Yadda kasuwar amawali ta bude a Calabar
Ayuba Mukhtar matashi ne mai sayar da amawali (ko takunkumin da ake sakawa don hana shakar cututtuka) a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba. Amma fa ba sana’ar shi ba ke nan makwanni biyu da suka wuce. Ayuba ya rungumi wannan sana’a ne saboda bukatar amawalin ta karu tashi guda. Titunan Kalaba Kusan ko ina […]
Ayuba Mukhtar matashi ne mai sayar da amawali (ko takunkumin da ake sakawa don hana shakar cututtuka) a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba.
Amma fa ba sana’ar shi ba ke nan makwanni biyu da suka wuce.
Ayuba ya rungumi wannan sana’a ne saboda bukatar amawalin ta karu tashi guda.
Titunan Kalaba
Kusan ko ina mutum ya duba a titunan birnin Kalaba kowa na sanye da amawali.
Hakan dai ya biyo bayan dokra da gwamnatin jihar ta Kuros Riba ta kafa ne cewa dole kowa ya sa amawalin ko ya zauna a gida.
A cewar Gwamna Ben Ayade lokacin da yake kaddamar da dokar, “wannan wata gagrumar yekuwa ce mai taken ‘Ba Amawali, Ba Fita’….”
Don haka ne a hanyoyin jihar jami’an tsaro kan tare duk wata mota da ke wucewa, idan kuwa aka ga wand aba shi da amawalin to za a sauke shi—ko da kuwa direban motar fasinja ne.
Kasuwar amawali
Wannan mataki da hukumomi suka dauka ne ya sa amawalin ya yi kasuwa sosai, har ma wasu teloli suka shiga dinka shi, matasa irin su Ayuba kuma suka fara sara suna sayarwa.
Amma ga alama amawalin ya samu saosai har ya fi bukatar mutane, don kuwa farashin ya karye.
“Lokacin da na fara, ina sayar da ita naira N200; lokacin ba kowa ke da ita ba. Yanzu kuwa farashin ya fadi”, inji Ayuba.
Yanzu dai farashin ya dangnata wani lokacin akan sayar a kan N100, wani lokaci kuma, idan ya hau, N150, kamar yadda wani matashin a Unguwar Hausawa Layin Bagobiri yake cewa.
“Kasuwar na gudana babu matsala — muna sayar da ko wane daya a kan kudi N100-N150”, inji Shafi’u, wanda shi yakan dinka amawalin ma.
Jama’ar gari
Yayin da wasu daga cikin al’aummar gari ke korafi saboda matakan da hukumomi suka dauke wasu kuwa cewa suka yi hakan ya dace.
Muhammad Sami, wanda ake yiwa lakabi da No Wonder, na cikin wadanda suka gamsu da matakan.
“Matakin kare kai da aka umarce mu da mu dauka ina murna da shi. Abin da [kawai] ban goyi ba shi ne shigo da likitocin China zuwa Najeriya domin su duba lafitar wadanda coronavirus ta kama”, inji Muhammad Sami.
Shi kuwa Jamilu Garba aya yake sayarwa. Kuma a cewarsa akwai takura a saka amawalin.
“Numfashi na yi min wahala saboda ban saba ba gaskiya; yana takura min wajen shakar iska”, inji shi.
Amawali a kimiyyance
Madinka amawalin dai kan yi shi da kyallaye daban-daban daban masu launi daban-daban.
Hasali ma, lokacin da ya kaddamar da yekuwar saka amawali, Gwamna Ayade ya daura wani da aka yi da kyallen da aka dinka masa riga ne.
Sai dai kuma was una ganin ba ko wanne amawali ne ke bayar da kariya ba.
Don haka ne wakilin Aminiya ya tambayi Dokta Asuquo Edet na Babban Asibitin Kalaba yadda lamarin yake.
“Sanya amawali na cikin matakan kariya daga kamuwa da COVID-19, haka ma wanke hannu da ruwa da sabulu da kuma bayar da tazara tsakanin jama’a a wuraren da ake da cinkoson jama’a kamar kasuwanni da kuma wuraren Ibada.
“Mutane a yi hakuri a jure yin amfani da amawalin zuwa wani lokaci har a ga wucewar wannan annoba”, inji Dokta Asuquo.
Gwamnatocin jihohi a fadin Najeriya dai na ta daukar matakai don ganin cutar ta coronavirus ba ta shiga yankunansu ko ta yadu ba.
Sai dai babu inda aka bayar da muhimmancin ga rufe baki da hanci kamar a jihar Kuros Riba.