Yadda karnukan Coci suka kashe dan Nijar a Legas
Wasu manyan karnuka irin na kasar waje guda biyu da ke gadin wani coci a yankin Abule Egba sun halaka wani dan kasar Nijar da ke zaune a Legas.
Wasu manyan karnuka irin na kasar waje guda biyu da ke gadin wani coci a yankin Abule Egba sun halaka wani dan kasar Nijar da ke zaune a Legas.
Lamarin da ya faru a ranar Talatar makon jiya bayan da marigayin mai suna Hashiru Isa da ke sana’ar tireda a kasuwar Allah Gatan Kowa da ke yankin Abule Egba ya tashi daga kasuwancinsa cikin dare.
- Yara 10 sun mutu sakamakon shan gurbataccen magani a Yemen
- An kama tabar wiwin miliyan N4 za a kai wa ’yan ta’adda
- NAJERIYA A YAU: ‘Mu ke da alhakin sayen audugar Al’adar ’ya’yanmu’
Marigayin ya rufe tiredarsa da misalin karfe 1:30 ya nufi gida, sai ya ci karo da karnukan wadanda suka fito daga Cocin suka shiga layin da marigayin ke tafe suka far masa da cizo da yakushi.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa, karnukan sun yi ta cizon marigayin suna yakushin sa har suka kai shi kas.
Haka kuma duk sanda ya yi yunkura tashi, sai su kuma far masa da cizo, haka suka yi ta yi masa har ya galabaita ya kasa tashi, inda daga bisani aka kai shi babban asibitin gwamnati da ke yankin Orile Agege, ya ce ga garinku nan.
Mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundai, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, rundunar na binciken lamarin tare da kokarin kama karnukan.
Malam Nasiru, Sakataren Kungiyar Matasan Arewa reshen Unguwar Gatankowa, ya shaida wa Aminiya cewa, kungiyar ta yi yunkunrin shiga lamarin domin ganin an ba mamacin hakkinsa, sai dai ’yan uwansa sun janye maganar bayan da suka karbi kudi Naira miliyan daya da dubu tamanin daga hannun masu karen.
“Abin takaicin shi ne ’yan sanda sun fara bincike, inda suka bukaci faston cocin da matarsa su kawo takardun likita na kula da karnukan, domin a tabbatar ko suna rike da karnukan bisa ka’ida.
“Sai dai a lokacin da ’yan sandan ke kokarin yin hakan, sai masu karnukan suka zagaye, suka bai wa ’yan uwan mamacin Naira miliyan daya, suka kuma biya kudin asibiti da ya kwanta Naira dubu tamanin, daga nan sai suka janye maganar,” inji shi.