Yadda kare ke sansano cutar daji
Wani binciken kimiyya ya bayyna yadda nau’ukan Karen Jamusawa (German Shepheard) le sansano cutar dajin mama daga tufafin da aka yi daurin kirji suka taba nonon mace. Binciken, wanda cibiyar Curie da ke Paris ta gudanar ya gano cewa bayan wata shida da horar da karnuka, an smau tabbcin cewa 100 bisa 100 suna iya […]
Wani binciken kimiyya ya bayyna yadda nau’ukan Karen Jamusawa (German Shepheard) le sansano cutar dajin mama daga tufafin da aka yi daurin kirji suka taba nonon mace. Binciken, wanda cibiyar Curie da ke Paris ta gudanar ya gano cewa bayan wata shida da horar da karnuka, an smau tabbcin cewa 100 bisa 100 suna iya gano ciwon daji.
Kan yadda aka gudanar da binciken kuwa, masu binciken sun tattara tufafin masu fama da cutar daji mutum 31. Sun yi amfani da tsarin bayar da la’ada, wato inda aka horar da karnukan sun gano bambancin da ke tsakanin suturun da suke sanye a jikin mai cutar daji da kuma lkayan da aka saba sanyawa.
“An aiwatar da aikin ne tamkar yadda ake yin wasanni,” a cewar kwararren masani kan karnuka Jacky Edperton.
Karnuka za su iya bincika akwatunan kaya, kuma idan aka gano cutar, sai su tsira tsinin hancinsu. A karon farko,m karnukan sun gano masu fama da cutar mutum 28 daga cikin 431 na mata masu cutar daji, amma zagaye na biyu na gwaji karnuka sun kara kwarewa har ta kai ga sun cimma gacin 100 bisa 100.
Masu binciken sun shirya yadda za a ci gaba da gudanar da wnanan bincike a tare da dimbin karnuka
Rukunin masu binciken sun ce yankunan karkara da ake da karancin kayan aiki na zamani za su ci gajiyar wannan binciken, sabanin yadda yanzu a kasashen da suka ci gab ne kawai ake da na’urorin binciken gano cutar daji ta “cancer,” ta hanyar mamamogramm.
“A wannan kasashe, akwai likitocin da sulka kware wajen tarairayar cutar daji da masu aikin tiyatar fidar yanke cutar, amma a yankunan karkara ana da karancin kayan aikin gano inda cutar take,” a cewar shugaban da ke kula da yadda ake gudanar da aiki, Isabelle Fromantin.