Yadda kungiyar IPOB ta kashe Musulmai da sunan #EndSARS —Okonkwo
Tsohon Daraktan Gudanarwan Majalisar Kolin Harkokin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Mallam Isa Friday Okonkwo ya ce kungiyar ’yan-awaren Biafra (IPOB) ta fake da zanga-zangar #EndSARS ta karkashe Musulmai ’yan kabilar Igbo. Mallam Isa Okonkwo, Daraktan Cibiyar Musulunci da Makarantar Harshen Larabci da Nazarin Musulunci a Anofia, Afikpo, Jihar Ebonyi, ya bayyana yadda aka kulle su […]
Tsohon Daraktan Gudanarwan Majalisar Kolin Harkokin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Mallam Isa Friday Okonkwo ya ce kungiyar ’yan-awaren Biafra (IPOB) ta fake da zanga-zangar #EndSARS ta karkashe Musulmai ’yan kabilar Igbo.
Mallam Isa Okonkwo, Daraktan Cibiyar Musulunci da Makarantar Harshen Larabci da Nazarin Musulunci a Anofia, Afikpo, Jihar Ebonyi, ya bayyana yadda aka kulle su a cibiyar a lokacin tarzomar #EndSARS.
- Dakatar da Rahama Sadau ba zai canza komai ba a Kannywood —Farida Jalal
- An ba da damar shan giya da zina bayan yi wa Shari’ar Musulunci kwaskwarima a UAE
Ko za ka bayyana mana halin da kai da mabiyanka kuka shiga a lokacin zanga-zangar #EndSARS a yankinku?
Kafin mu yi maganar #EndSARS bari mu waiwaya zuwa 2017 lokacin da wani Musulmi mai suna Muhammad Nbono da ya yi ridda.
Shi ne ya kai wa IPOB sunayen wasu Musulmi 26 ’yan kabilar Igbo cewa a kashe su bisa zargin su da zagon kasa ga shirin IPOB na kafa kasar Biafra.
An fi shekara daya ’yan IPOB na kiran mu a waya suna barazana ga rayuwarmu kafin daga baya suka daina.
A lokacin zanga-zangar #EndSARS sai kungiyar ta sake wallafa sunanyen mutanen a shafinta na Facebook, ta ci gaba da kira tana mana barazana.
Akan kira mu akalla sau uku a kulllum a yi barazanar halaka mu — Na farko ke nan.
Abu na biyu shi ne batun wannan cibiyar Musulunci da ke Afikpo, wadda makarantar Musulunci ce ta musamman a yankin Kudu maso Gabas ad ma Najeriya.
Tun a 1953 aka kafa cibiyar kafin daga baya a yi mata gyaran fuska a 1983 kuma tun daga lokacin take ta yaye malamai daga sassan Najeriya.
Yana da kyau a sani cewa a 2003 an yi yunkurin tayar da bom a cibiyar; an kawo wa wurin hari amma barnar ba ta yi yawa sosai ba.
Wannan karon sun yi ta aiko sakonni akai-akai cewa za su kawo wa cibiyar Musuluncin hari.
Saboda haka muka kasance cikin fargaba a lokacin zanga-zangar: Ana iya kai min hari a matsayina an Isa Okonkwo; cibiyar ma ana iya kai mata hari saboda kasancewarta cibiyar Musulunci.
A wane irin yanayi kuka kasance a lokacin zanga-zangar ta #EndSARS?
A tsawon lokacin a mun kasance a tsare ko fita waje ba ma yi.
A cikin makarantar muke tare da dalibai kasancewar akwai dalibai masu kwana sama da 300 daga sassan kasar nan.
Da barazanar ta yi ta karuwa sai muka sanar da Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Daraktan DSS da kuma gwamnan jihar.
Daga nan ne aka fara turo jami’an tsaro; da farko ’yan sanda ne ke zuwa suna zama da mu a makarantar don su ba mu kariya.
Daga baya Babban Kwamandan Runduna ta 18 ya umarci a turo soja bakwai daga Barikin Nkwangu, kuma har yanzu sojojin da ’yan sandan na tare da mu a cikin makarantar a koyaushe.
Yaya dalibai da malamai suka tsinci kansu sakamakkon yadda suka ga sojoji da ’yan sanda a cikin makarantar?
Ganin ’yan sandan ne ya ba mu kwarin gwiwar yin karantu da koyarwa saboda kafin zuwansu muna cikin tashin hankali ne.
A baya dagacin kauyen na ajiye motarsa a cikin makarantar saboda kyakkyawar dangantakar da ke tsakaninmu da mutanen kauyen.
Ana haka sai ya sa a dauke motar; da na tambayi direbansa dalilin dauke motar bagatatan sai ya ce dagacin ya ce daga yanzu zuwa kowane lokaci IPOB na iya kawo hari.
Ya ce sun kuma gaya masa cewa idan suka zo daraktan za su fara kashewa, don haka ba ya so su yi kuskuren daukar motarsa ce ta daraktan su lalata.
Shin makwabtanku ba su kawo muku dauki ba ne ko kana ganin su ma abin ya fi karfinsu ne?
Da mai garin ya dauke motarsa daga makarantar, ba mu tsaya jiran sai an ce mu sanar da jami’an tsaro ba.
Kalaman basaraken, wanda daga baya na tabbatar na nuna shi da ya kamata ya ba mu kariya ma yana ta kansa kar a kai masa hari a dauka shi ne shugaban makarantar.
Musulmai nawa ne a unguwar kuma mene ne yawan al’umman yankin?
Fiye da kashi 30 na mazauna garin Musulmai ne; Ban san hakikanin yawan al’umman ba amma na tabbata shi ne wuri na biyu da Musulmi suka fi yawa a fadin kasar Igbo.
Daga Nsukka sai kauyen Afikpo wurin yawan Musulmai da su ’yan asalin yankin ne.
Wane shiri gare ku yanzu da zanga-zangar ta lafa amma kuma ake cikin zaman zullumi?
Akwai zauren Musulmai masu zurfin tunani na Kudu maso Gabashin Najeriya wanda ni ma ina ciki kuma na gabatar da batun mun kuma yi zama a kansa domin kawo dauki.
Mun rubuta wasikar halin da muke ciki ga NSCIA, Shugaban ’Yan Sanda, Darakta Janar na DSS, Majalisar Tarayya, da gwamnonin jihohi biyar na Kudu maso Gabas.
Muna shirin yin taron ’yan jarida amma saboda ba mu da ’yan jaridarmu a nan muke son zuwa Abuja mu sanar da duniya halin da muke ciki.
Kodayaushe Amurkawa na cewa ana musgunawa Kiristoci a Najeriya amma ba haka ba ne, su ke gasa wa duk sassan kasar nan aya a ka, amma ba mai maganar halin da muke cike kuma ba mai jin kukanmu.
Saboda haka muke shirin yin kururuwa kuma ina cikin mutanen da suka yi amfani da sanayyarsu a wurare kuman an fara sanar da duniya halin da muke ciki.
Za mu aika wa kungiyar kabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo da ke bata wa Musulmai suna a Kudu maso Gabas don ta farga.
Kungiyar ta yi shiru kamar ba ta san abin da ke faruwa ba shi ya sa za mu rubuta mu sanar da ita a hukumance.
Za kuma mu rubuta wa Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a reshen Kudu maso Gabas saboda mu kafa hujja.
Wasu daga cikinmu kuma na shirin gudanar da taron Musulmai ’yan kabilar Igbo na duniya na gaba amma saboda tsaro ba za mu so mu yi taro a wurin da za a yi mafa kwaf daya ba.
Wasu daga cikin abubun da muke shirin yi a halin yanzu ke nan.
IPOB na neman kafa kasar ’yan kabilar Igbo kuma ku ’yan kabilar ne, me kake ganin yake sa suke kai muku hari?
Mutane ba su fahimci dabararsu ba ne, yakin addini suke yi ba na kabilanci ba.
Fakewa suke yi da Biafra amma galibin jagororin yakin basasan Biafra ai Kiristoci ne daga Arewa irinsu Yakubu Gowon.
Yanzu Yakubu Gowon na da sarauta a yakin kuma tarairayar sa ake yi kamar kwai saboda shi Kirista ne.
T. Y. Danjuma shi ma an ba shi sarauta a yankin ana kuma girmama shi saboda shi Kirista ne.
Mu ba mu taba goyon baya ko adawa da Biafra ba, me ya sa koyaushe mu ake fara kai wa hari? Dalili kawai shi ne saboda mu Musulmai ne ba wani abu ba.
Sunayen mutum 26 da suka wallafa cewa za su kashe duk Musulmai ne; amma ba su taba sanya sunan wani fasto ko reberen cewa za su kashe shi ba.
Hakan ke nuna cewa idan kai Kirsita ne daga Arewa to ka tsira a wurin ’yan Biafra idan kuma Musulmin ne kai, ko daga Kudu maso Gabas kake to kana fuskantar barazanar ’yan Biafra.
Mene ne sakonka ga shugabanni da ’yan siyasan yankin da ke da alhakin ba ku kariya?
Sakonmu ga Gwamnatin Tarayya, Jiha da Kananan Hukumomin yankin shi ne mu ’yan Najeriya ba baki ba, kuma nufin Allah ne da muka zabi addinin da muke yi a cikin kasar da tsarin mulkinta ya ba wa kowa ’yancin zabar addinin da ya yi masa.
Mun zabi addinin Musulunci kuma Allah Shi ne Ubangijinmu muna kuma da yakinin cewa abin da muka yi ba laifi ba ne a doka; hakki ne kuma a kansu su kare rayukanmu da dukiyoyinmu.