Yadda Kwastam ta kame sama da Naira biliyan 2 a tashar jirgin saman Legas
Shugaban Hukumar Kwastam Kanal Hamid Ali (mai murabus) ya bayyana cewa, hukumar ba zata iya rufe ko ina a iyakokin kan tudu na kasar nan ba. Kanal Hamid Ali, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya. Jim kadan bayan da ya baje wa manema labarai tarin kudi Dalar Amurka miliyan […]
Shugaban Hukumar Kwastam Kanal Hamid Ali (mai murabus) ya bayyana cewa, hukumar ba zata iya rufe ko ina a iyakokin kan tudu na kasar nan ba.
Kanal Hamid Ali, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya. Jim kadan bayan da ya baje wa manema labarai tarin kudi Dalar Amurka miliyan 8 da dubu dari 6 da jami’an hukumar suka kama a tashar jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Lagos, ya ce iyakokin kasar nan na kan tudu sun yi fadi da girman da ba ko ina ne jami’an hukumar zasu iya toshewa ba.
Shugaban na Kwastam, ya ce kudin da jami’ansu suka kama kwatankwacin Naira biliyan 2.8, ya sabawa ka’idar fita dasu, domin duk kudin da ya kai dala Amurka dubu 10, dole a sanar da hukuma in za a fitar ko a shigo da su kasar nan.