Yadda kwalliya ke ‘hana’ amare Sallah ranar biki

Tunda ba kullum ba ne Allah zai yafe mana –Budurwa

Yadda kwalliya ke ‘hana’ amare Sallah ranar biki

Kwalliyar fuska da ake yi wa amare wata aba ce da mata ke yi da nufin kayata fuskarsu ga duk wanda zai yi tozali da su.

Kwalliyar da mata ke yi wa fuskarsu tana danganta ne daga zamani zuwa zamani.

Ma’ana a da mata kan yi wa fuskokinsu ado da gazal da katambiri da koya da sauransu.

Amma a wannan zamani lamarin ya sauya inda mata suka dauki salon yin wata kwalliya ta hanyar shafe-shafen kayayyakin kwalliya na zamani daban-daban.

Kayayyaki sun hada da jagira da jambaki da aishado da sauransu.

Irin wannan kwalliya da ake yi wa mata musamman amare akan dauki tsawon lokaci ana gudanar da ita lura da yawan kayayyakin da ake amfani da su wajen fente fuskar.

Wannan kwalliya an fi yin ta a lokacin bukukuwa duk da cewa wadansu kan yi don son burge maigida da sauransu.

Kwalliyar tana hana amare Sallah

Galibi irin wannan kwalliya da ake yi wa mata ba a son sanya mata ruwa.

Hakan ke sanya matan kin yin Sallah a kan lokaci sai daga bisani bayan an kammala biki sannan a hada sallolin a yi su gaba daya.

Ba amarya kadai ce ke kin yarda ta ‘bata’ kwalliyarta ba, ta hanyar yin alwala, hatta kawayenta kan ki yin Sallar gudun wanke kwalliyar don kada ta lalace.

Samun karbuwar irin wannan kwalliya a wajen mata ya haifar da bude irin wadannan wurare na kwalliya da dama a cikin birane inda kuma masu wadannan wurare ke samun kudi cikin sauki.

Aminiya ta tattauna da matan da ke yin irin wannan kwalliya inda yawanci suka bayyana cewa suna yin alwala ne kafin a shafa musu kwalliyar.

Umma Hafizu ta bayyana cewa, “Gaskiya yin kwalliya bai hana ni yin Sallah.

“Abin da ke faruwa shi ne idan zan yi kwalliyar, sai na yi alwala sannan za a yi min ta yadda da zarar lokacin Sallah ya yi sai dai kawai na yi sallata.

“Idan kin ga masu yin haka sai dai dama wadanda ba su damu da Sallah ce ba.”

Ita kuwa A’isha Mansur cewa ta yi, “Kin san ita kwalliyar ba ta son ruwa, shi ya sa idan mun yi ba mu yarda mu sa mata ruwa.

“Abin da ba kullum ake yi ba, ai za mu roki Allah gafara!”

Ita kuwa Zainab Sani cewa ta yi, “Gaskiya ni ko na yi kwalliya ba na damuwa da sanya ruwa a fuskata saboda na san kadan ne kwalliyar za ta baci don haka idan na yi Sallah sai na dan gyaggyara ta.”

Wata uwa mai suna Fatima Ahmad ta bayyana cewa saboda a guje wa kin yin Sallah a kan lokaci sakamakon yin kwalliyar da amare da kawayensu ke yi, ya sa yanzu duk sha’anin bikin ake mayar da shi da daddare.

“Saboda a magance lamarin kin yin Salalh a tsakanin mata yanzu za ki ga bukukuwan da daddare ake yin su.

“Don haka mace za ta je ta yi Sallar Magariba bayan ta idar sai ta zauna a yi mata kwalliyarta.

“Dama ita Sallar Isha’i tana da isasshen lokaci ko da daddare aka tashi daga wajen bikin sai a yi Sallar,” inji ta.

Kwalliyar ba ta burge wadansu

Sai dai a yayin da masu yin kwalliyar ke alfahari da ita, a gefe guda wadansu mutanen na kushe lamarin inda suke kallon sa a matsayin wani abu na musamman da ke hana matan yin Sallah a kan lokaci.

Wani mai suna Malam Ali ya ce kwalliyar da ’yan matan amarya ke yi ba ta burge shi sakamakon yadda kwalliyar ke sauya wa mata halittarsu.

“Ni ba na ganin kyan kwalliyar ko kadan; idan wadansu matan suka yi abin zai ba ka dariya matuka, domin wallahi maimakon su yi kyau muni suke yi, musamman idan aka yi rashin sa’a an yawaita kayan kwalliyar a fuska. Duk da cewa abu ne na zamani amma abin ba ya yin kyau,” inji shi.

‘Iya kudinki, iya kyan kwalliyarki’

Madiha Salisu ita ce Shugabar Shagon Kwalliya na Madiha Beauty, ta ce kwalliyar tana bambanta daga mace zuwa mace kuma ya danganta da wacce mace take so ko yanayin aljihunta.

“To kin ga ita kwalliyar nan tana da rabe-rabe, ya danganta da karfin aljihun mutum domin akwai ta amare (bridal) da kuma ta sauran mutane.

“Haka kuma akwai kwalliyar da ake yi a lokacin biki da wacce ake yin ta a kowane irin lokaci (casual).

“Misali ta biki ana yin ta ta fito sosai amma wacce mata ke yi don maigida ana shafa kayayyakin ne kadan-kadan.

“Haka kwalliyar amarya ta fi tsada domin lokacin da ake batawa wajen yin ta da kuma irin kayayyaki na musamman da ake amfani da su wajen yi.

“Misali akwai wacce za a yi wa mace a kan Naira dubu biyar akwai ta dubu 30 har zuwa sama,” inji ta.

Da take amsa tambaya game da yadda ake cewa kwalliyar ba ta son a zuba mata ruwa, Amina ta ce “Eh, gaskiya ne kwalliyar idan an sa mata ruwa ingancinta yana raguwa.

“Idan wani abin ya zauna, to wadansu kuma kayan za su bi ruwa.

“Amma game da Sallah gaskiya ba mu shawartar mata da su ki yin Sallah saboda mun san muhimmancin Sallah a addininmu.

“Shi ya sa ma a yanzu matan ke yin alwala kafin a shafa kwalliyar.”

Amina Muhammad ita ce Shugabar Kamfanin Kwalliya na Amal’s Fashion, ta ce a kullum harkar kwalliya kara bunkasa take domin suna kara samun kwarewa daga wadansu ’yan uwansu masu kwalliyar.

“Gaskiya kullum samun kwarewa muke a harkar kwalliyar nan, domin kwalliyar da muke yi a yanzu ta bambanta da wacce muke yi a shekara biyu da suka gabata.

“Kuma a kullum samun karbuwa kwalliyar take a wajen mutane.

“Don a yanzu babu ranar da ba na samun mutanen da zan yi wa kwalliya ko na biki da sauransu,” inji ta.

Kwalliya ba aibu ba ne amma… —Sheikh Umar Sani Fage

Malam Umar Sani Fagge ya ce yin kwalliya ba aibu ba ne amma a yi ta a cikin tsarin addini.

“Yin kwalliya kowace iri ce a wurin mata ba aibu ba ce, sai dai kuma a kiyaye duk abin da zai shafi addini.”

Malamin ya yi kira ga matan su ji tsoron Allah su kula da harkar addininsu kasancewar ba wani abu da yake gaban addini.