Yadda kasafin kudin 2018 ya dara na bara – Gwmana Masari

A Litinin din farkon makon da ya wuce Gwamnan jihar Katsina Tsohon Kakakin Majalisar Wakillai ta Tarayya Aminu Bello Masari ya gabatar da kasafin kudi na shekara ta 2018 a Majalisar dokoki ta jahar Katsina karkashin Kakakin Majalisar Abubakar Yahaya Kusada. Kamar yadda Gwamna ya ce, jihar ta yi kasafin kudin mai taken,”kasafin kudi a […]

Yadda kasafin kudin 2018 ya dara na bara – Gwmana Masari

A Litinin din farkon makon da ya wuce Gwamnan jihar Katsina Tsohon Kakakin Majalisar Wakillai ta Tarayya Aminu Bello Masari ya gabatar da kasafin kudi na shekara ta 2018 a Majalisar dokoki ta jahar Katsina karkashin Kakakin Majalisar Abubakar Yahaya Kusada. Kamar yadda Gwamna ya ce, jihar ta yi kasafin kudin mai taken,”kasafin kudi a zahirance” har na zunzurutun kudi Naira bilyan Naira 211.497.191.095.00). Gwamnan wanda yayi dogon bayani akan kasafin kudin 2018, inda ya bayyana cewa, manyan ayyuka ne za su samu kashi 75 cikin 100 yayin da kashi 25 cikin 100 za su tafi ga ayyukan yau da kullum. bangaren tattalin arziki na da kashi 26.8 cikin 100, yayin da bangaren jin dadi da walwala zai samu kashi 29.5 cikin 100. Sannan sashen ayyukan ci gaba zai samu kashi 32.4 cikin 100. Kashi 4.3 cikin 100 zai tafi a harkar lafiya da ayyukan gwamnati, inda fannin shari’a zai samu kasha.4 cikin 100.

Gwamnan ya ce, Majalisar dokokin na da digo 2 cikin 100 na kasafin kudin na shekarar 2018 mai zuwa in Allah ya kaimu. A sashen Ko-ta kwana kuwa, ma’aikatar kudi, wadda ta hada har da abin da ya shafi bankuna da shi kansa Babban bankin Najeriya CBN za su samu kashi 4.6 cikin 100. 

Gwamnan har’ila yau ya ce, shi dai wannan kasafin kudi na da shirye-shiryen da suka hada da batun ilmi da kiwon lafiya da noma da samar da ruwan sha da muhalli da ma’aikatar ayyuka da sufuri tare da batun tsaro duk suna daga cikin abubuwan da za a mayar da hankali a kansu. 

Sai Gwamna Masari ya ci gaba da cewa,”saboda haka, a nan bangaren ma’aikatar ilmi ne suka fi samun kaso mai tsoka har na kashi 20 cikin 100. Ma’aikatar kiwon lafiya ce za ta samu kashi 11 cikin 100, inda ta ayyuka ke da kashi 11 cikin 100, sai ta ruwa mai kashi 9 cikin 100,ta noma na da kashi 7 cikin 100,sai bangaren muhalli mai kashi 5 cikin 100.

Da ya juya kan kudin shiga na shekarar ta 2018,Gwamna Aminu Bello Masari ya ce,adadin kudin da aka saka a kasafin kudin na 2018 sun kai Naira bilyan N167.634.213.235.00), wadanda suka hada da Naira bilyan 10.277.807.500.00 a matsayin kudin shigar cikin gida yayin da ake sa ran samun Naira bilyan 131da milyan 100 daga asusun Gwamnatin tarayya. 

A nan Gwamna Masari ya yi nuni da irin bambancin da aka samu na kashi 30 cikin 100 tsakanin kasafin kudin 2018 da na 2017. Sai dai kuma Gwamna Masari ya ce, an samu nasara har ta kashi 55 cikin 100 a kasafin kudin 2017 mai karewa nan gaba kadan. Gwamna Masari yayi matashiya akan kasafin kudin shekara ta 2016 inda ya ce, an samu nasara ta kashi 32 cikin 1000 ne, amma yana sa ran za a samu nasarar da za ta kai kashi 90 cikin 100 a wannan kasafin kudin 2018.

Anasa jawabin, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina Alhaji Abubakar Yahaya Kusada, tabbatar wa Gwamnan da goyon bayan majalisar ga gwamnatinsa ya yi. 

Shugaban ya ce, kasancewar yana daga cikin ayyukan majalisar na ganin cewa an aiwatar da tsare-tsaren gwamnati bisa doka da oda, saboda haka za su ba wannan kasafin kudi kyakyawar kulawa a cikin lokaci, domin bayar da dama ga al’umma don shan romon mulkin dimokuradiyya. 

Kamar yadda ya ce,shekara ta 2017 ta fuskanci kalubalen tattalin arziki, har ta kai ga gwamnati ba ta samu damar gudanar da ayyukanta na bunkasa jiha ba, wato “Restoration Agenda,” amma duk da haka gwamnati ta yi kokari, musamman wajen biyan albashin ma’aikata sabanin wasu jihohin. Sai dai ya yi kira ga gwamnan da ya kara daukar mataki a kan batun hanyoyin samun kudin shigar jahar bisa ga tanadin doka domin cigaba da aiyukan raya kasa.

Daga Ahmed Kabir S/kuka a Katsina

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50