Yadda kayan wasa ke samar wa dan shekara shida Dala miliyan 11 a shekara
Wani karamin yaro dan shekara shida a Amurka yana samun Dala miliyabn 11 a shekara, saboda kawai yana nazarin kayan wasa da nau’ukan alawa a talabijin shafin sadarwar YouTube. Bisa wannan dalilin ne Mujallar masu kudin duniya ta Forbes ta sanya shi na takwas a jerin taurarin ’yan ‘wasa da aka fi biyansu ladar aiki […]
Wani karamin yaro dan shekara shida a Amurka yana samun Dala miliyabn 11 a shekara, saboda kawai yana nazarin kayan wasa da nau’ukan alawa a talabijin shafin sadarwar YouTube. Bisa wannan dalilin ne Mujallar masu kudin duniya ta Forbes ta sanya shi na takwas a jerin taurarin ’yan ‘wasa da aka fi biyansu ladar aiki a shafin YouTube cikin shekarar 2017,” kamar yadda rahoton jaridan Hindustan Times ya tabbatar.
Ryan ya fara tashar nazarin kayan wasan yara ta Ryan ToysRebiew yana dan shekara hudu tare da taimakon iyayensa. Kwatankwacin ayyukansa a tashar na nuni da cewa, “ “Ryan na kaunar kayan wasa. Bibiyar kayan wasannin yara! Yana sha’awar motoci da jiragen kasa da wasannin Thomas and Friends da Lego da manyan gwaraza na ‘Superheroes’ da kayan wasannin shahararren filin wasa na duniya “disney’ da manyan motoci da hutun iyali.
Shirin hotunan bidioyon da yake baje wa al’umma ya sanya ya zama shahararren tauraro a YouTube, inda hamshakiyar adakarsa ta Giant Egg Surprise’ take dauke da kayan wasa 100. Wannan bidiyo a kalla mutum milliyan 800 ne suka kale shi zuwa yanzu.