Yadda karin jini ya jawo yarinya ta rasa kafa

Mahaifin wata yarinya ya zargi wani asibiti mai zaman kansa da yin sakaci da nuna rashin kwarewa inda ya yi sanadiyar gutsire kafar ’yarsa. Mahaifin yarinyar mai suna Adamu Ya’u dake zaune a gida mai Lamba 22, Layin Sarki, Falladan a karamar Hukumar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna ya zargi asibitin Salama Infirmary Clinic […]

Yadda karin jini ya jawo yarinya ta rasa kafa

Mahaifin wata yarinya ya zargi wani asibiti mai zaman kansa da yin sakaci da nuna rashin kwarewa inda ya yi sanadiyar gutsire kafar ’yarsa.

Mahaifin yarinyar mai suna Adamu Ya’u dake zaune a gida mai Lamba 22, Layin Sarki, Falladan a karamar Hukumar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna ya zargi asibitin Salama Infirmary Clinic Maternity and Surgery da ke Kwangila ’Yangoro a hanyar Samaru da jawo rasa kafar ’yarsa a dalilin karin jini.
Malam Adamu Ya’u wanda ke aikin gadi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kuma yake da inshorar lafiya a wancan asibiti, ya shaida wa Aminiya cewa ’yarsa Rukayya Adamu mai kimanin shekara hudu zuwa biyar tana da ciwon sikila sai dai bai taba kwantar da ita ba, sai dai ana kai ta asibiti lokaci-lokaci. “Sai dai a wanan karon an kai ta ne sanadiyyar zazzabin cizon sauro, kuma na kai ta asibitin ne da kafafunta a ranar 6/10/2016. Bayan an duba ta sai aka
kwantar da ita, aka ba ta magunguna aka ce za a yi mata karin ruwa. To sai suka ce sun nemi hanyar jijiya a hannunta ba su samu ba, suka ce ta kafa aka samu aka kara mata ruwa, bayan nan aka ce ba jini sai an kara mata. Aka debi jinina aka sanya mata ta kafa kamar, sai jinin ya yi ta gardama domin likitan bai tsaya ya yi aikin da kansha ba ya umarci kananan ma’aikatan jinya ne su sa duk da samun tangarda wajen aikin. Don haka rashin kware ne a ganina ya jawo wannan matsala,” inji shi.
Ya ce jinin ya rika dawowa baya kuma da ya yi musu magana sai suka ce, ya kyale su ba abin da ya sani ba aikinsa ba ne. “Haka na zuba musu ido, mahaifiyar yarinya sai kuka take ta yi saboda ganin irin azabar da yarinyar take sha. Daga nan kafar Rukayya ta kumbura, kwanammu hudu a asibitin suka sallame mu na ce a haka kafa a kumbore kuma mun zo da yarinya da kafarta za mu koma da ita a kafada? Sai na ce ban yarda ba sai muka fara sa-in-sa da likitan na ce ba zan yarda a sallame ni a wannan hali ba. Sai ya ce ba abin da zai iya min. Sai na samu wani Dokta Bola na gaya masa abin da ake ciki. Sai ya ce in yi hakuri in bi umarninsa ba abin da zai faru. Suka ce idan muka koma gida mu rika sa kafar a kan filo, kuma mu rika sa wa kafar kankara za ta sace,” inji shi.
Ya ce: “Bayan mun dawo gida a ranar ba mu yi barci ba saboda kukan yarinyar, gari na wayewa muka dawo musu sai suka ce wai ba mu bi shawarar da suka ba mu ba na sa mata kankara da dora kafar a kan filo. Sai suka tura mu Asibitin Koyarwa na Jami’a (ABUTH), Shika suka ce ba za su iya ba.”
Malam Adamu Ya’u ya ce bayan da suka ga likita ya ba su gado, sai likitan ya shaida musu cewa za a yanke yatsun kafar yarinyar. “Sai na ce ban yarda ba saboda kafar yarinyar lafiya lau take lokacin da na kai ta Asibitin Salama, na fita na bar su, washegari sai na ga yatsun sun bushe yarinyar na ta kuka hankalina ya tashi na koma na ce na yarda a yanke amma a fada min dalilin da ya jawo haka. Bayan an yanke yatsun sai kuma abu ya ki sauki suka ce kafar ce gaba daya ta lalace dole sai an yanke ta. Na ce yaya za a yanke wa yarinyata kafa? Suka ce ba laifinsu ba ne domin ba su suka fara aikin nan daga farko ba. Kuma ai laifina ne saboda me ya sa zan bude inshorar lafiya da Asibitin Salama? Sai na ce musu ai ni abin da na dauka Salama asibiti ne mai zaman kansa kuma yana da kwararrun likitoci,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Sai suka in sa hannu a yanke kafar. Wannan ya nuna cewa asibitin Salama ne sanadiyyar lalacewar kafar ’yata har ta kai aka yanke don haka zan dauki matakin da ya dace don bi mata hakkinta.”
Wakilinmu ya samu bayanai daga wadansu da suka gudanar da aikin yanke kafar da ba su so a ambaci sunansu, cewa sanadiyyar sa jini ta kafa ne ya jawo lalacewar kafar saboda rashin samun
hanyar da ta dace, wanda hakan ya sa cutar tetanus ta shiga ta lalata kafar yarinyar. Sun ce ganin yadda kafar take sai da jagoran aikin ya kira Babban Daraktan Asibitin Salama Clinic kan yadda aka yi hakan ta faru da yarinyar.
A Asibitin Salama Clinic, likitan da ya duba Rukayya, mai suna Dokta Bishop ya ce “Lallai ni na duba wannan yarinyar kuma na ba ta duk kular da ta dace, an kwantar da yarinyar a wannan asibitin domin tana da lalurar ciwon sikila, kuma jininta ya yi kasa da 15, saboda haka na ba da umarni a samu jini a kara mata, kuma ni na tura su Asibiti Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello ganin yadda kafar ta zama, saboda sun fi mu kwararrun likitoci. Amma Babban Daraktan Asibitin nan ya kira ni ya ce me ke faruwa da Rukayya Adamu domin an kira shi daga Asibitin Shika ana neman karin bayani a kan yadda aka kula da ita. A sanina duk abin da suke zargi na rashin iya aiki da kula da ’yarsu ba haka ba ne.”
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Babban Jami’in Asibitin Farfesa Lawal Khalid inda a zuwa na farko ya ce ta dawo washegari zai bincika, bayan ta koma sai ya ce ta yi hakuri har yanzu bai ga babban jami’in da ya jagoranci aiki ga yarinyar ba, amma zai neme ta bayan ya karbi bayanan abin da ya wakana amma har ya zuwa hada wannan rahoto bai kira ba.
Masu bibiyan lamarin sun ce zai yi wuya wakilinmu ya samu wani bayani daga Hukumar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello saboda mai Asibitin Salama ma’aikacinsu ne.