Yadda kwartanci ya yi sanadin yanke wa wata matar aure da Fasto hukuncin kisa

Asirin wani Fasto da ke yin soyayya da wata matar aure ya tonu, bayan da aka samu gawar mijin matar a kone a cikin mota wanda haka ya yi sanadiyyar yanke masu hukuncin kisa ta hanyar ratayewa. Lokacin da matar mai suna Misis Eniobong Isonguyo take tsakiyar shanawa da kwartonta Fasto Udoka Ukachukwu, ba ta […]

Yadda kwartanci ya yi sanadin yanke wa wata matar aure da Fasto hukuncin kisa

Fasto Udoka Ukachukwu da Misis Eniobong Isonguyo

Asirin wani Fasto da ke yin soyayya da wata matar aure ya tonu, bayan da aka samu gawar mijin matar a kone a cikin mota wanda haka ya yi sanadiyyar yanke masu hukuncin kisa ta hanyar ratayewa. Lokacin da matar mai suna Misis Eniobong Isonguyo take tsakiyar shanawa da kwartonta Fasto Udoka Ukachukwu, ba ta taba tsammanin cewa, wannan annashuwar ta su za ta yi sanadin a yanke mata da kwartonta Fasto hukuncin kisa ba.

Matar tana auren wani Injiniya ne mai suna Bictor  Gabriel Isonguyo, wanda yake babban ma`aikacin Kamfanin bunkasa albarkatun man fetur na Najeriya wato NPDC da ke Benin. Ana zargin cewa ta dade tana cin amanar mijinta wanda kuma huldar da ta kulla da kwarton ta yi sanadaiyyar mutuwar mijin nata, lamarin ya faru ne tun a shekarar 2013 a lokacin da shi Injiniya Gabriel din da kansa ya fahimci cewa, matarsa ta samu juna biyu a lokacin da ba ya nan. Lamarin da ya sanya ya tuhume ta don ta fada masa inda ta samo cikin.

Babbar Jojin jihar Edo Mai shari’a Esohe-Frances-Ikponmwen

Bincike ya nuna cewa tun daga wancan lokaci suka fara takun saka a tsakaninsa da matar wanda hakan kuma ya sanya ita da Faston suka  kitsa yadda za su halaka Injiniya Gabriel wanda suke ganin yana yi ma harkar sharholiyarsu karan tsaye. Rahotanni sun bayyana cewa a lokacin da wannan lamari ya auku aurensu ya nada shekaru 18 kuma suna da `ya`ya uku a tsakaninsu.

Kafin mutuwarsa an tabbatar da cewa, yana da rashin jituwa da matarsa akan rashin tabbacin ko yaran da suke a tsakaninsu `ya`yansa ne ko kuma sabanin haka tun bayan da ya gano cewa, matarsa tana fita gantali tare da Faston.  An tabbatar da cewa kafin rasuwarsa ya kai wannan korafi ga `yan uwansa sannan kuma ya kai korafin ga surukinsa inda ya sheda masu cewa cikin da take dauke da shi ba nasa ba ne, inda kuma duk suka amince cewa a bari idan matar ta haihu sai a yi gwajin kwayar halitta don tabbatar da sahihancin zargin nasa wanda kuma kafin ta haihu ita da kwarton nata Fasto suka kashe shi. Matar wacce a lokacin tana dauke ne da juna biyu da ya kai wata uku daga karshe ta haihu a gidan kurkuku.

Rahotanni sun nuna cewa, bayan sun halaka shi matar ta je ofishin marigayin inda ta fada masu cewa ya bace bata ganshi ba. A inda daga nan kuma sai ta wuce Banki ta je ta cire kudi har Naira miliyan 4 daga cikin asusun ajiya na hadaka wadda ita da mijin nata suka mallaka. Kamar yadda jami`an `yan sanda suka gano matar ta kai rahoton batan mijinta a wurin `yan sanda wanda kuma daga bisani bayan kwana daya da kai cigiyar mijin nata sai aka samu gawar mijin kone cikin wata mota akan hanyar Sapele da ke Benin.

Daga baya bincike ya gano cewa, matar ta bayar da kyautar motar mijin kirar Bolkswagen Passat ga wani Fasto wanda aka gano motar daga gare shi. An gano cewa, Faston har ya canza lambar motar da wata lamba ta bogi. Kafin a soma wannan bincike matar ta ki amincewa da cewa tana da masaniya akan mutuwar mijin nata. Kamar yadda `yan sanda suka bayyana matar ta fada masu cewa, “A lokacin da na ga mijina ya dade bai dawo gida ba sai na ruga na je wajen Fastona wanda kuma mun shaku da juna, a inda na bashi kyautar sabuwar motar mijina domin ya dage da yi mana da addu`a ko Allah ya bayyana mini mijina. Na fada masa cewa, ya dauki motar ya baiwa coci amma ban san cewa, ya je ya canza mata lamba ba. Na dai fada masa cewa ya dukufa da addu`a domin ina matukar son mijina kuma bana son wani abu ya faru da mijina”.

A lokacin da ýan sanda suke gabatar da bincike sun kama wata mata wacce aka samu motar mamacin a ajiye a cikin gidan da take zaune, wacce ita kuma daga bisani ta yi masu bayanin cewa wani Fasto ne ya kawo motar ya ajiye. Lokacin da `yan sanda suka kama Fasto ya fada masu cewa, wata mai zuwa ibada ce a Cocinsa ta yi ma Cocin sadakar wannan mota saboda tana da bukatar addu`a. Da `yan sanda suka tasa keyarsa don ya nuna masu wannan mata, abin mamaki sai ya kai su wurin matar mamacin.

`Yan sanda sun bayyana cewa, dukkanninsu sun furta aikata wannan aika-aika da bakinsu a yayin wannan bincike. Bayan tsawon shekarun da aka share ana bincike, a ranar Alhamis babbar Kotu ta garin Benin ta yankewa matar da kwartonta Fasto hukuncin kisa bayan da ta same su da laifin kisan Injiniya Isonguyo. A yayin zaman Kotun Lauya mai gabatar da kara ya bayyanawa Kotun cewa, wadanda ake tuhumar sun aikata kisan ne a kokarinsu na rufe zargin cikin da mamacin ya yi ma matarsa. Lauyan ya ce, “Matar mamacin ce ta fada wa Fasto ya tsaya akan hanyar da mijinta yake bi zuwa aiki, sannan idan mijin ya zo wucewa sai ya tsayar da shi ya nemi ya rage masa hanya zuwa wani wuri akan hanyar Sapele. Wanda kuma a yayin rage masa hanyar ne Fasto ya fito da wuka ya daba wa mamacin a wuya, kafin daga bisani kuma ya bude tankin motar ya banka masa wuta ya ya kona shi kurmus a cikin motar.” A yayin da take yanke hukunci mai shari`a Geraldine Imadeghelo, ta bayyana cewa dukkan shedu sun tabbatar da aikata wannan laifi, don haka kotun ta yanke ma Eniobong da kuma Fasto Ukachukwu hukuncin kisa ta hanyar ratayewa.