Yadda kasuwar karnuka mafi girma take ci a Filato
Babbar kasuwar kare mafi girma a Najeriya tana ci a kauyen Dawaki da ke karamar Hukumar Kanke a Jihar Filato, inda ’yan kasuwar daga yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Kudu da kuma shiyyar Kudu mafi Kudu suke tururuwa don cin kasuwar. A kasuwar, wadda take ci a ranar kowace Alhamis za ka ga […]
Babbar kasuwar kare mafi girma a Najeriya tana ci a kauyen Dawaki da ke karamar Hukumar Kanke a Jihar Filato, inda ’yan kasuwar daga yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Kudu da kuma shiyyar Kudu mafi Kudu suke tururuwa don cin kasuwar.
A kasuwar, wadda take ci a ranar kowace Alhamis za ka ga karnuka manya da kanana daure da sarka rike a hannun mata da suka fito daga kauyen Dawaki da kuma wadansu kauyukan kabilar Angas don sayar da su a kasuwar da ke da nisan wadansu kilomitoci daga kauyen Dawaki.
Binciken Aminiya ya gano cewa daga farko an samar da kasuwar ne don sayar da tumakai da awakai da kuma sauran kayayyakin masarufi, amma a yanzu kasuwar ta zama babbar kasuwar sayar da kuka da karnuka da aladu da sauransu, inda ake zuwa daga Kano da Kaduna da Barno don a sayi kukar.
Kasuwar a yanzu za a iya cewa ta zama wata hanya da ke bunkasa kasuwanci tsakanin Arewacin kasar nan da kuma Kudanci har da sauran kasashen Afirka da suke makwabtaka da Najeriya da suka hada da Nijar da Chadi da Ghana da sauransu.
Tarihi ya nuna cewa kasuwar Dawaki ce fiye da shekara 300 da ta gabata, inda har zuwa yanzu take ci gaba da bunkasa.
Wani abu da yake bada mamaki shi ne yadda ’yan kasuwar da ke zuwa daga Kalaba da ke Jihar Kuros riba suke zuwa cin kasuwa cikin wani salo mai daukar hankali.
A lokacin da wakilin Aminiya ya ziyarci kasuwar ne da misalin 2 na rana, sai ya ji mutanen sun barke da ihu da kuma sowa, ashe hakan yana nuna cewa ’yan kasuwar karnuka daga Kalaba suka iso kasuwar.
Ana cikin hakan wata babbar mota da ake kira 911 dauke da wani keji da aka cika shi da karnuka da kuma jarkokin manja ta shigo cikin kasuwar.
Bayan motar ta shigo cikin kasuwar sai ’yan kasuwar suka nufi wurin da motar ta tsaya cikin sauri. Wadansu matasa biyar suka fito daga cikin motar, sannan suka fara gaisawa da ’yan kasuwar, daga nan aka fara saukar da jarkokin manja da tsintsiya da lemo da sauran ganyayyaki, sannan suka fara sayar wa mutane, sannan suka fara amfani da kudin wajen sayen aladu da karnuka.
Shugaban ’Yan Kasuwar Dawaki, Alhaji Sule Maidoki ya ce a shekaru masu yawa da suka gabata “kakanninmu da su ma kakanninsu suna cin kasuwar, zan iya cewa kasuwar ta kai shekara 300 da kafuwa.”
Maidoki wanda yake da daraja da kima a idon ’yan kasuwar, ya bayyana wa Aminiya cewa daga farko kasuwar tana ci a wurin da a yanzu ya zama kauyen Dawaki ne, inda sannu a hankali ta rika matsawa har ta dawo wurin da take ci yanzu.
“Kasuwar ta rika bunkasa, inda ya sanya mutane suka rika gina gidaje al’amarin da ya sanya kasuwar ta yi kadan, inda a shekarar 2016 aka dawo da ita wurin da take ci yanzu. Kasuwar tana kan titin zuwa karamar Hukumar Tafawa balewa da ke Jihar Bauchi, inda kasuwar take da tazarar kilomita 46 zuwa karamar hukumar.”
Ya ce ba iya karnuka ake sayarwa a kasuwar ba, ana iya samun kayayyakin masarufi da awakai da tumakai da man-ja da ’ya’yan itatuwa da sauransu.
Sakataren ’Yan kasuwar, Yatem Jeftha Dauda ya bayyana a yanzu kasuwar ba ta da rumfunan zamani, sannan ’yan kasuwa suna shan wahala a lokacin damina, inda ruwa yake musu duka ba tare da isasshen wurin fakewa ba.
Ya ce, “’Yan kadan din runfunan da suke kasuwar ma iska ta yaye rufinsu a watan Afrilun da ya gabata, kuma har zuwa yanzu gwamnati ba ta kawo mana dauki ba, duk da cewa tana samun kudin shiga daga wurinsu.”
Aminiya ta fahimci yawancin runfunan da ke kasuwar an yi su ne da itatuwa da ganyayyakin bishiya da kuma langa-langa, wadansu kuma an rufe su da jinka, amma akwai ofis-ofis da kuma manyan rumbunan ajiya da aka gina a kasuwar wadanda suka kara mata kyau. Maidoki wanda dan kabilar Angas ya ce kasuwar ta samu sunan Dawaki ne saboda hanyar dawakai ne wadanda suke safara daga Bauchi da Kano da kuma sauran jihohin Arewa tun lokacin mulkin mallaka.
“Daga nan bayan kasuwa ta fara ci sai mutane suka rika gina gidaje, sannan aka sa rada wa kauyen sunan Dawaki saboda wucewar da dawakan suke yi.”
Ya ce kasuwar tana ci duk Alhamis ne tsawon shekara ba yankewa, inda ta fi ci lokacin rani, “Ana sayar da awakai da tumakai da aladu, amma an fi sayar karnuka, kuma kasuwancinsu ya fi bunkasa kasuwar.”
Ya ce, “Yan kasuwa daga Jihar Kuros Riba da sauran jihohin Kudu mafi Kudu suna zuwa kasuwarmu don su sayi karnuka, sannan muna tura mutanenmu har zuwa Nijar da Chadi da kuma sauran garuruwan arewacin kasar nan neman karnuka.”
Ya ce, da rani ’yan kasuwa daga Kalaba sukan zo a manyan motoci da ake kira 911 kamar 13, amma idan lokacin damina ne ba sa wuce motoci hudu, “wani lokacin ma ba sa iya zuwa ranar kasuwa saboda motocin sun lalace, amma kwastomominsu suna jiransu har zuwa washegari.” Inji shi.
Ya ce, kasuwar takan samar da Naira dubu 70 zuwa 100 kowace ranar kasuwa, kuma ana samun kudin ne daga wurin ’yan kasuwar, domin duk abin da mutum ya kawo zai sayar akwai kudin da zai biya.
“Kowace jarkar manja muna karbar Naira 50, sannan haka muke karba a kan kowace dabba da aka kawo za a sayar. Amma saboda rashin kudi wani lokaci ana ragi. Misali idan wani ya zo da karnuka 10, sai mu ce ya biya kudin biyar, ga wanda ya kawo kifi da sauran kananan abubuwa kuma muna karbar Naira 50 a wurinsu ne kawai.” Inji shi.
Sakataren ’Yan kasuwar Yatem Jeftha Dauda ya ce samun kudinsu ya danganta da yanayi ne, amma sun fi samun kudi daga masu sayar da karnuka a lokacin rani.
Alhaji Sule Maidoki ya ce an san Angasawa da karade garuruwan wajen ba da magani, inda za ka samu bayan sun ba da magani an warke sai a ba su kyautar karnuka, “to wadannan karnukan suke kawo wa matansu, inda su kuma sai su kawo kasuwa su sayar.”
Ya ce kodayake akan samu maza ma suna kawo karnuka don sayarwa amma mata sun fi yawa.
Wani abu da zai ja hankalin mutum shi ne yanayin yadda za ka ji karnuka suna ihu amma daga lokacin da aka shigo da su kasuwar sai ka ji sun yi shiru kamar ruwa ya cinye su.
Aminiya ta gano cewa kasuwar tana fara ci ne daga misalin karfe 6 na safiyar na kowace Alhamis, amma takan kankama duk lokacin da ’yan kasuwar Kalaba suka karaso kasuwar. “Sukan zo da jarkokin manja, sannan su yi amfani da kudin wajen sayen karnukansu.” Inji Dauda.
Aminiya ta binciko akan yi cinikin karnuka da kudinsu ya kai miliyan uku a kowace ranar kasuwa.
Manshack Ubandoma, wanda shi ne Shugaban Matasan Dawaki, sannan Shugaban kungiyar NURTW a Kasuwar Dawaki ya ce farashin kare ya kama daga Naira dubu bakwai zuwa 15, ya dai danganta da nauyin karen ne.
Misis Mutardang Gabwat wadda take sayar da karnuka tsawon shekara 15 ta ce ta dauki nauyin makarantar ’ya’yanta, ta kuma gina gida sannan da kudin kasuwacin sayar da karnuka take noma. Ta ce wani lokaci takan sayi karnuka a wurin mutane kafin ta jira ’yan kasuwar Kalaba su ta sayar musu.
“Nakan ware dubu 200 a kowane mako, inda nake sayen fiye da karnuka 20 kowane mako, inda nakan samu ribar Naira dubu 25 a karnukan da na sayar.” Inji ta.
Da aka tambaye ta me ya sa mafi yawan ’yan kasuwar mata ne sai ta bayyana hakan ya nuna mata sun fara tashi don neman na kansu ba tare da tsayawa komai sai an yi musu ba.
Ta yi korafin cewa wani lokaci mazajensu da suke zuwa garuruwa don nemo karnuka ba sa dawowa, inda a can suke kama wadansu sana’o’, “Wadansu su yi aure su zauna a wurin, idan ba mu nemi na kanmu ba wa zai dauki nuayinmu?”
Gideon Gambo Goyoma, Shugaban masu sayar da karnuka a kasuwar ya bayyana cewa suna da mambobi 200 da suke sayar da karnuka a kasuwar, kuma sun samar da kudin shiga ga karamar Hukumar Kanke, sannan Angasawa suna son naman kare ne saboda maganin da ke cikinsa, sannan za a iya sarrafa shi ba tare da kashe kudi ba.
Idris Abubakar wanda shi ne yake lura da yadda ake saukewa da lodin karnuka ya bayyana cewa yadda karnukan ba suke daina ihu yayin da ake sauke su ko lodinsu wani sirri ne da masu lodin karnukan suka bar wa kansu sani.
“Na sha ganin mafadatan karnuka amma daga an shigo da su kasuwar sai ka ga sun natsu, komai za a yi da su ba za su yi tirjiya ba, ban taba ganin wani kare ya ci ji wani a kasuwar nan ba, abin har mamaki yake ba ni.”
Shugaban ’yan kasuwar Kalaba, Robert Aniedi ya ce ya shafe fiye da shekara 10 wajen kasuwancin karnuka, don haka ya san ciki da wajen kasuwar karnuka.
Bayan ya fara shigar da karnukan cikin wani kejin da ke cikin motar don a yi jigilarsu zuwa Kalaba, sai ya ce kasuwar karnuka da dadi da kuma wuya.
Aniedi ya ce, wani dan uwansa ne ya koya masa kasuwancin karnuka shekara 10 da ta gabata, inda a yanzu yakan ci kasuwar akalla sau biyu a wata, inda yake sayar da manja sannan ya sayi karnuka da awakai ya kai Kalaba.
Aminiya ta lura cewa motarsa ta dauko kusan jarkokin manja 50 masu cin lita 25, inda kuma yake sayar da su duk ranar kasuwar, inda ya bayyana sukan bar Kalaba daga misalin karfe 12 na ranar Laraba sannan su shafe awa 24 a kan hanya kafin sui so Dawaki.
“Idan muka sayar da kayayyakinmu a ranar muke kama hanyar koma wa Kalaba.”
Ya ce, suna kai karnukan cikin koshin lafiya, inda suke sayar da su a Kalaba da kuma sauran jihohin Kudu maso Kudu, “muna kai su cikin koshin lafiya, amma kasuwancinsu akwai wahala sosai, amma dai muna samun riba, nakan samu riba daga Naira dubu 50 zuwa 100 a kowace tafiya.”