Yadda kasuwancin furfure ke habaka a kauyen Esuk Mba
Duk da kasancewar ci gaba na zamani ta hanyar cinikayya ta bankunan kasuwanci da kuma yin amfani da katin debi da kanka (ATM), da ma yin amfani da hanyar sadarwa ta intanet; wasu daga cikin al’ummar Esuk Mba da ke karamar Hukumar Apabuyo ta Jihar Kuros Riba, har yanzu suna gudanar da cinikin Furfure (Ba-ni-gishiri-in- […]

Duk da kasancewar ci gaba na zamani ta hanyar cinikayya ta bankunan kasuwanci da kuma yin amfani da katin debi da kanka (ATM), da ma yin amfani da hanyar sadarwa ta intanet; wasu daga cikin al’ummar Esuk Mba da ke karamar Hukumar Apabuyo ta Jihar Kuros Riba, har yanzu suna gudanar da cinikin Furfure (Ba-ni-gishiri-in- ba-ka-manda).
Kasuwar Esuk Mba na ci kowace ranar Asabar tun daga misalin karfe bakwai na safe, ta nade kayanta misalin karfe sha biyu na rana. Kasuwa dai na tsallaken kogin Kwara ne, da ya yi iyaka da Jamhuriyar Kamaru ta yammacin Jihar Kuros Riba yayin da ta kudancinsa kuma ya yi iyaka da Jihar Akwa Ibom. Akasarin ’yan kasuwar kuma suna zuwa ne da hajoji daga Bakassi da Oron, Jihar Akwa Ibom suna sayarwa. Sai dai wani abu da zai iya burge mutane shi ne ba da takardun kudin Najeriya ko na Kamaru ake kasuwancin ba, a’a, ana yin huldar cinikin ce da kaya zuwa kaya, wato kayan amfanin gona, irin su wake doya da kuma shinkafa da kifi jatalande. Sauran su ne ayaba garin kwaki, manja da kuma mangyada. Bugu da kari, tufafi, sabulun wanka da na wanki, dunkulen magi, gishiri da kuma ganyen miya da sauran kayan ci-maka .
Aminiya ta ga kwakwaf a wannan kasuwa, inda ta riski wata mata mai suna Ekamma, tana son yin musayar karas da dankalin Turawa, domin a ba ta kankana tsakaninta da wani kwastomanta mai suna Aminu, da ya kai kankana da kabeji kasuwar. A cewar ta, bisa kiyasi za ta ba shi buhun karas biyu da na dankalin Turawa, shi kuma ya ba ta kankana guda 200. Bisa kiyasi, idan da Naira za a yi amfani da ita, buhun karas da na dankalin Turawa zai iya saya mata kankana guda 200.
Bayan barin wakilinmu kasuwar, ya zagaya inda ya sake ganin wani mai son a ba shi shinkafa, shi kuma yana sayar da manja. Nan ma aka yi kiyasin buhun shinkafa daya zai bayar a ba shi jarkar manja uku. Aminiya ta tambayi wata mata mai suna Ekwo Effoing, shugabar ’yan kasuwar bangaren mata cewa tun yaushe ne suka fara gudanar da wannan ciniki, sai ta ce: “Ni kaina na shafe sama da shekara talatin ina cin kasuwar nan kuma tarihin kasuwar nan ya samo asali ne tun daga kafuwar wannan kabila da ke nan hayin teku saboda matsaloli na sufurin mota ko babur. Abin hawa ba zai iya kawo mana kaya ba, mu kuma ba za mu iya zuwa birni mu sayo a kawo mana ba. Shi ya sanya muke wannan kasuwanci. Idan kana bukatar wani abu da ba ka da shi sai ka kawo wani wanda ya kawo kana bukata, sai ku yi musaya, amma ba mu yin amfani da kudi shi ya sanya ma babu ruwanmu da zullumin barayi. Za su iya kawo mana ziyara nan kasuwar, idan ma barawo ya zo ya yi sata, babu ta yadda za a yi ya tafi da kayan.” Inji ta.
Domin jin asali da tarihin wannan kasuwa ta Esuk Mba da kuma lokacin da aka kafa ta ta fara ci gadan-gadan, Aminiya ta tattauna da Okon Bassey, basaren kauyen Esuk Mba, inda ya bayyana cewa: “Wani Baturen Ingila ne mai suna Doe a 1947 ya kafa kasuwar nan kuma ya fara ta ne a harabar gidansa da ke wannan kauye, kafin daga bisani a shekarar ta koma wannan wuri da ka iske ta na dindindin.”
An tambayi kwararre kuma masani kan harkokin kasuwanci da sanin tattalin arziki, Dokta Aliyu Muhammad Wazirin Wusa, na Jami’ar Abubakar Tafawa balewa, Bauchi ko yake ganin duk da sauyi da ci gaba na zamani da aka samu, ana yin kasuwanci ta bankuna da kuma intanet har ma da yin amfani da katin debi-da-kanka, ko hakan zai iya kawo ci gaba da habaka tattalin arzikin wadannan al’umma na Jihar Kuros Riba, da ma kasa baki daya? Sai ya ce: “A halin gaskiya idan aka dubi mahimmancin abin da ingancinsa, hakan zai habaka tattalin arzikin al’ummar da na jihar har ma da kasa baki daya da kuma al’ummomin da suke huldar kasuwancin. Ka ga kayayyakin da ake kawowa nan sun bambanta da wadanda ake kawowa daga Arewa zuwa nan, sannan kuma akwai wadanda daga nan Kuros Riba ake kai su Arewa, tun da yanzu rike kudi ya zama hadari. In ka lura manomanmu da wasu ’yan kasuwarmu ba su san mahimmancin yin amfani da katin ATM ba. Ina ganin wannan hanyace mai tasiri kwarai”. Inji shi.