Yadda kudurin canja jadawalin zabe ya raba kan ’yan majalisa
Shugaba Muhammadu Buhari ya ki sanya hannu kan kudurin dokar zabe da majalisa ta yi wa gyaran fuska wanda ya sauya lokutan zabe a kasar. Shugaban kasar ya kafa hujja da damar da kundin dokokin Najeriya ya bashi na ikon yin watsi da kudurin dokar a wasikar da ya aike wa shugaban majalisar dattawa, […]

Shugaba Muhammadu Buhari ya ki sanya hannu kan kudurin dokar zabe da majalisa ta yi wa gyaran fuska wanda ya sauya lokutan zabe a kasar.
Shugaban kasar ya kafa hujja da damar da kundin dokokin Najeriya ya bashi na ikon yin watsi da kudurin dokar a wasikar da ya aike wa shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da shugaban majalisar dokoki, Yakubu Dogara.
Shugabannin majalisar biyu ne suka karanta wasikar a zauren taron majalisun yayin zaman majalisun a jiya.
An yi wasikar lakabin : “Matakin shugaban kasa na kin sanya hannu a kan kudurin dokar zabe ta shekarar 2018”.