Yadda kudin fansa ya fallasa matashin da ya sace budurwa

Da kudin fansar da aka ba shi aka gano maboyarsa aka kuma cafke shi

Yadda kudin fansa ya fallasa matashin da ya sace budurwa

‘Yan sanda a bakin Aiki

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo ta cafke wani matashi mai shekara 19 bisa zargin yin garkuwa da wata budurwa mai shekara 16.

’Yan sanda sun cafke matashin ne a unguwarw Egab da ke kan titin Benin zuwa Auchi.

Da yake tatraunawa da manema labarai, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Edo, Phillip Aliyu Ogbaduz ya ce sun yi nasarar kama matashin ne bayan rahoton da mahaifiyar yarinyar ta shigar.

Ya ce sashen yaki da satar mutane da zambar intanet ne suka tsunduma bincike, bayan yarinyar ta tafi makaranta a ranar 25 ga Maris ba tare da ta dawo ba.

Matashin ya yi barazanar kashe ta ko sayar da ita ga makiyaya, matukar bai samu kudin da yake bukata ba.

Kwamishinan ’Yan Sandan ya ce mahaifiyar yarinyar ta biya N550,000 a wani asusun banki da mai garkuwar ya bayar.

Ogbadu ya kara da cewa da asusun bankin ne aka yi amfani aka gano inda matashin yake, sannan aka cafke shi a ranar 30 ga watan Maris, 2021.

Ya ce an samu kwamfuta biyu a tare da matashin, sai kuma kudi N220,000 da suka ragu daga abin da ya karba na kudin fansa.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna