwaso wasu daga cikin iyalina. Kudin abun hawa ya yi tsada sannan direbobi na kukan babu gas.”

Legas

Wani mai gyaran waya a ‘Computer Village’ a yankin Ikeja a Legas, Nnamdi Felix, ya ce ba zai samu yin tafiya Inugu don kada kuri’arsa ba.

“Ana shan wahala amma wannan wata dama ce da zamu yi sadaukarwa, mu jure wahalar da za a sha,” in ji shi.

Kazalika, wata mazauniyar yankin Oke-Aro, Ebere Achusi wadda akwatin zabenta na Ibadan, ta ce ba za ta yi zaben 2023 ba saboda ba za ta yi tafiya ba.

“Babu kudi a hannun mutane. Sai ka shafe awanni a banki ko wajen masu sana’ar PoS da ke zabga wa mutane caji mai yawan gaske. Sannan kudin mota ya yi tsada a wannan lokaci. Ina takaicin ba zan iya amfani da dama tab a wajen sauya kasar nan.

“Ba a can na ke da zama ba. Ba a iya kudin mota kadai zan biya ba dole ne na nemi inda zan sauka sannan bin titin zuwa da dawowa a rana daya akwai hatsari a gare ni,” a cewarta.

 

Daga Hamisu Kabir Matazu (Maiduguri), Salim Umar Ibrahim (Kano), Yvonne Ugwuezuoha (Lagos), Seun Adeuyi (Abuja) da Abubakar Muhammad