Yadda kungiyar muryar talaka ta yi taron ceton kai a Ibadan
kungiyar Muryar Talaka ta kasa ta gudanar da “Taron Ceton Kai” ga mambobinta da ke zaune a sashen Kudu maso Yamma. An gudanar da taron ne a birnin Ibadan, hedkwatar Jihar Oyo a ranar Juma’a da ta wuce. Babban Sakataren kungiyar Kwamared Bishir Dauda, shi ne ya jagoranci wasu wakilai daga hedkwatar kungiyar domin fadakar […]
kungiyar Muryar Talaka ta kasa ta gudanar da “Taron Ceton Kai” ga mambobinta da ke zaune a sashen Kudu maso Yamma. An gudanar da taron ne a birnin Ibadan, hedkwatar Jihar Oyo a ranar Juma’a da ta wuce.
Babban Sakataren kungiyar Kwamared Bishir Dauda, shi ne ya jagoranci wasu wakilai daga hedkwatar kungiyar domin fadakar da jama’a a game da muhimmancin zabar mutane masu shaidar kwatanta gaskiya da adalci a zabe mai gabatowa da kishin kasa da kyautata zamantakewa a tsakanin kabilun kasa, domin samar da zama lafiya mai dorewa a Najeriya.
Bayan kammala taron ne Kwamared Bishir Dauda, ya ziyarci ofishin Aminiya, da ke unguwar sabo cikin birnin Ibadan, inda ya yi wa wakilinmu bayani dangane da taronsu, wanda shi ne irinsa na farko da kungiyar ta gudanar a sashen Kudu maso Yammacin kasa.
“Idan mutane suna so su tsira da mutuncinsu da kare rayuka da dukiyoyinsu, to yanzu ne suka samu damar yin hakan, ta fannin fitowa a zabe mai gabatowa su zabi irin mutanen da za su yi musu jagoranci ga cimma burinsu. Idan muka kuskura wannan dama ta subuce mana to za mu kuka da kanmu, domin ba za mu sake samun irin ta ba. Wannan shi ne babban dalilin fitowarmu domin yin gangami tare da isar da sako ga ‘ya’yan Muryar Talaka da kada su kuskura ayi amfani da kudi wajen sayen mutuncinsu, kuma kada su ji tsoron barazana. Domin mun gano cewa, ba a taba samun lokacin da ake amfani da kabilanci da addini da bangaranci don wargaza kasar nan ba sai a wannan lokaci.” inji Kwamared Bishir Dauda.
A cewarsa, muna so mutane su yi la’akari da irin mutanen da za su zaba a zabe mai zuwa, wadanda za su tabbatar da dunkulalliyar Najeriya da tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma da samar da ayyuka ga miliyoyin matasa da shawo kan matsalar rashawa da cin hanci da ta baibaye kasa baki daya.
Da yake tofa albarkacin bakinsa mai masaukin baki, Kodineto na Muryar Talaka a Jihohi shida na kudu maso yamma, Alhaji Rabi’u Faya, cewa ya yi “muhimmin abin da muka sanya a gaba a wajen wannan taro na Ibadan, shi ne tattaunawa a kan batun mallakar katin zabe na din-din-din ga ‘ya’yan kungiya, domin tabbatar da ganin sun zabi mutanen da suke so su jagorance su. Lokaci ne na mulkin dimokuradiyya wanda ya kamata mu fito mu zabi mutanen da za su kawo mana canji a salon mulkin kasar nan, domin share mana hawaye musamman a kan durkushewar tattalin arzikin kasa.”
Ya ce, manyan masana’antu sun durkushe, sun haifar da rashin aiki ga matasa, wadanda suka shiga cikin kunci da miyagun ayyuka, saboda sakaci da halin ko oho na gwamnati dake kan gado. Ya kamata mu zo mu hada kai mu zabi mutanen da suka fito da burin canza salon mulkin Najeriya domin ceto jama’a daga mawuyacin halin.