Yadda kasuwar bayan Sallah ke ci a Katsina
Yan kasuwa na barje guminsu a duk lokacin da aka ce ana wani biki ko shagali wanda zai mamaye yanki ko shiyya ko kasa baki daya, kamar shagulgulan Sallah. A wannan lokaci kusan babu wani sashe na kasuwanci da zai ce bai dara ba, baya ga karin farashin da akan samu walau ta hanyar yawan […]
Yan kasuwa na barje guminsu a duk lokacin da aka ce ana wani biki ko shagali wanda zai mamaye yanki ko shiyya ko kasa baki daya, kamar shagulgulan Sallah. A wannan lokaci kusan babu wani sashe na kasuwanci da zai ce bai dara ba, baya ga karin farashin da akan samu walau ta hanyar yawan masu son abin ko karancin abin sayarwa a kasuwa. To sai dai kuma duk da wancan tsalle da murna da dan kasuwa ya yi a wancan lokaci da zarar lokacin ya wuce sai ya dawo abin tausayi.
Kafin bikin Babbar Sallah,’yan kasuwa sun yi hidimomin kasuwanci musamman ta fuskar sutura da suka hada da yadi ko zannuwa da takalma da sauran kayan kwalliya. Teloli sun fantama, tare da sauran wasu nau’o’in kasuwanci. Amma ana cewa Sallah ta ba da baya, abin sai ya koma tamkar ma ba a yi ba domin wadansu har sun fara barci a wuraren kasuwancinsu.
Malam Abdullahi na daga cikin masu sayar da takalma ya kuma shaida wa Aminiya cewa, “Gaskiya tunda wannan hidima ta Sallah ta wuce, batun kasuwanci sai hakuri. Ka ga na sayar da takalmi har na Naira dubu biyu wanda a baya bai wuce Naira dubu daya da dari uku zuwa da biyar kafin Sallar. Amma yanzu, sai an yi da gaske a saye shi dubu daya da dari daya ko biyu.”
Alhaji Mamman wani dan kasuwa a garin Jibiya, cewa ya yi, abin da kawai zai ci gaba da taka wata rawa a yanzu bai wuce kayan abinci ba. “Yanzu in ba kayan abinci ba ina tabbatar maka cewa harkokin kasuwanci sun fara ja baya. Kasuwar bayan Sallah ce sannan ga shi cikin damina ne ake kuma tsakiyarta, mafi yawan kudaden da ke hannun mutane duk sun binne su a kasa tunda an gane muhimmancin noma,” inji shi.
Ga manyan ’yan kasuwa, wani da ya nemi a sakaya sunansa cewa ya yi, “Ai yanzu babban ma kalubalen da ke gabanmu shi ne, ganin an maido mana kudaden kayan da muka bayar. Mun ba mutane kaya don su samu na abinci amma koken da muke samu a wajensu shi ne, bashin da aka dauka da sunan cewa sai an yi albashi. Ka san Jihar Katsina jiha ce ta ma’aikata wadda in ba lokacin albashi ba to harkar kasuwa na samun nakasu. To kuma ga shi an yi Sallar kuma ba lokacin albashin ba, a hannu daya kuma duk an sa yi raguna na yin layya. Su kuma wadanda suka ba kayan nan abokan hulda ne na yau da kullum. Ka ga kuwa ba za ka ce kada a yi ba, tunda kai ma haka ne a wajenka. Sannan wani abu da na lura da shi a yanzu shi ne, a baya da zarar an ce an gama bikin Sallah ko lokacin da ake cikin hidimar, akwai shigowar baki wadanda ke yin sayayya saboda sababbin abubuwa da ake kawowa. To a wannan karon ba a samu haka ba,” inji shi.
Shin batun kasuwancin ga maza ya tsaya ko har da mata? Hajiya Hurera Mai’abinci a Tashar NARTO cewa ta yi, “Duk da mun saba ganin canjin yanayin kasuwa, amma dai a wannan lokacin ba a cewa ba a samu ba, tunda akwai baki masu shigowa ko fita suna kuma tsayawa don cin abinci. Ka ga abin sai muce an samu bakin gwargwado a lokacin bukukuwan Sallar nan. To amma yanzu da ta yi baya, sai muce sai dai abin da Allah Ya yi domin ba mu iya sanin abin da zai faru a gaba, amma alamu na nunawa cewar za a dan fuskanci karancin ciniki tunda na bayan Sallah ne. An kuma saba ganin haka ba tun yanzu ba, musamman a yanzu da ba kudi a hannun mutane sosai. Sannan ga karancin zirga-zirga da ake samu.”
Hajiya Hurera ta ce, abin ba mai dorewa ba ne, tunda can baya an saba ganin haka. Kuma su a sashensu na mata, baya ga sana’ar sayar da abinci da suke fitowa suna yi, akwai kananan kasuwanci da ake yi cikin gida, kuma ana samun na zubin adashi.
Aminiya ta lura cewa, batun daukar bashi a hannun ’yan kasuwa daga wajen abokan huldarsu ya yi karanci in aka kwatanta da baya, saboda mafi yawa masu sayayyar wadansu tun daga Karamar Sallah suka saya, wadansu kuma sai kusa ga Sallar. Sai dai akwai hasashen dawowar kasuwancin nan da ’yan kwanaki masu zuwa, domin dawowar alhazai daga aikin Hajji wadanda wasunsu sai sun dawo gida suke sayen kayan tsaraba.