Yadda Kirista ya taimaki mahaifiyar Rarara a hannun masu garkuwa
Dattijuwar ta shafe kwana 20 a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da ita.
Mahaifiyar mawaki Dauda Kahutu Rarara, wadda ’yan bindiga suka sako bayan shafe kwanaki a hannunsu ta bayyana yadda wani matashi Kirista ya taimaka mata a lokacin da suke hannun masu garkuwar.
Hajiya Hauwa’u Adamu ta bayyana haka ne a wani faifan bidiyon godiya da ta yi, inda a ciki ta bayyana cewa ta samu matashin mai suna Bala Timothy a can, amma ya rika taimaka mata wajen yi mata wasu ayyuka.
- Dole a faɗa wa Shugaban Ƙasa gaskiya — Ndume
- Za mu rage mace-macen mata wajen haihuwa — Gwamnan Kano
A cewarta, yana cikin taimakonta ne aka biya kudin fansarsa, amma da ta roke shi, sai ya amince ya ci gaba da zama da ita har zuwa lokacin da ita ma ta samu ’yanci.
Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito cewa dattijuwar ta shafe kwana 20 a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da ita a gidanta da ke Karamar Hukumar Danja a Jihar Katsina.
Tuni Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama daya daga cikin waɗanda suka sace mahaifiyar mawakin, sannan ta ce ta samu nasarar kashe ɗaya daga cikinsu, kuma ta kwato Naira miliyan 26.5 na fansar bayan sako ta.