Yadda kasuwanci ya kasance a Kalaba bayan zabe
Wasu daga cikin ’yan kasuwa da aka ji ta bakinsu a Kalaba, babban birnin Jihar Kurosriba, yadda kasuwancinsu yake bayan kammala zabe, sun koka da rashin ciniki da kuma na zirga-zirgar jama’a, sakamakon wasu abokan hulda sun yi tafiya zuwa garuruwansu na asali domin yin zabe. Wakilinmu ya leka Layin Bagobiri Unguwar Hausawa domin jin […]
Wasu daga cikin ’yan kasuwa da aka ji ta bakinsu a Kalaba, babban birnin Jihar Kurosriba, yadda kasuwancinsu yake bayan kammala zabe, sun koka da rashin ciniki da kuma na zirga-zirgar jama’a, sakamakon wasu abokan hulda sun yi tafiya zuwa garuruwansu na asali domin yin zabe.
Wakilinmu ya leka Layin Bagobiri Unguwar Hausawa domin jin ta bakin wasu daga cikinsu, yadda sana’arsu ke gudana bayan zabe. A kasuwar Doya, Malam Rufa’i Isma’il Sarkin Doya ya bayyana wa Aminiya yadda cinikin doya ke gudana. Ya ce “al’amuran kasuwancin yanzu sai a hankali, ka san kasuwancin yanzu da yake kowa hankalinsa ya koma kan zabe, ciniki ana yinsa amma sai a hankali. Muna sa rai tun da an yi zabe lami-lafiya muna sa rai ciniki ya dawo, sannan hankalin kowa ya kwanta,” inji shi.
Shi kuwa Musa Dalhatu Zarewa, wani mai sana’ar sayar da lemon zaki, ya shaida wa wakilinmu cewa “yadda nake yin cinikin lemo kafin lokacin zabe da kuma yanzu sai a hankali. Babu ciniki, domin jama’a duk sun yi tafiya. A da kafin zabe, ina sayar da lemon zaki akalla guda dari da hamsin amma yanzu da kyar nakan iya sayar da kwara tamanin saboda babu ciniki kuma ga karancin mutane,” inji Zarewa.
Shi kuwa Alhaji Abubakar Dan Shehu mai Albasa Kalaba, kokawa ya yi da cewa bayan karancin ciniki wata matsala da suke fuskanta ita ce ta takurawa da masu karbar jankali ke yi masu idan sun dauko kayan kasuwarsu daga Arewa zuwa Kudu kamar sun dauko wani abu ba kayan kasuwa ba. “Ka ga a da can muna kashe Naira dubu bakwai mu kawo kaya Kalaba amma yanzu tun daga jihohin Kudu maso gabas, Enugu da Ebonyi idan muka biyo, mafi karancin kashe kudi daga Naira dubu 60 zuwa 70 duk kudin hanya muke kashe wa masu karbar haraji, alhali babu ciniki yanzu. Shin da wanne za mu ji?” Inji Alhaji Abubakar.