Yadda ‘koren ganyen shayi’ ke gyara jiki
Koren ganyen shayi na da amfani a jikinmu domin shan sa na kara lafiya da kuma kara santsin fata. Za a iya shafa ganyen shayin a fuska. Koren ganyen shayi na kare fata daga saurin tsufa. Bayan haka, yana kuma kare jikinmu daga cututtuka da dama. Yawan shan koren ganyen shayi na mayar da tsohuwa […]
Koren ganyen shayi na da amfani a jikinmu domin shan sa na kara lafiya da kuma kara santsin fata. Za a iya shafa ganyen shayin a fuska. Koren ganyen shayi na kare fata daga saurin tsufa. Bayan haka, yana kuma kare jikinmu daga cututtuka da dama. Yawan shan koren ganyen shayi na mayar da tsohuwa yarinya.
Hanyoyi da za a iya amfani da koren ganyen shayi:
– Za a iya amfani da koren ganyen shayi a fuska:
Za a yi hakan ne idan aka hada koren ganyen shayi da mayukan da ake shafawa, idan an yi hakan sai a rika shafawa a fuska. Ganyen na kunshe da sinadarin bitamin C da A da kuma E. Amfani da ganyen na rage maikon fuska kuma fuska za ta yi santsi yadda ko alamar kuraje ba za a gani ba. Za a samu man ‘mayonnaise’ sai a dibi cokali uku, sannan a hada da dakakken koren ganyen shayi. Za a rika shafawa a fuska, saj dai kada a shafa a gefen idanu. Daga nan a bar hadin na tsawon minti 20, sai kuma a wanke da ruwan dumi.
– Amfani da koren ganyen shayi na rage numfashi mai wari:
A tafasa ganyen shayi. Bayan haka, sai a jira na tsawon minti 30. Sai a rika amfani da shi wajen wanke baki. Yin hakan na hana datti zama a kan hakori. Kuma zai magance warin baki.
– Shan shayin na rage kiba:
Za a iya shan shayin safe da yamma domin rage maikon jiki.