Yadda kato ya yi jigida da bam ya tarwatsa dalibai
Sabanin rahotonnin da aka bayar cewa wanda ya tayar da bam a makarantar sakandare ta Potiskum karamin yaro ne, Aminiya ta gano cewa babban mutum ne ya sanya kaya irin na daliban makarantar ya shiga cikinsu ya tarwatsa bam din. A ranar Litinin dai wani dan kunar bakin wake ya kai hari a wata makarantar […]

Sabanin rahotonnin da aka bayar cewa wanda ya tayar da bam a makarantar sakandare ta Potiskum karamin yaro ne, Aminiya ta gano cewa babban mutum ne ya sanya kaya irin na daliban makarantar ya shiga cikinsu ya tarwatsa bam din.
A ranar Litinin dai wani dan kunar bakin wake ya kai hari a wata makarantar sakandaren kimiyya (GSTC) da ke garin Potiskum a Jihar Yobe, inda ya yi sanadiyyar hallaka yara dalibai ’yaan kasa da shekara 17 kusan 50 tare da jikkata akalla 80.
Wata majiya a makarantar sakandaren ta bayyana wa Aminiya cewa wannan dan kunar bakin waken ya sanya kaya irin na daliban ne ya shiga cikinsu a yayin da suka yi layi da misalin karfe 7:30 na safe domin sauraron jawabin shugabannin makarantar (Assembly) a ranar Litinin kamar yadda aka saba, shi ne ya kutsa cikinsu ba zato ba tsammani ya tada bam din da ke jikinsa, nan take ya tarwatse ya kashe dalibai masu yawa tare da jikkata wadansu da dama.
Wami malamin makarantar da ya nemi a sakaye sunansa, ya bayyana wa Aminiya cewa, wannan dan kunar bakin wake ya shammace su ne, domin kuwa daga bisani an bayyana musu cewa wadansu daga cikin dalibai kafin faruwar lamarin har sun rika cewa, yau kuma sun samu sabon dalibi ne? kasancewar sun ga ba yaro ba ne, ana cikin hakan ne kafin a farga sai kawai aka ji wuri ya kaure da wata muguwar kara, ta yadda su da suke ofis ma sai da suka firgita, ashe dan kunar bakin wake ne ya tayar da bam a cikin dalibai.
Malamin ya ci gaba da cewa, lalle wannan abu akwai sakacin jami’an tsaro da kuma gwamnati, domin kuwa a ’yan kwanakin nan ne aka gano wani bam a wannan makarantar, amma kafin ya kai ga fashewa aka sanar da jami’an tsaro suka zo suka warware shi, “ashe ka ga tun da an ga hakan da ya kamata a dauki cikakken mataki kan hakan saboda gaba, tun da makarantar duk da dadewarta a bude take ba tare da an kewaye ta ba.”
Shugaban makarantar Malam Buba Sanda Mustapha, ya bayyana cewa babu malamin da ya rasa ransa, saboda a lokacin da al’amarin ya faru malaman sun taru a gaban ofishinsa ne suna jiransa domin su tafi wurin da daliban suka yi layi, kafin su tafi ne bam din ya tashi.
Da Aminiya ta ziyarci babban asibitin garin Potiskum inda aka fara kai wadanda suka jikkata, ta gana da wani karamin yaro dan shekara 13 mai suna Usman M. Bawa da ya tsira da munana raunuka a kafafunsa, wanda ya ce a lokacin da wannan bam din ya tashi yana cikin layi ne kuma lallai shi wannan mutumin da suke zaton shi ya tayar da bam din ya wuce ta gabansa ne, bai fi minti daya da wucewa ba sai kawai ya ji an jefa shi sama, daga bisani kuma ya gan shi ana masa fifita a asibiti, iya abin da ya sani ke nan, “amma na yi sa’a da bai tsaya kusa da ni ba,” sai ya fashe da kuka.Wani dalibin kuma mai suna Muhammad A. Abdullahi, wanda bai wuce shekara 16 ba, a lokacin da yake kan gadon asibiti ya bayyana wa Aminiya cewa, abin da kawai zai iya tunawa shi ne, ya san dai sun yi layi da wadansu abokansa sai kawai ya ji ya fadi kasa, daga nan kuma sai ya daga ido ya gan shi a asibiti, kafafuwansa duka biyu an daddaure su da bandeji, ya kuma kasa daga su, don haka, a cewarsa, wannan kaddara ce ta same su.
Da Aminiya ke zanta da mahaifin wani dalibi da yake tsaye a kan dansa, amma ya ki fadar sunansa, cewa ya yi, su yanzu babu abin da za su ce sai dai Allah (SWT) Ya saka musu, kuma shugabanni su sani cewa, mulki yana tabbata ne idan an yi adalci, amma ba ya tabbata idan ana zalunci.
Da yake jawabi ga manema labarai a fadarsa dangane da lamarin, Mai martaba Sarkin Fika kuma Shugaban Majlisar sarakunan Jihar Yobe, Alhaji Muhammad Ibn Abali Muhammad, cewa ya yi wannan babban abin bakin ciki ne ya faru ga al’ummarsa,’’ domin bai wuce kwanaki 6 ba aka samu makamancin irin wannan aika-aika a garin na Potiskum da ya haifar da rasa rayukan mutane sama da 30, sai ga shi an sake halaka dalibai kusan 50 haka kawai, ai ka ga abu ne mummuna.’’
Mai martaban ya roki al’ummarsa da su kwantar da hankalinsu tare da mika al’amarinsu ga Allah.
A lokacin da Kwamishinan ’yan sandan Jihar Yobe ya je fadarsa domin yi masa jaje, Mai martaba ya bayyana masa cewa jama’a fa sun fara gajiya da irin wannan aika-aika, don haka akwai bukatar a dauki matakin gaggawa don dakile masu aikata irin wannan barna.
Tun farko da yake bayani ga Aminiya a cikin asibitin na Potiskum, Shugaban karamar Hukumar Potiskum Alhaji Yusuf Yahya, ya nuna alhininsa ne dangane da faruwar wannan lamarin, tare da cewa duk wadanda suka ji rauni za a kula da su.
Wannan abu da ya faru ya harzuka al’ummar garin Potiskum ta yadda a lokacin da jami’an tsaron hadin gwiwa (JTF) suka shiga makarantar domin kai dauki bayan fashewar bam din sai mutane suka taso musu, wanda ya sanya dole suka juya suka koma.
A halin yanzu dai wadansu mazauna garin Potiskum suna ficewa daga garin a sakamakon razana da suka yi.
Wani magidanci da Aminiya ta zanta da shi a garin Potiskum, mai suna Malam Umaru Mai almajirai, yayin da yake hanyar zuwa tasha shi da iyalinsa, cewa ya yi, a halin yanzu barin garin Potiskum ya zama masa dole, domin kuwa babu amfanin zamansu wurin da ba za su samu natsuwa ba, a kullum barci suke yi da ido daya, haka nan idan sun fita harkokin kasuwanci ba su da tabbacin dawowa gida lafiya, kuma idan ’ya’yansu sun tafi makaranta ba su da tabbacin dawowarsu lafiya. “Don haka a gaskiya rayuwa a garin potiskum a halin da ake ciki babbar kasada ce, tun da yake ba ka san waye mai kokarin kashe ka ba, abu ne a duhu, tun da babu kama ga dan kunar bakin wake, kuma ga shi hukuma babu abin da za ta iya yi mana.”
Wani tsohon ma’aikacin gwamnati da ya nemi a boye sunansa, da ya yake bayyana wa Aminiya dalilinsa na son barin garin Potiskum cewa ya yi, yanzu mazauna garin potiskum suna cikin halin tsaka mai wuya ne, domin ’yan Boko Haram din a kullum kara kusanto garin suke yi, tun da a ’yan kwanakin nan sun ji labarinsu a garin Ngalda da Fika, bayan da suka aikata ta’assa a garuruwan Nafada da Ashaka, to ai ka ga abin da ya ci Doma ba zai bar Awe ba, domin ina Fika da Ngalda da Nafada? Ai kusa suke da garin Potiskum.”
Wani dan kungiyar direbobi ta kasa (NURTW) da ke lodi a tashar mota a Potiskum ya ce, a kullum sukan samu mutane masu yawa suna neman shatar mota don dibar iyalansu da kayayyakinsu zuwa garuruwansu na asali.
Shi kuwa shugaban rundunar adalci na Jihar Yobe Malam Zakari Adamu, cewa ya yi, dole ne mutane su bar garin tun da ana turowa a kashe mutane haka siddan.