Yadda katobarar gandiroba ta jawo rikici a gidan yari
A ranar alhamis din makon jiya ne rikici ya barke a gidan yarin Zariya sakamakon wani furucin batanci da wani gandiroba mai suna Patrick Shalon da aka ce ya yi a kan Manzon Allah (SAW). A lokacin rikicin an shafe tsawon awa biyar ana harbe-harbe a tsakanin ‘yan kason da jami’an tsaron hadin gwuiwa, wanda […]

A ranar alhamis din makon jiya ne rikici ya barke a gidan yarin Zariya sakamakon wani furucin batanci da wani gandiroba mai suna Patrick Shalon da aka ce ya yi a kan Manzon Allah (SAW).
A lokacin rikicin an shafe tsawon awa biyar ana harbe-harbe a tsakanin ‘yan kason da jami’an tsaron hadin gwuiwa, wanda ya sanya mutane biyar suka raunana.
Makwabtan gidan yarin sun shaida wa Aminiya cewa tun misalin karfe tara na safiyar ranar Alhamis suka fara jin karar harbe-harbe, can sai suka hango gidan yarin na ci da wuta, wanda ya janyo duk wani abu da ake gudanarwa a Unguwar ya tsaya cik, a sakamakon kewaye Unguwar da jami’an tsaro suka yi kuma suka hana kowa fita ko shiga Unguwar.
Wani ma’aikacin gidan yarin wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya sheda wa Aminiya cewa wannan hargitsin ya samo asali ne a lokacin da suka tara ‘yan kason suna yi musu huduba tare da ba su shawarwari, ‘’sai daya daga cikinmu mai suna Patrick Shalon ya fadi wata kalma da take aibanta Manzo a lokacin da yake tasa hudubar. To daga nan ne fa hargitsi ya barke,’yan kason suka nuna bacin ransu saboda kalmar batancin nan da ya fada ga Manzon Allah (SAW), suka fara harbin kan mai uwa da wabi, suna kabbarori, suka tunkari dakin da ake ajiye bindigogi suka fasa suka dauko suka fara harbi, sannan suka cinna wa gidan wuta, wannan shi ne abin da yafaru.’’
Da yake ganawa da manema labarai, Kwanturola mai kula da shiyya ta (B) wadda ta kunshi jahohin Kaduna da Kano da Jigawa da kuma Katsina, Malam Usman Abdulhamid Maina Kaina, cewa ya yi duk da cewa ya gane wa idanunsa irin abin da ya faru amma yana ganin tarzomar karama ce domin ‘yan kason ba su kona dakin ajiye abincinsu ba, don haka babu wani abu da zai ce sai bayan kammala bincike, saboda haka ya bukaci a ba shi lokaci.